Tuesday, April 7, 2026
Home Blog Page 483

Tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar Zamfara ne a gabana – Gwamna Dauda

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawan Dare ya ce har yanzu bai yi kasa a guiwa ba wajen tabbatar da rantsuwar da ya sha ta kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar Zamfara.
Dauda Lawan Dare na magana ne a Masarautar Maru ta jihar da ya je ziyarar ta’aziyya da jajantawa bisa hare-haren ta’addanci da suke fama da su.
Gwamnan ya yi ta’aziyya ga Masarautar da daukacin al’ummar wannan masarauta bisa ayyukan ta’addanci da ke wakana ga al’ummar yankin.
A yayin ziyarar, Gwamnan tare da Mai Martaba Sarkin Maru Alhaji Abubakar Gado sun gudanar da sallar Juma’a a babban masallacin garin, inda aka gabatar da addu’o’i na samun zaman lafiya a yankin da ma jihar bakidaya.

‘Yan bindiga na tursasa wa manoma su biya haraji kafin su girbe amfanin gonakinsu a Kaduna

‘Yan bindiga na tursasa wa wasu manoma a wasu kauyukan jihar Kaduna su biya haraji kafin su kyale su, su girbe amfanin gonakinsu da suka noma a daminar bana.
Kauyukan da lamarin ya shafa sun hada da na Kidandan da Galadima a karamar hukumar Giwa, sai mutanen kauyen Angular Fala’u da na Kerawa suka ce kodayaushe ‘yan ta’addar na yin garkuwa da su a duk lokacin da suka je girbin amfanin gonakinsu.
Wani mazaunin kauyen Kidandan Malam Jamil, ya ce al’ummar kauyensu na biyan kudin harajin da suka kai Naira 70,000 zuwa 100,000 don su girbe amfanin gonakinsu.
Ya ce wadanda suka ki ko gaza biya, za a sace su ko a kashe ko kuma ‘yan bindigar su kwace amfanin gonakin.

Hukumar CCB za ta gurfanar da Muhyi Magaji Rimin Gado

Hukumar kula da da’ar ma’aikata ta Code of Conduct Bureau, ta sanar cewa ta kammala dukkanin shirye-shirye na gurfanar da shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano da aka fi sani da ‘Anti Corruption’ a gabanta.
Hukumar kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito, ta sanar cewa a ranar Alhamis ta makon gobe 16 ga Nuwamba ne hukumar za ta gurfanar da Barr Muhyi.
Wata majiya daga hukumar ta ce za a gurfanar da Barr Muhyi ne bisa zargin wasu laifuka na gaza mika mata rubutaccen bayani game da kadarorin da ya mallaka da sauran laifuka.
A wani sammace da Magatakardan hukumar ya aike wa shugaban hukumar, an umurce shi da ya bayyana a gabanta domin amsa wasu tuhume-tuhume guda 10.

Kimiyya ta taimaka wajen rage yaduwar Corona da sauran cutuka – UNESCO

Darakta Janar ta Hukumar Bunkasa Ilimi da Al’adu ta Duniya (UNESCO), Ms. Audrey Azoulay, ta jaddada tasirin da kimiyya ke da shi wajen samar da ingantacciyar duniya. 
Ta bayyana haka ne a cikin wani sakon da ta gabatar na bikin ranar kimiyya ta duniya don haɓaka zaman lafiya da ci gaba a ranar 10 ga Nuwamba, 2023.
A cewarta, kimiyya ta taimaka wajen rage yaɗuwar cututtuka kamar COVID-19, baƙon dauro, da foliyo ta hanyar samar da allurar rigakafi.
Haka kuma, ta ce UNESCO na tunawa da ranar Kimiyya ta Duniya ce don inganta zaman lafiya da ci gaba a kowace shekara tare da jaddada muhimmancin da kimiyya take da shi. 
A bana, bikin ya ninka sau biyu, yayin da ya zo daidai da lokacin bikin shekarar ilimi ta ƙasa da ƙasa don samar da ci gaba mai ɗorewa, wadda daga bisani za ta shiga cikin shekaru goma na kimiyyar ƙasa da ƙasa don ci gaba mai dorewa daga 2024 zuwa 2033.
Bugu da ƙari ari, Ms. Azoulay ta bayyana jajircewar UNESCO wajen tallafa wa bincike na kimiyya, wanda aka misalta ta hanyar shawarwarinta na 2021 a kan haɓaka kiniyy.
“UNESCO tana aiki domin haɓaka daidaiton jinsi a fagen kimiyya, gami da shirye-shirye a Afirka da Caribbean tare da haɗin gwiwar gidauniyar L’Oréal.
“A cikin shekarun da suka gabata, wannan hadin gwiwa ya karfafa ayyukan masana kimiyya, mata fiye da 4,100 da suka fito daga kasashe sama da 110”. In ji ta.
Wannan shi nebabban jigon ranar Kimiyya ta Duniya ta wannan shekara kuma za ta kasance jigon taron ministocin da zai gudana a hedikwatar UNESCO a ranar 13 ga Nuwamba, 2023. 
Manufar wannan taron shi ne a karfafa dogaro ga kimiyya ta hanyar magance mishkiloli da suka jiɓanci ilimin kimiyya, sada kimiyya daidai da bukatun al’umma, da kuma ba da kariya da tabbatar da ‘yancin masana kimiyya.

Hisbah a Kano ta kori wani jami’inta

Hukumar Hisbah a jihar Kano ta sanar da korar daya daga cikin ma’aikatanta bayan samunsa da laifin yi mata zagon-kasa a yakin da take yi da aikata badala a jihar.
Babban kwamandan hukumar Shekh Aminu Daurawa ya sanar da hakan ga manema labarai a Kano, inda ya ce akwai karin wasu jami’ai biyar da ake bincike a kansu.
Ya ce mutumin da aka kora din na hada baki da bata-gari wajen kitsa wata kitimirmira a jihar.
Sheikh Daurawa ya ce tun bayan nada shi kwamandan Hisbah, ya dukuba wajen tsaftace ayyukanta ta hanyar zakulo bare-gurbi.

NLC ta saka ranar da za a tsunduma yajin aiki a Nijeriya

Kungiyar kwadago ta NLC a Nijeriya ta saka ranar Talata 14 ga watan Nuwamba, 2023 a matsayin da za ta tsunduma yajin aiki na sai baba-ta-gani.
Kungiyar ta yanke shawarar tsunduma yajin aikin ne bayan taron jiga-jigan kungiyar da ya gudana a Abuja.

Ministan Tinubu ya yi nasarar zama Sanata a kotun daukaka kara

Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta tabbatar wa da Simon Bako Lalong kujerar Sanatan da ke wakiltar Plateau ta Kudu a majalisar dattawan Nijeriya.
Simon Lalong dai shi ne ministan kwadago a gwamnatin Bola Ahmad Tinubu, da ya yi takarar Sanata a karkashin jam’iyyar APC.
Kotun ta yi watsi da bukatar Napoleon Bali na jam’iyyar PDP.
Dama dai kotun sauraren kararrakin zabe ta ayyana Simon Lalong a matsayin wanda ya yi nasarar bayan da ta yanke hukunci.

‘Yan bindiga sun bude wuta kan masu Mauludi a Katsina, sun kashe kusan 20 sun sace da dama.

‘Yan bindiga da ba a san adadinsu ba, sun afka kauyen Kusa da ke cikin karamar hukumar Musawa a jihar Katsina cikin daren Lahadi, inda suka hallaka mata da kananan yara sama da 20.
‘Yan bindigar da suka farmaki inda ake taron Mauludi, sun kuma yi awon-gaba da mutanen da ba a san adadinsu ba a halin yanzu.
Bugu da kari, rahotannin da jaridar Daily Trust ta tattara sun ce karin wasu mutane kusan 17 sun samu raunuka, inda aka garzaya da wasu babban asibitin Musawa wasu kuma aka nufa da su asibitin kashi na Katsina.
Wani shaidar gani da ido daga garin, ya shaida cewa ‘yan bindigar sun bude wa masu taron Mauludin da misalin karfe 11:05 na daren Lahadi.
Ya ce kafin jami’an tsaro su kawo dauki, maharan sun tsere , ba a tarar da ko daya ba.
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta hannun mai magana da yawunta ASP Aliyu Abubakar Sadiq, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce maharan sun raunata kusan mutane 18.

SERAP ta maka Shugaba Tinubu kotu kan wasu kudade

Kungiyar nan da ke rajin ganin an tabbatar da adalci ta SERAP ta kai karar shugaban Nijeriya Bola Tinubu bisa zargin ya gaza bincikar zargin yin wadaka da kudaden gyaran matatun man kasar nan da karin wasu kudade da aka samu daga man fetur a shekarun 2020 da 2021.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mataimakin daraktan kungiyar Kolawole Oluwadare da aka raba wa manema labarai a Abuja.
Wannan zargi na Shugaban kasa ya gaza bincikar wadannan kudade dai na cikin wani rahoto da kungiyar tabbatar da gudanar da adalci a tsakanin masana’antu ta fitar a shekarar 2021.
Oluwadare ya ce kungiyar na neman kotu ta tilasta wa Shugaban kasa, cewa ya umurci hukumomin yaki da cin hanci da rashawa na su binciki kamfanin NNPC kan wannan batu.
A cikin takardar karar da suka shigar mai lamba FHC/L/CS/2334/2023, SERAP na son kotu ta ba Shugaba Tinubu umurni kamar yadda kundin mulkin kasa ya tanadar na a binciki kudin da suka kai Dala bilyan 15 na kudaden shigar da aka samu ta bangaren man fetur da Naira bilyan 200 da aka kasafta don gyaran matatun man kasar nan da suka yi batan-dabo.

An yi yunkurin garkuwa da wani mutum, ‘yan sanda sun hana a Katsina

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta sanar cewa jami’anta sun yi nasarar dakile kokarin sata da garkuwa da wani mutum mai suna Tukur Adamu na kauyen Masaku cikin karamar hukumar Kankara ta jihar.
Mutumin mai shekara 40, kamar yadda sanarwar da ta fito daga mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan ASP Aliyu Abubakar Sadiq ta ce hakan ta faru ne bayan samun kiran gaggawa da jami’anta suka yi, cewa masu garkuwa da mutane na yunkuri baje hajarsu a kauyen Masaku, amma cikin lokaci suka je suka dakile wannan yunkuri har suka ceto wannan mutumi ba tare da ya rasa ransa ba.
Sai dai sanarwar ta ce mutumin ya samu rauni ta dalilin harbin bindiga, amma dai an garzaya da shi asibiti, yanzu haka yana karbar magani.
Sanarwar ta ce kwamishinan ‘yan sandan jihar CP Aliyu Abubakar Musa ya yaba da irin kwazon jami’an da suka ceto mutumin, ya kara da cewa ‘yan sanda a jihar Katsina ba za su yi kasa a guiwa ba wajen tsare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.