Tuesday, April 7, 2026
Home Blog Page 486

Sai mun yi ‘yan dabaru muke iya biyan albashin ma’aikata – FG

Gwamnatin Nijeriya ta koka kan cewa sai ta yi ‘yan dabaru sannan take iya biyan albashin ma’aikata domin babu kudi a kasa.
Ministan kasafin kudi da tsare-tsare na kasa Atiku Bagudu ne ya bayyana haka ga manema labarai a Abuja. 
Bagudu ya bayyana cewa kasar ta riga ta faɗa cikin wani irin matsanancin matsin tattalin arziƙi unda take fuskantar manya-manyan kalubalen ƙarancin samun kuɗaɗen shiga.

‘Yan sanda sun kama mijin da ake zargin ya kashe matarsa a Borno

Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta ce a ranar Juma’a jami’anta sun kama wasu mutane biyu, Adamu Ibrahim da Bukar Wadiya bisa zargin kashe wata mata mai suna Fatima Alhaji-Bukar ‘yar shekara 24.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, ASP Sani Kamilu ya bayyana wa manema labarai a Maiduguri ranar Juma’a.
Marigayiyar tana zaune a Dikechiri unguwar Bayan Gidan Dambe a cikin birnin Maiduguri na jihar Borno.
A cewarsa, marigayiyar wadda ke auren Ibrahim, wanda shi ne babban wanda ake zargi da aikata laifin.
Kakakin ‘yan sandan ya ce “A ranar 18 ga Oktoba, 2023, wani Adamu Alhaji Ibrahim mai unguwar Dikechiri bayan Gidan Dambe Maiduguri ya ziyarci ofishinsu da ke Gwange tare da rakiyar wani Bukar Wadiya, inda ya kai gawar wata mata wadda ya ce matarsa ​​ce, ya kuma nemi agajin gaggawa daga hukumar. ‘yan sanda,” in ji shi.

APC ta dakatar da shugabanta a Roni, jihar Jigawa kan zargin yi wa mace fyade

0
https://drive.google.com/uc?export=view&id=1MehvEY00kGj18ofq2HPaUCKLTCaa8Yyv
Jam’iyyar APC ta dakatar da shugabanta na karamar hukumar Roni ta jihar Jigawa Alhaji Sale Idris. Sanarwar da shugaban jam’iyyar ta APC a jihar Hon Aminu Sani Gumel ya fitar ta ce matakin zai ba da dama doka ta yi aikinta a zargin fyade da ake yi wa Alhaji Sale.
Ana dai zargin dan siyasar da yi wa ‘yar aikinsa mai shekaru 14 fyade tuni kuma a cewar jaridar Daily Trust har ta samu juna biyu ta sanadiyyar fyaden da shugaban jam’iyyar na karamar hukumar ya yi mata.

Kotun koli ta sanya ranar da za ta saurari karar Atiku kan nasarar zaben Tinubu

0
https://drive.google.com/uc?export=view&id=1RqjW2wV0MDt44j4zt_7hV0mfsiv1OkDxhttps://drive.google.com/uc?export=view&id=1JHcGmioJr0gkmNg08kPIXqey_RVqH1uZ
Kotun kolin Nijeriya ta ce a ranar 23/10/2023 za ta saurari bukatar da madugun adawa Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ya gabatar mata domin duba yadda za ta soke nasarar Shugaba Bola Tinubu. Hukumar zabe ta INEC dai ta ayyana Shugaba Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na 2023. Kotun sauraran kararrakin zabe ma ta tabbatar da wannan nasara ta Tinubu.

Tinubu ya soke nadin da ya yi wa matashi Imam Kashim a hukumar FERMA

0
https://drive.google.com/uc?export=view&id=1zyW1JjmHvrR6uzwlnOTRY4uhTdtM-lwD
Shugaba Tinubu ya soke nadin da ya yi wa matashi dan shekaru 24 Engr. Imam Kashim Imam domin ya jagoranci hukumar gudanarwa (Board of Directors) na hukumar FERMA da ke gyaran hanyoyin gwamnatin Tarayya. Sanarwar da mai magana da yawun shugaba Tinubu, Chief Ajuri Ngelale, ya fitar ba ta bayyana dalilin janye wannan mukami da aka sanar ba da jimawa ba, amma dai nadin matashin ya janyo suka daga bangarori dabam dabam saboda karancin shekarunsa.

Shugaba Tinubu ya sauke shugabannin NBC da FRCN da NTA da NOA da VON da NAN da ARCON

0

 

Ga sunayen sabbin mutanen da shugaban na Nijeriya ya nada domin su jagoranci wadannan hukumomi na gwamnatin tarayya da ke da nasaba da yada labarai

(1) National Orientation Agency (NOA) — Director-General / CEO — Mr. Lanre Issa-Onilu

(2) Nigerian Television Authority (NTA) — Director-General / CEO — Mr. Salihu Abdulhamid Dembos

(3) Federal Radio Corporation of Nigeria (FRCN) — Director-General / CEO — Dr. Muhammed Bulama

(4) National Broadcasting Commission (NBC) — Director-General / CEO — Mr. Charles Ebuebu

(5) Voice of Nigeria (VON) — Director-General / CEO — Mr. Jibrin Baba Ndace

(6) Advertising Regulatory Council of Nigeria (ARCON) — Director-General / CEO — Dr. Lekan Fadolapo

(7) News Agency of Nigeria (NAN) — Managing Director / CEO — Mr. Ali Muhammed Ali

(8) Nigerian Press Council (NPC) — Executive Secretary / CEO — Mr. Dili Ezughah

Tinubu na kitsa yadda zai yi shekaru 8 amma ba za mu yarda ba – Sheikh Gumi

0
https://drive.google.com/uc?export=view&id=1X1liesF6jCXXBiT_-zrbLy7zSEl2sBRZ
Malamin addinin Islama Sheikh Abubakar Gumi ya ce Shugaba Tinubu da mutanensa na kitsa yadda za su yi shekaru takwas a kan mulkin Nijeriya amma a cewar malamin shugaban ba zai samu biyan bukata ba.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito malamin a wani faifan bidiyo na fadin yadda gwamnatin Tinubu ta mayar da arewacin kasar saniyar ware. Ya ce an nada ministocin tsaro Musulmai amma a zahiri manyan sojoji da ke bayar da umurni a fagen daga ba Musulmai ba ne.
A cikin bidiyon kuma malamin ya nuna rashin jin dadinsa da kamun ludayin ministan Abuja Nyesom Wike, wanda malamin ya yi zargin na gab da mayar da Abuja matattarar Yahudawa tamkar birnin Tel Aviv.

Tinubu ya dakatar da kaddamar da sabbin jami’o’i 37 da Buhari ya amince da su – Minista

0

Gwamnatin Tarayya ta ce za a samu jinkiri kafin sabbin jami’o’i 37 da gwamnatin da ta shude ta amince da su su fara aiki.

Ministan Ilimi Tahir Mamman ya bayyana haka jim kadan bayan ya yi wata ganawa da shugaban kasa Bola Tinubu a ranar Laraba a Abuja.

Ministan ya ce hakan ya kasance ne bisa la’akari da bukatar za a  samar wa da jami’oin da ingantattun shirye-shirye domin bayar da ingantacen ilimi.

Tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ne dai ya amince da sabbin jami’oin guda 37 kwanaki kadan kafin ya mika mulki ga gwamnatin shugaba Tinubu.

Rahoto: Ahmad Rabe Yanduna/Umar Ibrahim

Shirin Dadin-Kowa ya sa samari son yin wuf da ni – Fati Harka

0

Fitacciyar jaruma a cikin shirin Dadin_Kowa mai dogon zango Amina Adam Jos da aka fi sani da Fati Harka ta ce rawar da take takawa a cikin shirin Dadin_Kowa ta soyayya da kananan yara ta sanya a zahiri samari masu kananan shekaru na tunkararta da zance cewa suna son yin soyayyar gaske da ita.
Fati Harka a cikin wata hira da BBChausa ta ce duk da cewa tana da samari hakan bai sanya ta wulakanta kananan yaran da ke zuwa wajenta su yi mata lafazin cewa suna son yi soyayya da ita a zahiri ba.
Rahoto: Ahmadu Rabe Yanduna/Umar Ibrahim