Tuesday, April 7, 2026
Home Blog Page 481

Sabuwar Zanga-zanga ta barke a Kano

0

 

Sabuwar zanga-zanga ta barke a
jihar Kano, yayin da jama’a ke ci gaba da nuna fushin su kan hukunci kotun
daukaka kara da ta ayyana Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben
bana, a maimakon Abba Kabir Yusuf da hukumar zabe ta INEC ta sanar.

 

Wannan ba ita ce zanga-zanga ta
farko da al’umma a jihar ke gudanarwa ba, cikin makonni biyu da suka wuce,
yayin da suke ganin shari’ar na cike da kura-kurai musamman bayan bullar
takardun kotu da ke nuna cewa Abba Kabir Yusuf ne ya yi nasara ba Nasiru Gawuna
ba.

 

Duk da kotun daukaka karar ta
fitar da sanrwar da ke nuna cewa hukuncin ta na nan daram, kuskure ne aka samu
a takardun, amma hakan bai hana jama’ar Kano nuna shakku da kuma bayyana fushin
su ta hanyar zanga-zanga ba.

 

A wani labarin na daban duk a
jihar Kano na cewa al’ummar Unguwar Kurna da Rijiyar Lemo a karamar hukumar Dala,
sun rufe hanyoyi tare da kone-konen tayoyi da kuma zanga-zanga don nuna fushin
su game da zargin wani dan sanda da harbin matashin dan wasa na kungiyar
kwallon kafa ta Kurna Samba Alhaji Salisu Rabi’u tare da karin wasu mutane
biyu.

 

Har yanzu babu wani martani game
da hakan daga jami’an tsaro, sai dai kuma rahotanni na cewa matasan sun rufe
unguwar ba shiga ba fita.

 

 

Sanatocin arewacin Nijeriya sun bukaci ECOWAS ta janye takunkumin da ta kakaba wa Jamhuriyar Nijar

Sanatoci daga arewacin Nijeriya sun bukaci kungiyar ECOWAS da ta janye takunkumin da ta kakaba wa Jamhuriyar Nijar bayan da sojoji suka hambarar da gwamnatin farar hula a watannin da suka gabata.
A watan Juli da ya gabata na shekarar 2023 ne dai sojoji suka gudanar da juyin mulkin da ya hambarar da gwamnatin Bazoum Mohamed a Jamhuriyar Nijar.
Daga cikin takunkuman da aka sanya wa Nijar din akwai na yanke duk wata alakar kasuwanci tsakaninta da kasashen da ke cikin kungiyar ta ECOWAS, sai Nijeriya ta yanke wutar lantarkin da take ba Nijar sai kuma kasar Ivory Coast ta yanke duk wata alakar shige da ficen kaya tsakaninta da Nijar.
Sanatocin bayan wata ganawa da suka yi a Abuja, sun bukaci da ECOWAS ta janye wannan takunkumin da ta kakaba wa Jamhuriyar Nijar.
Sannan sanatocin sun bukaci sojojin Nijar da su saki tsohon shugaban kasar Bazoum.

Gwamna Dikko ya ware Naira bilyan 17 don biyan fansho da giratuti a shekarar 2024

Gwamnan jihar Katsina ya gabatar da daftarin kasafin kudin shekarar badi, 2024 na Naira bilyan 454,308 a gaban Majalisar dokokin jihar.
Bangaren ilmi dai ne ke da kaso mai tsoka a cikin kasafin kudin da Gwamnan ya gabatar da ke da kaso 20.13%.
Da yake yi wa manema labarai Karin haske game da abin da ke kunshe cikin kiyasin kasafin kudin, kwamishinan kasafin kudi na jihar Katsina Bello Hussaini Kagara, ya ce idan an kwatanta da kasafin kudin shekarar ta 2023, na shekarar badi, 2024 ya karu da Naira bilyan 153.
Ya yi karin hasken cewa za a biya albashin Naira bilyan 38, a shekarar 2024 sai giratuti da fansho gwamnatin ta kiyasta za ta kashe Naira bilyan 17b.
Kwamishina Bello Hussaini Kagara ya ce manyan ayyuka na da kaso 72% sai kaso 27% na ayyukan yau da kullum.
Wannan ne dai karon farko da Gwamnan ya gabatar da daftarin kasafin kudi a matsayin Gwamnan jihar Katsina bayan da ya yi nasara a babban zaben 2023.
Tsohon Gwamna Masari a cikin watan Nuwambar 2022, ya gabatar da kasafin kudin Naira bilyan 288 a gaban Majalisar dokokin jihar Katsina, da ya zamo shi ne na karshe a kwanakin mulkinsa da ya shafe shekaru 8 yana gudanarwa a jihar Katsina.

Muna bakin cikin halin da jihar Zamfara ke ciki – Masu rajin ‘yancin Dan’adam

Shugaban kungiyar mai rajin kare hakkin bil’adama Comrade Abraham Ekokotu ya bayyana cewa sun shirya wannan taron ne a yau litinin 27 ga watan nuwamba 2023, domin yin karin haske kan halin da jihar Zamfara ke ciki da kuma yin kira da a dauki matakin gaggawa.. 
Ya kara da cewar wannan kungiyar tasu ta Gamayyar kungiyoyin farar hula da masu kare hakkin jama’a a Najeriya (CoCSPION) na kan wani aiki na kasa baki daya domin zakulo hazikan gwamnoni a Nigeria da kuma Gwamnonin da suka gaza cimma abinda sukayi alkawari a lokacin yaqin neman zabe, ya kara da cewar a yau kungiyarsu ta isa jihar Zamfara, inda suka gamu da wani mawuyacin halin da jihar take ciki karkashin mulkin gwamna dauda lawal dare.. 
Sakataren kungiyar ya bayyana cewa, A karkashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal Dare, Jihar Zamfara na fama da matsaloli da dama da suka hadar da rashin tsaro, rashin aikin yi, fatara, tabarbarewar tattalin arziki da rashin isassun kayayyakin more rayuwa da kuma matsalar karancin ababen more rayuwa. Hakki ne akanmu a matsayinmu na yan kasa mu jawo hankali ga waɗannan batutuwa masu mahimmanci da kuma ba da shawara domin kawo canji mai kyau.
Tsawon watanni 8 da suka gabata al’ummar jihar Zamfara na cikin mayuyacin hali sakamakon gazawar sabuwar gwamnati wajen cika alkawarin data dauka lokacin yakin neman zabe, yayi alkawarin kawo karshen matsalar tsaro a kasa da hour 24 idan tayi tsamari sati daya, amma adadin mutanen da aka kashe ko aka sace ya linka adadin mutanen da aka kashe a zamfara a gwamnatocin baya sau uku, Wannan mummunan tashin hankali ya jefa al’ummar Zamfara cikin fargaba.. 
Bugu da kari, rashin mayar da hankali kan manyan ayyuka, sannan kuma yazo ya fara korar jami’an gwamnati wanda hakan ya kara dagula lamarin. Al’ummar Zamfara na fama da matsanancin talauci, wanda hakan ya tilasta musu yin hijira daga gidajensu domin neman ingantacciyar rayuwa. Wannan gudun hijirar dai wata alama ce da ke nuna gazawar gwamna wajen biyan bukatun al’ummar da suka zabeshi.
Duk da tsananin talauci da jama’a ke fuskanta, gwamnan ya kashe sama da Naira miliyan 400 wajen tafiye-tafiyen kasashen waje a cikin watanni uku kacal.
Wannan makudan kudaden da ake kashewa a tafiye-tafiyen kasashen ketare na haifar da ayar tambaya game da inda gwamnatin zamfara ta sa gaba, A yayin da al’ummar Zamfara ke fafutukar ganin sun samu tsaro da kuma abinda zasu ci, abin takaici ne ganin yadda gwamnatin ta kashe makudan kudaden al’umma wajen yin abubuwan more rayuwa maimakon magance matsalolin da jihar ke fuskanta.
CoCSPION ta yi kakkausar suka kan wannan almubazzaranci da dukiyar al’umma tare da yin kira ga kungiyoyi da duk wata ma’aikata ta gwamnati datake da iko, da yan majalissu domin kawo karshen wannan almubazzaranci da kudin alumma bata hanyar daya dace ba. Al’ummar Zamfara sun cancanci shugaban dazai fifita jin dadin su da kuma hanyoyin da za su inganta rayuwarsu, maimakon kashe kudaden tafiye-tafiye fiye da basuda wani amfani ga talakawan jihar zamfara.. 
Muna kira ga hukumomin da abin ya shafa da su binciki lamarin sosai tare da daukar matakin da ya dace don ganin an yi amfani da dukiyar al’umma domin ci gaban al’ummar Jihar Zamfara.
A yau mun tsaya tsayin daka wajen ganin mun janyo hankalin yan kasa domin susan halin da al’ummar jihar Zamfara suke ciki, gazawar wannan gwamnatin ta Dauda lawal Dare a bayyane take, kuma ya zama wajibi a garemu a matsayinmu na yan kishin kasa, mu fito mu bayyanawa duniya halin da gwamnatin jihar zamfara ta sakasu a ciki! 
Daga karshe Muna kira ga al’ummar duniya, hukumomin gwamnati, da ‘yan kasa da abin ya shafa da su hada kai da mu wajen neman a dauki matakin gaggawa da kawo sauyi ga al’ummar jihar Zamfara. Mu hada kai mu ɗaga murya kuma mu tabbatar da cewa an samu sauyi na gaggawa a jihar zamfara ba tare da bata lokaci ba….

Taskar DCL: Sarkakiyar hukuncin zaben Kano da rikicin sojoji da ‘yan sanda ya ci rayukan jama’a

0

 Taskar DCL: Sarkakiyar hukuncin zaben Kano da rikicin sojoji da ‘yan sanda ya ci rayukan jama’a

Taskar DCL: Zazzafar muhawara bayan tabbatar da kwace kujerar Abba da Dauda a kotun daukaka kara

0

 Taskar DCL: Zazzafar muhawara bayan tabbatar da kwace kujerar Abba da Dauda a kotun daukaka kara

‘Yan ta’adda na tilasta wa manoma biyan haraji kafin girbe amfanin gona a Kaduna

Wasu mazauna yankuna karkara a jihar Kaduna na kokawa kan yadda ‘yan bindiga ke kakaba musu haraji kafin su kyale su, su girbe amfanin gonakinsu.
Manoman musamman na yankunan kananan hukumomin Giwa, Birnin Gwari da Igabi sun ce suna samun tsaiko da razani mai yawa daga ‘yan ta’adda a yankin a daidai lokacin da suke kokarin girbe amfanin gonakinsu.
Bayanan da jaridar Daily Trust ta samu, sun ce da yawa daga cikinsu ma sun bar zuwa gonakin saboda barazana kisa ko sacewa daga ‘yan ta’adda.
Hakan na zuwa ne duk kuwa da kokarin jami’an tsaro wajen kakkabe ayyukan ta’addanci a yankunan. Amma dai hakan ba ta sa manoman sun samu sukunin kawar da amfanin gonakinsu ba, da wasu lokuttan ake sanya musu tilas su biya haraji kafin a bari su je gonakin.
Yankunan sun hada da kauyen Kidandan, Galadimawa Kerawa, Sabon Layi, Sabon Birni da Ruma, inda bayanai suka ce manoman a yankunan na biyan harajin 70k-100k ga ‘yan ta’adda kafin a bari su je gonakin.
Bayanai dai sun ce wadanda suka ki biyan wadannan kudaden kuwa na fuskantar barazanar sacewa, kisa ko kuma cinye amfanin gonakinsu.
Wani mazaunin yankin ya shaida cewa wannan lamari da ya yi kamari ya sa mutane da yawa sun fara shawarar yin hijira zuwa wasu garuruwan.

‘Yan sanda sun kama matashin da suka ce ya shahara wajen satar awaki a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta sanar da kama wani da ake zargi ya shahara a satar awaki a kauyen pasali Konu na karamar hukumar Kagarko ta jihar.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan ASP Mansur Hassan ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Nijeriya NAN cewa an kama wanda ake zargin ne a ranar Asabar.
‘Yan sandan sun ce ‘yan sintirin Vigilante na yankin ne suka kama matashin mai kimanin shekaru 20 da ya fito daga kauyen Igwa na karamar hukumar a lokacin da suke sintiri da dare suka hannanta shi ga ‘yan sanda.
Mai magana yawun rundunar ‘yan sandan ya ce a lokacin da aka kama matashin, an same shi da muggan makamai, sannan kuma ya saka takunkumin rufe fuska na facemask.

Kotu ta sauke Gwamnan Plateau na PDP ta ba na APC

Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta soke zaben gwamna Caleb Muftwang na jihar Filato.

Kotun ta ce zaben na gwamnan wanda dan jam’iyyar PDP ne bai inganta ba kamar yadda ta bayyana a Lahadin nan. 
Kotun ta kuma umurci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da ta janye takardar shaidar cin zabe da aka baiwa Muftwang tare da ba Goshwe na APC sabuwar takardar shaidar lashe zabe.

Duk kotun da za a je Gawuna ke da nasara – Ganduje

Shugaban jam’iyyar APC na kasa kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya yaba da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke na tsige gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf tare da bayyana dan takarar jam’iyyar APC a zaben ranar 18 ga watan Maris Nasir Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben.
Ganduje ya ce APC za ta sake yin nasara idan jam’iyyar NNPP da Gwamna Yusuf suka garzaya kotun koli.
Da yake mayar da martani kan hukuncin yayin wani taron manema labarai a ranar Juma’a a Abuja, Ganduje ya ce gwamnatin Gawuna za ta samar da damammaki masu kyau ga talakawa tare da samun nasarori fiye da shekaru takwas da ya yi yana gwamnan jihar.