DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 11, 2026
Home Blog Page 416

Joe Biden ya ce ba zai yi takara ba a zaɓen da ke tafe

Shugaban Amurka Joe Biden ya janye daga takarar neman shugabancin kasar a karo na biyu.

Joe Biden ya sanar da hakanne Lahadinnan bayan matsin da ya sha daga ‘yan mjalisa na jam’iyar sa ta Democrats su talatin kan ya aje takarar komawa kujerar shugabancin Amurka.

Akwai kuma rahotanni da ke nuna cewa tsohuwar kakakin majalisar wakilai ta Amurka Nanci Pelosi ma ta ƙarfafa wa Biden gwiwar ya aje takardar ta bayan fage.

Wani dalili da ya karfafa ajiye takarar ta Biden shine yadda ya gagara yin magana mai ma’ana sakamakon gigin tsufa a mahawara da aka gudanar na ‘yan takarar shugabancin Amurka na shekarar nan ta 2024.

Janye takarar ta Joe Biden ya   bar jam’iyar ta Democrats cikin wani yanayi a inda saura wata guda kacal ya rage ta gudanar da babban taron ta, sa’annan watanni biyar suka rage a shiga zabe.

Yanzu dai duk wanda ya maye gurbin Joe Biden zai kara ne da Donal Trump a zaɓen na neman shugabancin Amurka da za’a yi ranar biyar ga watan Nuwamban wannan shekara ta 2024 da muke ciki.

Matasa a Yobe sun lalata allunan da ke ɗauke da hotunan Tinubu

Wasu fusatattun matasa a Damaturu jihar Yobe sun lalata allunan kan haya masu ɗauke da hotunan shugaban kasa Bola Tinubu wadda aka sanya dan tarar shugaban zuwa Yobe.

Jim kaɗan bayan kammala wani taron ƙaddamar da shirin bayar da tallafin noma na jihar ta Yobe da aka gaiyaci shugaba Tinubu matsan suka kekketa hotunan na shugaba Tinubu da Kashim Shetima da kuma Gwamnan Yoben Mai Maka Buni.

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shetima ne ya wakilci shugaba Tinubu a taron da aka yi Asabat ɗinnan a Yobe.

Akwai buƙatar ayi bincike kan irin dizil da ake shigo da shi ƙasarnan – Dangote

Hamshaƙin ɗan kasuwa a Najeriya Aliko Dangote yayi zargin cewa ana shigo da Bara gurbin mai zuwa ƙasarnan a saidawa ‘yan Najeriya.

A yayin wata ziyara da kakakin majalisar wakilai ta taraiya Tajuddeen Abbas ya jagoranci ‘yan majalisar zuwa matatar mai ta Dangote, Aliko Ɗangwate ya fada musu cewa akwai bukatar gudanar da bincike saboda gani ko akwai masu zagon ƙasa ga harkar mai ko ma ga harkar kasuwancin shi.
Ya bada shawarar a riƙa bi gidajen mai ana duba man da ake sayar wa ‘yan Najeriya dan tabbatar da hakan.
Dangote ya ƙalubalanci shugaban hukumar kula da harkokin haƙo tare da tãce man fetur na ƙasar Ahmed Farouk kan ingancin man da ake tãce wa a gida, inda ya ce man da da yake tãce yafi wanda ake shigo da shi nesa ba kusa ba.
Kakakin majalisar wakilai ta Najeriya Tajuddeen Abbas ya ce la’akari da zarge zarge da bangarorin biyu ke yi akwai bukatar gudanar da bincike.

Masu shirya gudanar da zanga-zanga ranar Talata zasu ɗanɗana kūɗar su – shugaba Yoweri na Uganda

Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni yana gargadi ga masu ƙoƙarin gudanar da zanga-zanga a kasar ranar Talata mai zuwa da su guji yin hakan ko kuma su guji da fushin hukuma.

Tawagar kungiyoyin fafutuka sun yi niyyar fita zanga-zanga zuwa Majalisar dokokin ƙasar dan nuna fushin su kan cin hanci da rashawa.

Shugaba Museveni a kafafen yada labarai ya ce bazai yiyu yana gani ya bari a rusa abinda ya daɗe yana ganawa ba, kuma idan masu shirya wannan zanga-zanga basu sake shawara zasu gamu da su!

Gwamnatin Najeriya na ƙoƙarin durƙusar da mu – Ƙungiyar masu tãce man fetur a Najeriya

Ƙungiyar masu tãce ɗanyan mai a Najeriya ta koka kan matsayar gwamnatin ƙasar na cigaba da shigo da tãceccen man, abinda suka baiyana da cewa kokarin durƙusar da su ne.

Ƙungiyar tana magana ne bayan wata hira da tace tana yawo da akayi da shugaban hukumar kula da harkokin haƙo tare da tace man fetur na kasar Ahmed Farouk, wanda ya ce dizil da ake tãce a gida Najeriya bashi da kayan wanda ake shigo da shi daga ketare.

Sakataren yada labarai na ƙungiyar ta masu tãce man fetur a Najeriya Eche Idoko ya ce sun damu matuka da kalaman da shugaban hukumar kula da harkokin haƙo da tãce mai Ahmed Farouk yayi na kushe dizil ɗin gida yana yaba na waje, ya ce wannan ba daidai ba ne.

A ranar Juma’an nan ne rahotanni suka ruwaito gwamnatin Najeriya ta bakin wannan hukuma ta NMDPRA ta sanar cewa zata ci gaba da shigo da tãceccen man fetur saboda tabbatar da wadatar sa da kuma kaucewa fadawa hannun bangare guda kachal ke mallakar man da dizil

Kira fita zanga-zanga ya sa an kai wani matashi gidan yari a Nijeriya

 Kira fita zanga-zanga ya sa an kai wani matashi gidan yari a Nijeriya 

Rahotanni sun tabbatar sa cewa ana tsare dan Nijeriya mai amfani da shafin Tik tok, Junaidu Abdullahi da aka fi sani da Abusalma a gidan yari bayan ya wallafa wani faifan bidiyo da yake kiran yan kasar da a su shirya domin a gudanar da zanga-zanga kan tsadar rwyuwa a kasar.

Jaridar Daily Nigerian  ta ruwaito cewa jami’an tsaro sun kama Abusalma tun a ranar Laraba kuma daga baya aka kai shi Abuja.

Mustapha Hamza wanda daya ne daga cikin yan’uwan Abusalma ya tabbatarwa da wakilin Daily Nigerian cewa dan uwansa Abusalma a halin yanzu yana a gidan yarin Kurmawa da ke Kano.

Fãdar shugaban ƙasa na kitsa yadda za’a kama Peter Obi – Ofishin yãɗa labaran Obi

Ofishin yãda labarai na ɗan takaran shugaban ƙasa a jam’iyar Leba party a zaɓen shekara ta 2022 Peter yana zargin fadar shugaban ƙasa da kulla wa Peter Obi maƙarƙashiya da zummar ɓãta masa suna.

Ofishin na harkokin yada labaran Peter Obi ya musanta kalaman kakakin shugaba Tinubu Bayo Onanuga na alakanta ɗan takaran nasu da zanga-zangar da ake ƙoƙarin aiwatarwa a Najeriya.

Ofishin ya ce Bayo Onanuga ya wallafa a shafin sa na twitter cewa Obi da magoya bayan sa ya kamata a ɗora wa alhakin duk wani mummunan abu da zai auku a zanga-zanga da ake ƙoƙarin yi.

Saidai a sanarwar da ofishin na kula da harkar yaɗa labarai na Peter Obi ya fitar ta bakin Yunusa Tanko Asabat ɗinnan ya baiyana cewa zarge zarge marasa tushe da mai magana da yawun shugaban ya ke yi, ba komai bane illa munaƙisar yadda za’a samu dalilin kama Peter Obi a tauye masa hakki.

An yi zanga-zangar rashin tsaro a kauyen jihar Katsina

Dikko Umar Raɗɗa 

Al’ummar garin Marabar Kankara dake kan hanyar Funtua zuwa Malumfashi a jihar Katsina na gudanar da zanga-zangar lumana kan rashin tsaro.

Jama’ar garin sun rufe hanyoyin wucewar motoci, lamarin da ya kawo tsaiko ga matafiya.

A cewar Al’ummar yankin sunce suna gudanar da zanga-zangar ne sakamakon rashin tsaro da ya addabi yankin.

Ko a ranar Juma’ar data gabata yan bindiga sun hallaka mutane da dama a cikin gona kinsu.

Wannan dai na zuwa ne bayan da gwamnan jihar Malam Dikko Umaru Radda ya tafi kasar waje domin gudanar da hutun aiki na tsawon wata daya .daya dauka.

Ka dena fake wa da Guzuma don ka harbi Karsana – saƙon Ƙungiyar matasa na arewa ga Dele Momodu

Ƙungiyar matasa masu ƙoƙarin wanzar da zaman lafiya ta arewacin Najeriya da ake ƙira Northern Yoths for Peaceful Coexistence ta yi martani mai zafi ga mawallafin jaridar nan ta Ovation Dele Momodu game da buɗaɗɗiyar wasiƙar da ya tura ga shugaban Najeriya Bola Tinubu.

Ƙungiyar ta bakin shugaban ta Haruna Bature, ta ce Mawallafin Dele Momodu yana ƙoƙarin yin amfani da wannan wasika ne kawai don cimma wasu muradun sa, saboda bata ga abin da ya haɗa matsalar tattalin arzikin ƙasa da rikicin jihar Rivers ba da har mawallafin ya hade su wuri guda a wannan wasika yana jana hankalin shugaba Tinubu kan su.

Buɗaɗɗiyar wasiƙar Dele Momodun ga shugaba Tinubu dai an wallafa ta ne a wata Jaridar yanar gizo a makonnan.

Ƙungiyar ta ce Dele Momodu ya fake ne da batun tattalin arzikin ƙasar da biyan buƙatar sa kan batun taƙaddamar siyasar jihar Rivers.

A gaggauta kamo wadanda suka kashe basaraken Chanchanji – Gwamnan Taraba

Gwamnan jihar Taraba Agbu Mefas ya bada umurnin a gaggauta kamo waɗanda suka kashe basaraken garin Chanchanji da ɗan sa.

A sanarwar da kakakin gwamnan Emmanuel Bello ya fitar ta nuna cewa gwamnan ya jajanta wa iyalan basaraken da ilahirin jama’ar ƙaramar hukumar Takum kan wannan aika aika.

Sarkin mai suna Kumbiya Tanimu da ɗan sa Yusuf sun gamu da ajalinsu ne a hanyar Chanchanji zuwa Takum bayan sun halarci wani jana’iza a hanyar komawa gida.