DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 11, 2026
Home Blog Page 415

Biden bai dace da tsayawa takarar shugaban kasa ba- Trump

Biden bai dace da tsayawa takarar shugaban kasa ba- Trump

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump yace dama Joe Biden bai cancanci tsayawa takara ba kuma a hakika bai cancanci zama a matsayin shugaban kasa ba.

Trump kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Republican ya bayyana hakane a jiya Lahadi, bayan da shugaban na Amurka ya bayyana cewa bazai yi takara a zaben kasar dake karatowa ba.

Yace ”za mu sha wahala sosai saboda shugabancinsa, amma za mu gyara barnar da ya yi a cikin kankanin lokaci”.

Za a rika ba mata hutun ‘ta-kaba’ idan mazajensu sun rasu a Katsina

Za a rika ba mata hutun ‘ta-kaba’ idan mazajensu sun rasu a Katsina

Gwamnatin jihar ta bullo da sabon tsarin ba mata ma’aikatan da mazajensu suka rasu hutun watanni hudu da kwanaki 10 don su yi ‘ta-kaba’ a jihar.

Musulunci dai ya tanadi ‘ta-kaba’ ga matan da mazajensu suka rasu su zauna gida a killace don jimamin rasuwar mazajen nasu.

Jaridar Punch ta jiyo shugaban ma’aikatan gwamnati a jihar Katsina Falalu Bawale ba cewa an aike da sanarwa ga duk ma’aikatu, sassa da hukumomin gwamnati da su rika ba mata hutun ‘ta-kaba’ idan mazajensu sun rasu.

Hakan dai ya biyo bayan bukatar da majalisar dokokin jihar ta gabatar na neman a samar da tsarin ba da hutun ‘idda’ ga mata ma’aikatan da mazajensu suka rasu, wanda daga bisani sashen zartarwar jihar ya amince.

Za a inganta alaka tsakanin Nijeriya da Masar

Za a inganta alaka tsakanin Nijeriya da Masar

Jakadan Masar a Nijeriya, Mohamed Fouad, ya bayyana cewa Nijeriya da Masar na fatan inganta huldar dake tsakanin kasashen biyu.

Fouad ya ce, a shekarar 2023, yawan ciniki tsakanin kasashen ya kai dalar Amurka miliyan 190.

Jakadan ya bayyana mamakinsa kan yadda huldar dake tsakanin kasashen biyu take, yana mai cewa da gangan ana kokarin sanya gaba a tsakani.

Ya ce akwai manyan tsare-tsare guda biyu a wani bangare na kokarin kyautata huldar dake tsakanin Nijeriya da Masar.

Jakadan ya yi wannan jawabi ne a Abuja yayin bikin cika shekaru 72 da juyin juya halin kasarsa a watan Yuli.

Yace a matsayin mu na manyan kasashe a Afrika,dole mu kyautata alaka a tsakani ta yadda al’ummar mu zasu amfani kwancen.

Ya kara da cewa, a yau, Masar da sauran kasashen Afirka suna kokarin ganin sun magance kalubalen dake gabansu wadanda suka fuskanta a lokacin gwagwarmayar neman ‘yancin kai.

Don haka Nijeriya da Masar na da bukatar karfafa alaka ta hanyar cinikayya da sauran dabarun tattalin arziki.

Likitoci sun tsunduma yajin aiki a asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria

Likitoci sun tsunduma yajin aiki a asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria

Likitoci a asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello (ABUTH) da ke Zariya, sun fara yajin aikin gargadi na kwanaki biyar domin matsawa hukuma ta biya su hakkokin su.

Dokta Ashiru Mikail, mataimakin shugaban kungiyar likitoci ta kasa (NARD) reshen asibitin ne ya bayyana hakan a wani taron karawa juna sani a Zariya.

Ya bayyana cewa yajin aikin gargadin ya fara ne da sanyin safiyar Litinin dinnan bayan wa’adin mako guda da aka baiwa mahukunta domin shawo kan lamarin.

Mika’il ce idan ba a yi komai ba bayan yajin aikin na gargadi, kungiyar za ta sake zama domin duba matakin da zata dauka na gaba.

Ya ce bukatun kungiyar sun hada da ” biyan albashin mambobin kungiyar GIFMIS wanda ta bukaci a gaggauta biyan wasu sassan albashin likitocin da aka hana a baya.

Ya kara da cewa,ko a watan da ya gabata an rage albashin ‘yan kungiyar da kusan kashi 25 zuwa 27 cikin dari wanda ke nuna daga N58,000 zuwa N60,000.

Ya kara da cewa duk da kalubalen tattalin arziki da ake fama da shi a kasar, babu wani kwakkwaran dalili da hukumar ta bayar na cire kudaden likitocin.

Obi ya yi tir da koma bayan da tattalin arzikin Nijeriya ke ciki, ya yi kira da a dauki matakin gaggawa

Obi ya yi tir da koma bayan da tattalin arzikin Nijeriya ke ciki, ya yi kira da a dauki matakin gaggawa

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a 2023, Peter Obi, ya nuna matukar damuwarsa kan yadda tattalin arzikin kasar ke tafiya tun daga shekarar 2015.

A cikin wata sanarwa a ranar Litinin dinnan daya fitar ta shafinsa na X, Obi ya bayyana bambancin da ke tsakanin yadda tattalin arzikin Nijeriya ya samu a farkon shekarun da ta dawo kan tafarkin dimokuradiyya da kuma halin da take ciki yanzu.

Yace lokacin da Nijeriya ta koma kan mulkin dimokuradiyya a 1999, ta ci gaba da samun karuwar GDP da kusan kashi 6.72 cikin dari na tsawon shekaru 16 daga 1999 zuwa 2014.

Yace duk da cewa, wannan ci gaban bai dore ba, inda karuwar GDP ta ragu zuwa kashi 2.79 cikin 100 a shekarar 2015, sannan kuma tattalin arzikin kasar ya shiga cikin koma baya a shekarar 2016.

A shekarar 2014, gabanin kafa sabuwar gwamnati shekara guda, Nijeriya ce ta fi kowacce kasa karfin tattalin arziki a Afirka inda ta samu babban arzikin cikin gida da ya kai dalar Amurka biliyan 568.5.

Sabanin haka, ya yi nuni da cewa, ya zuwa shekarar 2023, Nijeriya ta fada cikin kasa ta 4 mafi karfin tattalin arziki a nahiyar Afirka, inda ta samu GDP da ya kai dala biliyan 375.

Don haka, lamarin ya kara tabarbarewa a shekarar 2024, inda GDP ya kara raguwa zuwa kimanin dala biliyan 253.

Wannan ya kasance bisa ga bayanan da aka samu daga StatiSense, wani kamfani na AI wanda ya ƙware a nazarin rahoton kuɗi da kimanta bayanan banki.

Daga bisani,Peter Obi ya nuna bacin ransa kan yadda al’amura ke tafiya, inda ya ce, a yau, talauci ya yi kamari, kuma sai karuwa yake yi. rashin aikin yi na karuwa,farashin kayan abinci ya karu sama da kashi 43%.

Ya ce, ya kamata a dauki matakan gaggawa domin ceto al’ummar kasar daga durkushewar tattalin arziki da kuma fitar da ita daga cikin yunwa.

Ambaliyar ruwa ta lalata gidaje 228 a wani yanki na jihar Sokoto

Ambaliyar ruwa ta lalata gidaje 228 a wani yanki na jihar Sokoto

Da yawa daga cikin mazauna karamar hukumar Gada da ke jihar Sokoto sun rasa matsuguni, gonakinsu, da gidaje 228 da dabbobinsu sakamakon ruwan sama da aka yi a kwanakinnan nan.

Wasu daga cikin al’ummomin da lamarin ya shafa sun hada da Dantudu, Balakozo, Gidan Tudu, da kuma garin Tsitse.

Sakamakon tantancewar da hukumar bada agajin gaggawa ta kasa (NEMA) da hukumar bada agajin gaggawa ta Jihar Sakkwato (SEMA) suka gudanar a yankin, da lamarin ya fi shafa shi ne kauyen Dan Tudu, inda gidaje 62 da gidaje 71 suka shafa. A kauyen Balakozo kuma gidaje 33 da gidaje 48 ne lamarin ya shafa.

Hakazalika lamarin ya shafi gidaje 38 da gidaje 52 a kauyen Gidan Tudu, gidaje 68, da kuma 89 a cikin garin Tsitse duk a karamar hukumar ta Gada.

Adadin mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Dan Tudu, Balakozo, Gidan Tudu, da garin Tsitse sun kai 1,664.

Hukumomin kuma sun gano cewa dabbobi da dama da suka hada da tumaki da awaki sun bace saboda rugujewar gine-gine a lokacin ruwan sama.

Abokina da ya yi min gargadi akan saka hannun jari a Najeriya yanzu yana min dariya-Dangote

Abokina da ya yi min gargadi akan saka hannun jari a Najeriya yanzu yana min dariya-Dangote

Attajirin mai kudi a Afirka, Aliko Dangote, ya ce daya daga cikin abokansa da ya fara zuba jari a kasashen waje shekaru hudu da suka wuce, yana yi masa gori a baya a ‘yan kwanakin nan.

Tun da farko Dangote ya ba da labarin yadda wani ke kokarin toshe hanyoyinsa na shigo da danyen mai da kuma yadda ake samun wahalar kayayyakin cikin sauki.

Sai dai a makon da ya gabata, hukumar kula da man fetur ta Nijeriya (NMDPRA) ta ce har yanzu gwamnatin Nijeriya ba ta ba wa matatar man Dangote lasisin fara aiki a kasar ba.

Farouk Ahmed, babban jami’in gudanarwa na hukumar NMDPRA, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Alhamis.

A cewar Ahmed, ikirari da ake yi na durkusar da ayyukan matatar ta Dangote sakamakon rashin samar da danyen mai da kamfanonin mai na kasa da kasa ke yi ba gaskiya ba ne, ya kara da cewa matatar ta na nan a matakin farko kuma har yanzu ba a ba ta lasisi ba. 

Ahmed ya kara da cewa man dizal din Dangote bai kai matsayin kasa da kasa ba, lamarin da dan kasuwar ya musanta a wata tattaunawa da yayi a karshen mako.

A wata tattaunawa da ya yi da jaridar PREMIUM TIMES, Dangote ya bayyana yadda wani abokinsa da ya yi kokarin yin magana ya nuna kishin kasa a Nijeriya a yanzu yana yi masa ba’a.

Yace shekaru hudu da suka wuce, wani abokina ya fara saka kudinsa a kasashen waje. Ban yarda da shi ba, na kuma roke shi da ya sake tunanin matakin da ya dauka domin maslahar kasarsa.

Yace a kwanakin baya abokina ya gargade ni,da saka jari a Nijeriya yanzu kuma yanayin dariya.

Jam’iyyar APC ta lashe zaben kananan hukumomi a Ebonyi

Jam’iyyar APC ta lashe zaben kananan hukumomi a Ebonyi 

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Ebonyi, EBSIEC, ta bayyana jam’iyyar APC a matsayin wadda ta lashe zaben kananan hukumomin jihar da aka gudanar ranar Asabar.

Shugaban Hukumar Jossey Eze, ya bayyana hakan a Abakaliki babban birnin jihar, inda ya ce jam’iyyar ta lashe dukkan kujerun Shugabanin kananan hukumomi 13 na jihar da Kansiloli 171.

Eze ya ce jam’iyyun siyasa uku a Nijeriya ne suka shiga zaben jihar da suka hada da APC, APGA da LP.

Eze ya sanar da cewa hukumar ta amince da sakamakon zaben kananan hukumomin kamar yadda jami’an hukumar suka sanar da sakamakon zaben kansiloli a wuraren zaben.

Shugaban ya bayyana farin cikinsa da cewa an gudanar da aikin cikin lumana tare da yabawa jami’an tsaro da masu ruwa da tsaki kan irin tallafin da suke bayarwa.

Ya godewa duk masu ruwa da tsaki wajen gudanar da zaben, bisa goyon baya da karfafa musu gwiwa.

Mista Eze ya ce ina mika godiya ta musamman ga gwamnatin jihar kan yadda ba ta yi katsalandan a wajen gudanar da zaben ba, domin hakan ya taimaka wajen tabbatar da zabe mai inganci, da adalci.

Ba ma goyon bayan duk wata zanga-zanga – Gwamnatin Kogi

Ba ma goyon bayan duk wata zanga-zanga – Gwamnatin Kogi

Gwamnatin jihar Kogi ta ce ba ta goyon bayan duk wata zanga-zangar da aka shirya yi a fadin kasar saboda matsin rayuwa da tabarbarewar tattalin arziki tattalin arziki da ake fama da shi a Nijeriya.

A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar Kogi, Kingsley Fanwo, ya fitar ranar Lahadi, ya ce gwamnatin jihar na goyon bayan kokarin da gwamnatin shugaba Bola Tinubu ke jagoranta na gyara tattalin arzikin kasar.

Fanwo ya ce,Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, na aiki tukuru don ganin tattalin arzikin kasar ya ya daidaita.

Yace gwamnatin tarayya ta bullo da wasu hanyoyin karfafa tattalin arziki don magance kalubalen da ake fuskanta na matsin rayuwa da al’umma ke ciki, na habbaka harkokin noma,masana’antu, ilimi da kiwon lafiya a kasa baki daya.

Don haka al’umma su kara hakuri,domin gwamnatin tarayya tana kokari wajen bijiro da sabbin hanyoyin inganta tattalin arziki.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu matasa na shirin gudanar da zanga-zanga a fadin kasar a tsakanin ranakun 1 zuwa 15 ga watan Agusta domin nuna adawa da tsadar rayuwa da tabarbarewar tattalin arziki.

A shirye nake na sayar wa NNPCL da matatar fetur da na gina – Dangote

 

Dangote ya ce a shirye yake ya sayar da matatar fetur dinsa ga kamfanin NNPCL na gwamnatin Nijeriya.

Hamshakin attajirin na Afirka ya fadi haka ne a wannan Lahadi, daidai lokacin da ake tsaka da takaddama tsakaninsa da wasu jami’ai da ke sanya ido kan kula da matatun mai na kasar. 

Dangote a wata hira da jaridar Premium Times ya ce ‘idan har suna zargi na da zama mai mamaye kasuwanci, na ba su izini su zo su sayi matatar man fetur din da ake cece-kuce a kanta.’

Matatar da aka kwashe shekaru 10 ana ginawa na da karfin fitar da lita 650,000 ta fetur a kowace rana