Tuesday, April 7, 2026
Home Blog Page 485

Sai da Buhari ya dagula komai a Nijeriya kafin ya sauka – Rarara

Sanannen mawakin siyasar nan a arewacin Nijeriya Dauda Adamu Abdullahi da aka fi sani da Rarara ya ce gwamnatin da ta gabata ta tsohon shugaban kasa Muhammad Buhari ta lalata kusan kowane bangare na kasar.
Rarara a wata ganawa ta musamman da manema labarai a Kano, ya ce ya ba gwamnatin ta Buhari shawarwari daban-daban na yadda za ta inganta ayyukanta, amma ba ta dauki shawara ko daya daga bangare na ba.
Mawakin da ya yi jawabi mai kama da ya dawo rakiyar gwamnatin da ta shude, ya nuna kamar yana nadamar irin goyon bayan da ya bata.
Ya yi karin hasken cewa bai samu sisin-kwabo a gwamnatin Buhari ba, ya kara da cewa duk wanda ya ke da hujjar cewa ya samu kudi gwamnatin Buhari ya zo ya nuna.
Ta fuskar ba da gudunmuwa a wajen kafa sabuwar gwamnatin Tinubu kuwa, mawaki Rarara, ya ce tsoffin gwamnonin Katsina Aminu Masari da na Kano Abdullahi Ganduje ne kadai za su iya hada kafada da shi wajen tallafar nasarar gwamnatin Tinubu arewa.
Sai dai Dauda Adamu ya yi karin hasken cewa akwai makiya Tinubu da aka nada mukamai daban-daban a gwamnatinsa.

Zubar da mutunci ne dan sanda ya rika karbar N100 daga hannun direbobi

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Nijeriya Olumuyiwa Adejobi, ya caccaki jami’an da ke karbar Naira 100 a kan hanya daga hannun masu ababen hawa, inda ya ce jami’an da suke aikata haka suna zubar wa da kansu mutunci ne.
A cewarsa ya kamata ‘yan sandan da ke yin wannan aika-aika su daina saboda suna cin hanci da rashawa.
Adejobi ya bayyana hakan ne a yayin da yake mayar da martani ga wani mai amfani da shafin Tuwita (X) wanda ya tambayi dalilin da ya sa ‘yan sanda ke karbar Naira 100 daga masu amfani da hanyar.

Kaso 60% na al’ummar duniya sun rungumi amfani da shafukan sada zumunta – UNESCO

Darakta Janar na Hukumar Bunkasa Ilimi da Al’adu ta Duniya (UNESCO), Ms. Audrey Azoulay, ta ce a shekarar 2023, kashi 60% na al’ummar duniya mai jimlar mutane biliyan 4.75, sun rungumi amfani da shafukan sada zumunta wajen bayyana abubuwan da suka shafe su da neman amsoshin tambayoyi da sauran mu’amala.
Ms. Audrey, wanda Darakta na Hukumar UNESCO ta Nijeriya, Mista Diallo Abdourahamane, ya wakilta, ta bayyana hakan a yayin bikin Ranar Amfani da Kafofin Yada Labarai da Yada Bayanai ta bana, ranar Laraba, a Abuja.
Ta yi bayani a kan alfanun hanyoyin sadarwa na zamani da kuma kalubalen da suke haifarwa ga al’umma.
A cewarta, “Ana sa ran UNESCO nan ba da jimawa ba za ta fitar da dabarun daidaita tsarin dandamali na fasahar sadarwa, da samar da umarni na bai-daya da za a rika amfani da shi wajen auna kididdiga, yadda ake aiki da harkoki daban-daban, da tabbatar da ingancin tattara bayanai da adana su, da kiyaye sirri da kuma tabbatar da ‘yancin dan adam.”
“UNESCO, ta himmatu wajen inganta tunani mai mahimmanci da kuma kauce wa amfani da tsattsauran ra’ayi mara misali a tsakanin jama’a da yawa,” in ji ta.
A nashi jawabin, Ministan yada labarai, Mohammed Malagi, wanda Misis Comfort Ajiboye ta wakilta ya ce, “a yau, muna rayuwa a wani zamani da ake tafiyar da komai cikin sauri ta hanyar fasahar zamani, shi ya sa musayar bayanai ke gudana ba tare da wahala ba.
“Amfanin hakan ga duniya, abu ne mai girma wanda ba za a iya musantawa ba kuma wanda ya ba mu damar yin hulɗa tare da mutane a duk Nahiyoyi, da kuma samun damar koyon ilimi mai yawa, da kawo canji mai kyau a cikin al’ummarmu.
“Ilimi game da harkar yada labarai ya kasance babban jagora ga ci gaban ƙasa wajen amfani da damammaki marasa iyaka waɗanda intanet da sauran kafofin fasahar sadarwa na zamani suke bayarwa”.
Har ila yau, a yayin taron dai, an yi wata tattaunawa da mahalarta game da yadda za a iya amfani da ilimin amfani da kafofin watsa labarai don kawo babban ci gaba a cikin al’umma da kuma yadda za a iya magance rashin fahimta.

‘Yan ta’adda sun kashe mutane 6 a wani sabon hari a Dansadau jihar Zamfara

Wasu mutane dauke da muggan makamai sun mamaye tare da kashe mutane kusan 6 a kauyen Dansadau na karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara.
A ganawar da Radio Nigeria ya yi da wasu shaidun gani da ido, sun sanar cewa barayin dajin sun kai hari a kauyen da misalin karfe biyu na ranar Talata, a lokacin da mutanen ke sallar azahar.
Rahotanni sun ce mutanen sun je kauyen bisa babura dauke da makamai su na harbin kan mai uwa da wabi, suka kashe mutanen tare da sace daya.
Shaidun suka ce ‘yan ta’addar sun fara harbi a tashar mota, sai suka fantsama zuwa kasuwa suna harbe-harbe suka jikkata da dama.
Bayanai sun ce mutane kusan 4 sun samu raunuka inda suke karbar magani a babban asibitin Dansadau.

Nijeriya na bin MTN bashin kudin haraji Naira bilyan 57.5

Kotun da ke sauraren kararrakin da suka shafi haraji da ke zamanta a Lagos ta umurci kamfanin sadarwa na MTN da ya biya gwamnatin kasar kudin da suka kai Dalar Amurka milyan 72,551,059 kwatankwacin Naira bilyan 57.5 (idan an sayar da Dalar kan kudi Naira 795).
An dai umurci kamfanin ya biya wadannan kudaden da aka yi lissafin ba a biya ba daga shekarar 2007 zuwa 2017 ta hannun hukumar tattara kudaden haraji ta FIRS.
Sai dai kotun ta sahale wa kamfanin da kada ya biya Dala milyan 21,039,807 daga cikin kudin a matsayin kudin ruwa da kuma na jan kafa.
Tawagar alkalai biyar, karkashin jagorancin Prof A.B Hamed ne suka yanke wannan hukunci bayan da hukumar FIRS ta gabatar da koken hakan gaban kotu.

Majalisar Dinkin Duniya ta cika shekaru 78 da kafuwa

Babban Jami’in Majalisar Ɗinkin Duniya a Nijeriya, Mista Matthias Schmale, ya gabatar da jawabi domin bikin ranar Majalisar Dinkin Duniya, wanda ake gudanarwa kowace shekara don tunawa da muhimmiyar ranar da Yarjejeniyar Kafa Majalisar Dinkin Duniya ta fara aiki a ranar 24 ga Oktoba,1945.
A jawabin nasa, babban jami’in ya yi tsokaci a kan ka’idoji da ayyukan Majalisar Dinkin Duniya da kuma kalubalen da duniya ke fuskanta a yau.
Mr. Schmale ya fara ne da tabo batun yadda aka bude taron Yarjejeniyar Kafa Majalisar Dinkin Duniya, wanda ya jaddada cewa babban kudirin kafa hukumar shi ne “ceto al’ummar duniya daga bala’in yaki.” 
A shekarar 2023, ya bayyana cewa, wannan kudiri na fuskantar kalubalen da ba a taba ganin irinsa ba, inda tashe-tashen hankula suka shafi miliyoyin mutane a wurare kamar Ukraine, Falasdinu, Isra’ila, Sudan da Myanmar, da kuma korar shugaban Nijar da aka yi a kwanan baya.
Babban Jami’in ya bukaci kasashen kungiyar su sake jaddada sadaukarwarsu da girmama Yarjejeniyar ta Majalisar Dinkin Duniya, da kuma sabunta kokarinsu na inganta zaman lafiya, yana mai bayyana cewa, wannan shi ne muhimmin sakon Babban Sakataren MDD Antonio Guterres a bana.
Ya kuma yaba wa ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniya a Nijeriya, wadanda suke aiki ba tare da gajiya ba, a lokuta da dama a cikin mawuyacin hali, domin cika burin Majalisar Dinkin Duniya na samar da zaman lafiya da wadata ga kowa da kowa.
Ya kuma tuna tare da bayyana alhini kan ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniya guda 23 da suka rasa rayukansu a harin ta’addancin da aka kai a ofishin MDD da ke Abuja a shekarar 2011 da kuma abokan aikinsu da ke ci gaba da sadaukarwa a yanayi na tashe-tashen hankula.
Mr. Schmale ya kuma bayyana kudira MDD kan cimma ajandar 2030 da kuma manufofin ci gaban zamani masu dorewa (SDGs), tare da jaddada ka’idar kowa ya bayar da gudunmawa a dama da shi ba tare da barin kowa a baya ba. 
Ya yi alkawarin mayar da hankali wajen magance matsalolin da suka shafi yara da ba su zuwa makaranta, rashin abinci mai gina jiki, cin zarafin mata da ‘yan mata, da bukatun al’umma masu rauni da suka hada da tsofaffi, nakasassu, da ‘yan gudun hijira.
Har ila yau, ya yi kira ga shugabannin gwamnati da su hanzarta aiwatar da ajandar 2030 sannan ya yi magana game da dimbin damar da Nijeriya ke da ita ta bunkasa da ciyar da kanta gaba, yana mai jaddada bukatar mayar da hankali wajen aiwatar da lamarin bilhakki. 
Taken bikin ranar Majalisar Dinkin Duniya na bana, “Hadin gwiwar Majalisar Dinkin Duniya tare da Nijeriya don Cimma Tsarin SDGs,” ya mayar da hankali ne a kan bayyana mahimmancin haɗin gwiwa da sauke nauyin da ke wuyar juna.
Babban Jami’in ya jaddada kokarin da majalisar ke yi na kara samun kayan aiki don magance matsalolin kiwon lafiya kamar cuta mai karya garkuwar jiki (AIDS), da tarin fuka, da zazzabin cizon sauro, da kuma tallafa wa samar da zaman lafiya, magance rikice-rikice, da inganta hanyoyin sa ido ga rundunar ‘yan sandan Nijeriya.
Bugu da kari, ya amince da ayyukan jin kai a jihohin Borno, Adamawa, da Yobe, inda aka bayar da agajin gaggawa ga marasa galihu miliyan 3.6 a farkon rabin shekarar nan.
Mr. Schmale ya kuma tunatar da kowa da kowa cewa dole ne dukkanin ayyukan ci gaba su kasance daga tushe a cikin mutunta hakkin Dan’adam, bayar da shawarar ‘yancin fadin albarkacin baki, da kuma dakile kalaman batanci da kiyayya.
Mr Schmale ya kammala jawabinsa da neman hadin kai da hadin gwiwa tsakanin gwamnati, kungiyoyin fararen hula, bangarori masu zaman kansu, da kafafen yada labarai wajen tabbatar da akidu da ganin kimar Majalisar Dinkin Duniya don ci gaban mutanen duniya da samun wadata, da zaman lafiya.

Tsadar rayuwa ta sa wata mata sayar da jikanta kan kudi Naira dubu 50 a Nijeriya

Wata mata mai suna Mrs Oluchukwu Nwosu ta sayar da jikanta dan watanni uku kan kudi Naira dubu 50, inda ta zargi halin matsin rayuwa da cire tallafin man fetur ya ingiza ta a Nnewi ta jihar Anambra.
Mrs Nwosu ta ce diyarta da ta haifi wannan jariri, dama ta taba haihuwar wasu biyu a baya, ta sakar mata, tana ta wahala da su, inda ta ce ba ta da karfi, yanzu haka wadancan yaran biyu na gidan marayu na Awka.
Matar na neman yafiya, sai dai ta ce tana cikin halin matsin rayuwa tun bayan da diyarta ta haihu, ba su iya cin abinci sau uku a rana.
Tochukwu Asiegbu ne dai ake zargin ya sayi wannan jariri sabuwar haihuwa. Sai dai kwamishinar mata ta jihar Anambra Lfy Obinabo ta tabbatar da cewa an ceto jinjirin da aka cefanar.

Shugaba Tinubu ya sanar da lokacin da za a fara ba daliban Nijeriya bashin kudin makaranta

Shugaban Nijeriya Bola Ahmad Tinubu ya sanar da a watan Janairun 2024 za a fara ba daliban kasar bashin kudin da za su dauki dawainiyar karatunsu.
Shugaban kasar da ya furta haka a a Abuja wajen taron kula da tattalin arziki, ya ce idan aka aiwatar da hakan, batun yajin aikin malaman jami’o’i zai zamo tarihi.
Shugaban kasar ya kuma yi magana sosai kan yadda gwamnatinsa ta yi tsare-tsare don ganin an saita tattalin arzikin kasar.

Taskar DCL: Zargin Tinubu da danne arewa a mukamai da rigimar Sanata Elisha Abbo da Akpabio

0

Labaran DCL Hausa 16/12/2024

Kotun koli ta yi watsi da karar da ke neman a tsige shugaba Tinubu daga kujerar shugabancin Nijeriya

Hedikwatar tsaron Nijeriya ta musanta rahotanni dake cewa sojin Faransa na shirin kafa sansani a cikin a kasar

Gwamnan jihar Kano ya aike da sunan tsohon shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin da wasu mutune 5 majalisa don nada su mukamin kwamishinoni

Mai gabatarwa: Yahanasu MD Ibrahim

Tinubu ya yi abin a zo a yaba da ya nada kwararre a shugabancin asusun harkokin noma – Umar Abdullahi Yaya

An bayyana nadin Muhammed Abu Ibrahim a matsayin shugaban asusun kula da ci gaban harkokin noma da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya yi a matsayin abinda ya dace, wanda zai samar da ci gaba a fannin noman ƙasar nan.
Sakataren kungiyar masu kiwon kaji na jihar
Katsina, Alhaji Umar Abdullahi Yaya, ne ya bayyana hakan ya yin hira da yan jarida a Katsina.
 
Ya ce wanda aka naɗan, kwararren Akaunta ne, wanda ke da kwarewa kan shugabanci na sama da shekaru 25 a bangarorin harkokin kudi da fasaha da aikin gona.
Umar Yaya ya ce Mr Ibrahim shi ne wanda ya kafa wata cibiya mai suna (Sponge Analytics); wacce ka tattara bayanai kan harkokin noma da samar da mafita.
Malam Ibrahim wanda kafin nadin nasa shi ne mataimakin shugaban cibiyar (Livestock247); cibiyar harkoki da ci gaban dabbobi, irinta na farko a Najeriya.
 
Hakazalika, Ibrahim ya kasance memba a kwamitotin zartarwa na kampanoni da dama da suka shafi fasaha da muhalli da aikin gona da sai sauransu.
Alhaji Umar Yaya ya bayyana nadin a matsayin wanda yazo a kan lokaci, kuma mai karfafa gwiwar matasan ƙasar nan baki ɗaya.