Tuesday, April 7, 2026
Home Blog Page 484

Mun gamsu da jagorancin Kwankwaso a tafiyar NNPP – Jiga-jigan Kwankwasiyya

Shugabannin Jam’iyyar NNPP Na Ƙasa Reshan Arewa Maso Yamma Ƙarƙashin Jagorancin Hon. Shehu M. Bello (Shehun Garu) Sun Gudanar Da Taro A Jihar Kaduna.
Taron shugabancin jam’iyyar ta NNPP reshen arewa maso yamma tare da masu ruwa da tsaki na shiyyar a jiya a Kaduna sun gudanar da taro na musamman inda ya haɗa da mataimakin gwamnan jihar Kano, yan majalisun jiha, tare da manyan kwamishinoni.
Maƙasudin taron shine kaɗa “Kuri’ar Amincewa” da Shugaban Kasa kuma Dan Takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar NNPP a 2023- Sanata Engr Rabi’u Musa Kwankwaso, Kwamitin Ayyuka na kasa kuma Shugaban riko na NNPP na kasa.
 Hakan dai na zuwa ne jim kadan bayan wasu sun sanar da fitar da Jam’iyyarsu ta kasa daga jam’iyyar.
Haka kuma shugabannin shiyyar Arewa maso Yamma sun yi alkawarin ladabtar da duk wanda aka kama yana aikata irin wannan aika-aika a cikin jam’iyyar.
 Mahalartan sun taya Gwamnan Jihar Kano murna bisa duk wani kyakkyawan aiki da yake yi na kokarin cika dukkan wani alkawari da ya dauka.
Haka-zalika sun kuma taya mambobinsu a Majalisar Dokoki ta kasa murnar samun wasu kujerun manyan kujeru masu yawa da suka haɗar da kujerun Chairman da mataimakansu.
Sun kuma taya ‘yan majalisar wakilansu murnar samun nasara a kotuna da kuma wadanda suka samu nasara a kotun daukaka kara.
 A karshe sun jaddada cewa duk waɗannan nasarori sun samu ne saboda jajircewa irinta shugabansu kuma jagoransu a matakin kasa baki daya, tare da shugaban mu na kasa a NNPP hakan ke ƙara bamu cikakken numfashi!  Haka idan kuma ba tare da shi ba, to ta mutu baki daya.

Sojoji da DSS sun bankado wani yunkurin kai hari a Kano

Rundunar sojin Nijeriya hadin guiwa da jami’an tsaron ciki na DSS sun dakile wani yunkurin kai hari a karamar hukumar Gezawa ta jihar Kano.
Jami’an hukumomin biyu dai sun gudanar da aikin dakile harin da aka tsara da sanyin safiyar Juma’a, inda suka kama mutane biyu da ake zargi da kokarin kitsa harin.
A cikin wata sanarwa daga daraktan yada labarai na rundunar sojin Nijeriya Nwachukwu Onyeama, ta ce a yayin samamen, an yi nasarar kwato bindigu samfurin AK 47 guda biyar, da sauran kayan kai hari.

‘Yan Nijeriya sama da milyan 90 ba su samun hasken lantarki – Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Ahmad Tinubu ya ce shekaru 10 bayan cefanar da sashen lantarki na kasar, har yanzu akwai mutane sama da milyan 90 da ba su samun lantarkin yadda ya kamata.
Da ya ke magana a Abuja, Shugaba Tinubu ya koka cewa babban layin lantarki na ‘National Grid’ na wadatar da kaso 15% kacal na al’ummar Nijeriya.
Ya ce hakan ke barin gidaje da masana’antu da dama su dogara da janaretoci da sauran hanyoyin samar da makamashi.

Na fi Akpabio kwarewa da gogewa a aikin majalisa – Ndume

Sanata Ali Ndume mai tsawatarwa na majalisar dattawan Nijeriya, ya sanar cewa ya fi shugaban majalisar Sanata Godswill Akpabio gogewa da kwarewa a aikin majalisa.
Sanata Ndume da ke wakiltar Borno ta Kudu ya sanar da hakan ne a cikin wani shirin gidan talabijin na Channels, Abuja.
Tun dai a shekarar 2011, Sanata Ali Ndume ya ke majalisar dattawan, amma shi Akpabio ya fara zuwa majalisar dattawan ne a shekarar 2015.
Sanata Ndume dai ya sanar da dalilinsa na ficewa daga majalisar a lokacin da Akpabio ya katse shi lokacin da ya ke magana a majalisar.

Ana yunkurin tsige Gwamnan jihar Rivers Sim Fubara

Yunkurin tsige Gwamnan jihar Rivers Sim Fubara ya sa an sauke jagoran majalisar dokokin jihar (House Leader) Edison Ehie da sanyin safiyar Litinin din nan.
Dama dai a 10pm na daren Lahadi, wata gobara ta tashi a ginin majalisar da har yanzu ba a san musabbabin tashin ta ba.
Gwamnan jihar ta Rivers Sim Fubara ya ziyarci majalisar da sanyin safiyar Litinin, inda ‘yan majalisar kowa ya watse a lokacin da aka fara harba hayaki mai sa hawaye na ‘tear gas’.

Ana fatar yi wa jarirai 797,209 rajista a Katsina

Hukumar kidayar al’umma ta Nijeriya hadin guiwa da Asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF sun kuduri aniyar yi wa jarirai 797,209 rajistar haihuwa a jihar Katsina.
Jami’ar Asusun UNICEF Mrs Ogbodo Adaku ta sanar da hakan a lokacin taron horar da wadanda za su yi aikin rajistar a ranar Asabar.
Ta ce kusan ma’aikatan wucin-gadi 1,083 ne za su yi aikin rajistar a fadin mazabu 361 da ake da su a kananan hukumomi 34 na jihar.
Mrs Adaku ta ce za a yi wannan aikin kidayar jarirai a jihohi 23 hada babban birnin tarayya, Abuja.
Ta kara da cewa ana kokarin ganin an yi wa yara milyan 12 rajista a fadin Nijeriya.

Matsin rayuwa ya sa ana samun mutanen da ke kwana 3-4 ba su ci abinci ba – Mustapha Inuwa

Tsohon Sakataren Gwamnatin jihar Katsina Mustapha Muhammad Inuwa ya ce yanzu ana wani yanayi na matsin rayuwa da har ta kai mata na cewa mazajensu sun rasu don a taimake su alhali mazan na nan da ransu.
Mustapha a wata zantawa da ya yi wasu kafafen yada labarai na zamani a Katsina, ya ce yanzu haka ana samun mutanen da ke kwana 3-4 ba su ci abinci ba, hasalima, ba su kirguwa a cikin al’umma a wannan yanayin da ake ciki.
Mustapha Inuwa wanda ya yi wa APC takarar Gwamna a jihar Katsina a zaben 2023, ya koka kan irin halin karancin tsaro da sassan jihar ke fama da shi, inda ya yi addu’ar duk masu amfana da yanayin matsalar tsaro da ake ciki, “muna addu’ar Allah Ya yi mana maganinsu”.
Ya koka cewa idan aka ci gaba da tafiya haka a kasar nan, ba a san halin da ‘ya’ya da jikoki za su shiga ba a rayuwarsu ta gaba.
Mustapha Muhammad Inuwa ya ce “Ni dan siyasa ne, ba dan takara ba. Tun daga lokacin da aka kammala zabe, har ya zuwa yanzu, ban taba tafiyar da na kwana bakwai bani Katsina ba. Kuma ina iya wata biyu cur, ban bar Katsina ba. Gidana a bude yake ga kowa, haka ofis dina, duk rana sai na je”.

‘Yan sanda sun ceto mutane 4 da aka yi garkuwa da su a Katsina

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta sanar cewa hadin guiwa da rundunar soji sun yi nasarar ceto mutane 4 da aka yi garkuwa da a su a sassa daban-daban na jihar.
A sanarwar da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya fitar da DCL Hausa ta samu kwafi, ta ce an yi nasarar ceto mutanen ne a lokacin da jami’an ke aikin sintirin ‘patrol’ ta wajen kauyen Dankolo na karamar hukumar Dandume ta jihar.
Sanarwar ta rawaito kwamishinan ‘yan sandan jihar Katsina CP Aliyu Musa ya yaba wa jami’an da irin aikin da suka gudanar na yadda suka nuna kwarewa wajen gudanar da aikin.
Sannan an kai mutanen asibiti don duba lafiyarsu da tuni an mika su ga iyalansu.

Mutane milyan 283 na kwana da yunwa a Nahiyar Afrika – Adesina

Shugaban bankin bunkasa Nahiyar Afrika Dr Akinwumi Adesina ya sanar cewa mutane milyan 283 na kwana da yunwa a Nahiyar Afrika.
Dr Adesina na magana ne a taron daidaita farashi a kasar Amurka, inda ya ce bankin ya ware wasu kudi Dala bilyan 1 don tallafar jihohi 24 na Nijeriya.
Ya ce hakan wani kari ne daga Dala Milyan 520 da aka tura don inganta aikin gona da zummar abinci ya wadata.
Shugaban bankin ya ce an yanke shawarar kai wannan dauki a Nijeriya don a bunkasa sassan aikin gona saboda yawan kasar noma da Allah Ya huwace mata.

Za a yi wa ‘yan mata milyan 7.7 rigakafin cutar kansar mahaifa a Nijeriya

Nijeriya a hukumance ta shigar da allurar rigakafin cutar HPV a cikin tsarin rigakafinta na yau da kullum, da nufin kai wa yara mata miliyan 7.7 agaji cikin zagaye guda na allurar rigakafin cutar, wanda ya kasance mafi girman irinsa a yankin Afirka.
Ministan Lafiya da Walwalar Jama’a, Muhammad Ali Pate, ya bayyana matukar damuwarsa kan cutar ta kansar mahaifa, yana mai cewa, “Asarar mata kusan 8,000 a duk shekara daga cutar da ake iya rigakafinta ba abu ne da za a amince da shi ba.“.
Pate ya jaddada cewa ceton rayuka da tabbatar da ingantaccen kiwon lafiya su ne jigon kudirin inganta lafiyar al’umma na shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Ya kuma bayyana cewa, “A matsayina na uba, ni kaina, ina da ‘ya’ya mata hudu, dukkansu sun yi allurar rigakafin cutar HPV guda daya don kare su daga cutar kansar mahaifa.
“Ina so in yi kira ga ‘yan uwanmu iyaye da su tabbatar da cewa ‘yan matanmu sun amshi allurar rigakafin kamuwa da cutar kansar mahaifa”.
‘Yan mata masu shekaru 9 zuwa 14 za su sami kashi ɗaya na maganin rigakafin na HPV, wanda yake da tasiri wajen hana kamuwa da cutar.
Daga nau’ukan maganin rigakafin akwai HPV 16 da 18.
Cutar kansar mahaifa ita ce ta biyu da take sanadin mutuwar mata masu shekaru 15 zuwa 44.
Wakilin WHO a Nijeriya, Dokta Walter Kazadi Mulombo, ya ce, “Wannan wani muhimmin lokaci ne a kokarin da Nijeriya ke yi na rage yawaitar kansar mahaifa – daya daga cikin cutar kansar da za a iya kawar da su ta hanyar alluran rigakafi.”
“Mun himmatu wajen tallafa wa gwamnati ta kara samun damar yin amfani da allurar rigakafin cutar ta HPV don kare lafiya da jin dadin rayuwar mata a nan da wasu shekaru masu zuwa.“.
UNICEF ta taka muhimmiyar rawa a wannan shiri, inda ta siyo rigakafin cutar ta HPV kusan miliyan 15 a madadin Gwamnatin Nijeriya. Bugu da kari, UNICEF ta samar da kayan fadakarwa da suka hada da radiyo da tallace-tallace na Talabijin a cikin harsunan gida da yawa don kawar da jita-jita game da rigakafin.
Taron kaddamar da shirin rigakafin na tsawon kwanaki biyar, ya kunshi makarantu da al’umma a fadin jihohi 16 da kuma Abuja.
A haka kuma, maganin zai zama wani ɓangare na tsarin rigakafi na yau da kullum a cibiyoyin kiwon lafiya. 
Ana sa rai Kashi na biyu zai fara aiki a watan Mayun 2024, wanda zai ƙunshi jihohi 21.
Ana yin allurar rigakafin cutar HPV kyauta, wanda Ma’aikatar Kiwon Lafiya ta Tarayya, tare da tallafin Gidauniyar Gavi, the Vaccine Alliance, UNICEF, WHO, da sauran abokan haɗin gwiwa suka haɗa hannu suka samar.