Tuesday, April 7, 2026
Home Blog Page 482

Ana yaki da Badaru da Matawalle ne domin ture ginshikin nasarar Tinubu a 2027 – Eskimini Bassy

Hadakar kungiyar ‘yan kishin kasa daga sassan Nijeriya daban-daban ta ce a tsakanin jihohin arewa maso yamma, Shugaba Tinubu bai da masoya kamar ministan tsaro Mohammed Badaru da karamin ministan tsaro Bello Matawalle, saboda sune mutanen da suka jajirce domin kawo Tinubu akan kujerar shugaban kasa.
Babban jami’in kungiyar Mr Bassy Eskimini na magana ne a lokacin da yake amsa tambayoyi daga ‘yan jarida, inda ya yi zargin cewa akwai wasu mutane daga cikin ‘yan siyasar Nijeriya da suke yaki da Badaru da Matawalle domin a cire su saboda sun san sune ginshikan Shugaba Tinubu a zaben 2027 mai zuwa.
Mr Bassy ya ce duk duniya ta san cewa cikin wata biyar kacal ministocin tsaro Badaru da Matawalle, sun yi aikin da tun daga shekarar 1999 da aka dawo dimokradiyya, babu wani minista da aka yi a ma’aikatar tsaro wanda ya kawo tsaro cikin gaggawa irin su ba.
Mr Bassy ya buga misali da aikin da sojoji suka gudanar a jihohin Katsina, Sokoto, Kebbi, Zamfara, Neja da Kaduna, inda a nan ne matsalar tsaro take.
 “Amma yanzu ka duba ka ga irin yadda aka samu tsaro yanzu musamman hanyar Zuba zuwa Kaduna, Kaduna zuwa Zaria, Zaria zuwa Funtua, Funtua zuwa Zamfara, Zamfara zuwa Sokoto”. 
“Sannan ka duba ka ga irin yadda aka samu tsaro a Zamfara da Sokoto karkashin jagorancin mulkin Badaru da Matawalle a matsayin ministocin tsaro, misali military sun yi ma bandits Ambush rana daya cikin Maru Local Government sun kashe bandit sama 3,000. Kuma an zuba sojoji cikin daji da kan hanya duka fadin Nijeriya kuma suna aiki tukuru. An samu solution babba. Don haka, muna godiya ga wadannan ministoci.

Majalisar dokokin jihar Jigawa ta dakatar da shugabannin kananan hukumomi uku

Majalisar dokokin jihar Jigawa a ranar Larabar da ta gabata ta dakatar da wasu shugabannin kananan hukumomi uku bisa zargin yin balaguro zuwa kasashen waje ba tare da neman izini daga bangaren zartarwa ba. 
Shugabannin kananan hukumomin da aka dakatar sun hada da Mubarak Ahmed na karamar hukumar Yankwashi, sai Rufai Sunusi na Gumel da kuma Umar Baffa na Birniwa wadanda aka ce sun tafi kasar Rwanda.
Rahotannin sun ce kafin tafiyar ta su majalisar jihar ta bayar da umurnin cewa kada shugabannin kananan hukumomin jihar su je ko’ina saboda shirye-shiryen gabatar da daftarin kasafin kudin shekarar 2024 da gwamnan jihar Umar Namadi ke shirin gabatarwa majalisa.
Majalisar ta kuma amince da matakin dakatar da shugabannin kananan hukumomin uku tare da umurtar mataimakansu da su ci gaba da jan ragamar mulkin kananan hukumomin.

Kada ku yada karya ko sharri don kare gwamnati, kiran gwamnatin Katsina ga matasan da aka nada mukaman yada labarai

Gwamnatin jihar Katsina ta kare matakinta na nada matasa masu amfani da kafafen sadarwar zamani mukamai daban-daban a gwamnatin, inda ta ce ta yi haka ne don ba al’ummar jihar Katsina damar samun sahihan bayanai daga gwamnati.
Maiwada DanMalam, Darakta Janar na bangaren yada labaran Gwamna Dikko ne ya sanar da hakan a lokacin da aka gayyaci daukacin matasan da aka ba mukaman a gidan gwamnatin jihar domin sanar da su hakkokin da suka rataya kansu.
Maiwada DanMalam ya ce a zamanin dimokradiyya, ana bukatar sanar da al’umma matakai da kudurce-kudurcen gwamnati da hanyoyin da take bi don ta kawo ci gaba da al’umma. Don haka ne, ya ce aka nada wadannan matasa domin su taimaka wajen isar da sakon da gwamnati ke kokarin isarwa ga jama’a da sakon jama’a ga gwamnati.
Ya ce masu ganin kamar an dauki wadannan matasa ne domin su yi yada ‘farfaganda’ a gwamnatance, Maiwada ya ce sun yi wa abin gurguwar fahimta, domin gwamnatin Malam Dikko, ba wannan layin ta dauko ba.
Darakta Janar din ya ja hankalin matasan da cewa gwamnatin jiha ta aminta da cancanta da jajircewar su ne ya sa aka ba su wadannan mukamai, don haka ya bukace su da su bayyana gaskiya a duk inda suka samu kansu.
Maiwada DanMalam ya tabbatar da cewa za a shirya taron horar da su domin su san makamar aiki da yadda ya kamata su rika aiki cikin kwarewa da gogewa.
DCL Hausa dai ta ba da labarin yadda a kasa da mako daya, Gwamnan Katsina Dikko Radda ya nada matasa sama da 50 mukamai daban-daban a fannin sadarwar zamani.

Ku janye yajin aikin, mun kama wadanda suka bugi shugabanku, rokon NSA ga ‘yan kwadagon Nijeriya

Mai ba shugaban Nijeriya shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu ya nemi afuwar ‘ya’yan kungiyar kwadago bisa abin da ya kira harin da aka kai wa shugabansu na kasa Comr Joe Ajaero a birnin Owerri na jihar Imo a ranar 1 ga watan Nuwamba, 2023.

Joe Ajaero dai ya isa birnin Owerri ne a ranar domin jagorantar wata gagarumar zanga-zanga, amma aka samu wasu suka lakada masa duka, suka kuma tsare shi na tsawon awanni.
Ba da jimawa ba da faruwar lamarin, kungiyar kwadago ta kasa ta ba gwamnatin tarayya wa’adi da sharudda, ciki hada sai an kamo wadanda suka aikata hakan ga shugaba Ajaero, inda suka yi barazanar tsunduma yajin aiki idan har ba a cika musu wadannan sharudda ba.
Sai dai gwamnatin tarayya ta garzaya kotu, inda ta nemi da a dakatar da NLC daga tafiya wannan yajin aiki, amma dai sai da kungiyar ta tafi yajin aikin a ranar Litinin wayewar Talata. Wannan mataki dai na NLC ya gurgunta harkokin aikin gwamnati a sassa daban-daban.
Sai dai a cikin wata sanarwa daga shugaban sashen yada labarai na ofishin mai shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Zakari Mijinyawa, ta roki ‘yan kwadagon da su yi hakuri su janye yajin aikin don kuwa an kama wadanda suka yi wa shugabansu wannan cin kashi har ma na kaddamar da bincike a kansu.
Malam Nuhu Ribadu ya ce gwamnatin tarayya ta yi nadamar tare da nuna rashin jin dadinta kan wannan lamari da ya faru. Inda ya yi nuni da cewa an taka hakkin bil’adama da hakan ya saba dokar kasa.

Da yiwuwar kudin sayen ‘fom’ din takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya kai milyan 250 a zabe na gaba

Akwai alamu da ke nuni da cewa jam’iyyar APC na iya kara kudi a farashin ‘fom’ din takarar ‘yan siyasa a kakar zabe mai zuwa kamar yadda jaridar Daily Trust ta tattaro.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da dama tun farkon kafa jam’iyyar ta APC a 2014, farashin sayar da ‘fom’ din takara ke ta hauhawa. 
A shekarar 2014 ana tsaka da kakar zaben 2015, jam’iyyar ta sayar da ‘fom’ din takarar shugaban kasa kan kudi Naira milyan 27.5, sai na Gwamna kan kudi Naira milyan 5.
A zaben 2019 kuwa, jam’iyyar ta APC ta sayar da ‘fom’ din takarar shugaban kasa kan kudi Naira milyan 45 da Gwamna kuwa Naira milyan 22.5. Bayan nan, a zaben 2023 sai ga ‘fom’ din ya kai Naira milyan 100 ga mai takarar shugaban kasa da Naira milyan 50 ga masu takarar Gwamna a jam’iyyar.
Wasu jiga-jigan jam’iyyar APC sun yi zargin cewa ana nan ana kokarin kara wa ‘fom’ din farashi kafin zaben 2027. Sai dai sun yi zargin cewa duk da makudan kudaden da aka tattara, musamman a zaben 2023, har yanzu jam’iyyar ta gaza yin bayanin inda kudin nan suka nufa.
Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar APC mai kula da shiyyar arewa maso yammacin Nijeriya, Salihu Lukman a cikin wata sanarwa, ya koka kan yadda farashin kudin sayar da ‘fom’ din ke ta kara hauhawa, inda ya yi fargabar APC na iya cazar masu takarar shugaban kasa kudin ‘fom’ da suka kai Naira milyan 250 da Naira milyan 125 ga masu neman tsayawa takarar Gwamna.

Hisbah za ta sake zama da ‘yan fim a karo na biyu

https://drive.google.com/uc?export=view&id=1Qspbk9s9BWkZfM8QV8pEY2uvkh6tNRZr.
Hukumar Hisbah a jihar Kano za ta sake shirya wani sabon zama a karo na biyu da yan Kannywood.
A Litinin din makon nan ne dai aka yi zaman da ya’yan kungiyar ta Kannywood. 
Gidan Rediyon Nasara da ke Kano ya ce hukumar Hisbah ta ce za a yi zaman ne ta sigar aika masu gayyatar kamar yadda suka yi korafin cewa gayyatar farko an yi masu ne ba bisa ka’ida ba.

Buhari bai bar sisin-kwabo a lalitar gwamnatin Nijeriya ba – Nuhu Ribadu

Mai ba shugaban Nijeriya shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu ya ce halin karancin kudin da gwamnatin Bola Tinubu ke fuskanta ya faru ne ta dalilin samun babu ko sisi a lalitar gwamnati a lokacin da ya hau kan karagar mulkin kasar watanni da suka gabata.
Sai dai Malam Nuhu Ribadu ya ce duk da halin da aka shiga na karancin kudin, gwamnatin tarayya na yin duk abin da ya kamata wajen ganin tsaron kasa ya inganta a sassan kasar nan.
Mai ba shugaban kasar shawara ta musamman ya yi wannan furucin ne a Abuja wajen taron hedikwatar tsaro na shekara-shekara.
Wannan taron dai ya samu halartar ministan tsaro Badaru Abubakar da karamin ministan tsaro Bello Matawalle da manyan hafsan sojin Nijeriya da sauransu.
Malam Nuhu Ribadu ya tabbatar wa da sojojin cewa gwamnatin tarayya ba za ta gajiya ba wajen ganin ta shiga ta fita don ta samar da kayan aiki don inganta tsaron kasa.
Ya ce “a zahirin gaskiya, muna fuskantar matsalar kudi. Ya kyautu in sanar da ku. Sannan yana da kyau ku sani cewa mun gaji wani matsanancin yanayi, abin da nake nufi, babu ko sisi a lalitar gwamnatin lokacin da muka karbi mulki”.

Babu kishin kasa a yajin aikin NLC/TUC – Tinubu

 

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya ce bai ji dadin yadda kungiyar kwadago ta NLC da TUC suka yanke hukuncin fara yajin aiki daga safiyar ranar Talata 14.11.2023. A  cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Bayo Onanuga ya fitar gwamnati ta ce ba ta ji dadin yadda ‘yan kwadagon suka yi gaban kansu duk da umurnin kotu na hana su tsunduma yajin aikin. 

An dakatar da jarumi Malam Ali Kwana 90 daga fim a Kano

https://drive.google.com/uc?export=view&id=1drh05vIDp2W-UM4V2uNxbnsdgYkfr-2S
Hukumar Tace Fina-finai ta Kano ta dakatar da Jarumi Abdul Saheer da aka fi sani da Malam Ali Kwana Casa’in daga Fina-finan Hausa har tsahon Shekaru biyu.
Gidan Rediyon Freedom ya ce hukumar tace hakan ya biyo bayan korafe-korafen da aka yi a kansa na cewa yana yada bidiyon batsa a kafafen sada zumunta.
Hukumar ta ce ta gayyace shi amma ya bijirewa amsa gayyatar ta.