Tuesday, April 7, 2026
Home Blog Page 487

Sabbin nade-naden Tinubu ba su kawar da kyamar da yake nuna wa arewa ba – Mahadi Shehu

0

Ga videon wannan rahoto: 

 

Ruwan
mukamai ne dai Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wa mutanen da suka fito daga
arewacin Nijeriya a baya-bayan nan. Kama daga jagorancin hukumar alhazai ta
kasa zuwa hukumar PTDF wadda ke tura matasan Nijeriya karatu kasashen ketare ta
amfani da  rarar kudaden da gwamnati ta
samu a harkar man fetur zuwa hukumar NCC mai sanya ido kan harkoki na sadarwa
da kuma hukumar ICPC mai yaki da rashawa a Nijeriya, dukkaninsu Shugaba Tinubu
ya damka su a hannun mutanen arewa. Sai dai a cewar, Mahadi Shehu, wanda ya jima
yana zargin gwamnatin Tinubu da fifita kabilar Yarbawa a wajen nada mukamai,
wadannan nade-nade ba su gyara kyamar da Mahadin ke zargin Tinubu da nuna wa
mutanen arewa ba.

Sai dai
gwamnatin Tinubu ta ce babu adalci a cikin irin wannan fahimta ta Mahadi Shehu.
Abdulaziz Abdulazi da ke magana da yawun Shugaba Tinubu ya ce zafin shan kaye a
zabe ne ke sanya irinsu Mahadi Shehu sukar gwamnatin ta APC.

Duk da cewa
tun a zamanin mulkin mallaka ne dai manyan kabilun Nijeriya suka fara nuna wa
juna rashin amincewa a wajen rabon mukami, har yanzu matsalar taki ci, taki cinyewa,
a cewar Ibrahim Baba Shatambaya, malamin jami’ia da ke  sharhi a kan lamurran siyasa a Nijeriya.

A yayin da
masu adawa da salon nade-naden gwamnatin Tinubu ke ci gaba da matsa mata lamba,
masu sharhi na aza ayar tambaya a kan, shin mutanen arewa suke son  gani a shugabanci ko da  ba za su iya tabuka wani abu ba ko kuwa
mutanen da za su kawo ci gaba a Nijeriya, tun da a baya an ba ‘yan arewa
mukamai masu gwabi kuma ba a ga wani cci-gaba ba?

Masu sharhi
dai sun tsura ido su ga ko wadanda Shugaba Tinubun ya nada mukamai dabam-dabam
za su tabbatar da zargin ‘yan adawa na danne yankin arewacin Nijeriya a wajen
zuba ayyukan gwamnati ko kuma za su bai wa mara da kunya.

 

DCL Hausa

Aisha Usman
Gebi

FG ta kashe Biliyan 135 don rage wa ‘yan Nijeriya tsadar farashin lantarki

0
https://drive.google.com/uc?export=view&id=1h_sEo99fnwMEN2B9jexWWzTo0MFYDpjL
Naira biliyan 135.2 gwamnatin Tinubu ta kashe a cikin watanni uku domin hana wutar lantarki yin tsadar da za ta fi karfin talaka. Jaridar Daily Trust wacce ta ruwaito wannan labarin ta ce a zangon farko na wannan shekara, kafin zuwan Shugaba Tinubu , Naira biliyan 36 tsohuwar gwamnati ta biya domin daidaita farashin lantarkin.

Shugaba Tinubu zai yi kasafin Naira Tiriliyan 26 a 2024 domin tafiyar da gwamnatin Nijeriya

0


Gwamnatin shugaba Tinubu ta tsara yin kasafin kudin shekarar 2024 da zai iya lakume kimanin Naira Tiriliyan 26.

Kasafin kudin wanda ake sa ran mika wa majalisun kasar domin amincewa da shi kafin karshen wannan wata na Oktoba kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Sai dai wannan ne karo na farko da kasar ta yi kasafin kudi mafi girma da ya kai kimanin dala bilyan 33.8 wanda ya zarta wanda gwamnatin da ta shude ta yi.

Gudun bara ko afka wa assha ya sa nake sayar da ruwa a ‘kura’ – Macen da ke tura kurar-ruwa a Kano

Malama Gambo Haruna, mace ce mai matsakaitan shekaru a birnin Kano da ta shafe shekaru sama da biyu tana tura kurar-ruwa domin sayar da ruwa ta samu abin da za ta ciyar da ‘ya’yanta 6.
Mijin Gambo dai, ya rasu ne shekaru kusan 6 da suka gabata.
Matar na zaune ne a wani gidan da ta kama hayar daki daya, inda take biyan kudi Naira 12,000 duk shekara a Gadar Katako Rimin Kebe cikin karamar hukumar Ungoggo jihar Kano.
Binciken Daily Trust ya gano cewa matar na cikin matsanancin halin rayuwa, ganin yadda a shekarunta bai kamata ta yi wannan tsufan ba.
Malama Gambo ta ce tana yin dukkanin mai yiwuwa don ganin ta samu abin da za ta ciyar da ‘ya’yanta don tana gudun ta yi bara ko shiga wata harkar da bata dace ba.
Ta yi imanin cewa duk halin da take ciki, Allah Ya sani, kuma zai fitar da ita.
Sai dai duk da wannan hali da Malam Gambo take ciki, bai hana ‘ya’yanta zuwa makaranta ba.

Shugaba Tinubu na cikin jerin musulman duniya 500 da ke da karfin fada a ji

Shugaban Nijeriya Bola Ahmad Tinubu na daga cikin jerin sunayen mutane 500 musulmai da ke da karfin fada a ji a duniya.
Kazalika, akwai mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar da mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da karin wadansu ‘yan Nijeriya 12 da ke cikin jerin sunayen mutanen.
Wannan ne karon farko da aka ambato sunan shugaba Tinubu a jerin sunayen musulmai masu karfin fada a ji a duniya da cibiyar kula da harkokin addini ta kasar Jordan ke fitarwa duk shekara.
Sai dai, a wannan sabon bugun, an cire sunan tsohon shugaban kasa Muhammad Buhari da ya ke yawan fitowa a duk lokacin da aka fitar da sunayen.
Shekh Habib Umar Bn Muhammad Bn Salim Bn Hafiz ne Musulmin da ya fi kowa karfin fada a ji a duniya.

Farkon Kannywood, karuwai ma kyamarta suke yi – Kamaye

Sanannen marubucin nan, mai shirya fim tare da ba da umurni, Dan Azumi Baba da aka fi sani da Kamaye ya ce lokacin da aka bude masana’antar shirya fim ta Kannywood karuwai ma kyamarta suke yi.
Kamaye da aka zanta da shi a shirin Gabon Talk Show ya ce a zamanin babu macen da ke son a ga fuskarta a fim, saboda ana zaton harkar shashanci ce kawai a ciki.
Dan Azumi Baba ya ce “an yi lokacin da idan muka je gidan karuwai neman wadda za mu saka a fim, sai karuwa ‘yar’uwarta ta hana, ta ce za ki shiga fim kamar dai ‘yar iska”.
Ya ce a zamanin, Hindatu Bashir wata tsohuwar jaruma a masana’antar ce kadai ke aminta ta fito a fim.

Atiku ya rubuta wa Hedikwatar BBC korafi bisa zargin bayar da labarin son zuciya kan ingancin takardun Tinubu

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya rubuta wa Hedikwatar BBC takardar korafi bisa zargin wuce gona da iri kan ingancin takardun Shugaba Tinubu.
A cikin wani kundi, BBC ta yi bayani dalla-dalla kan ingancin karatun boko na Bola Ahmad Tinubu. Binciken BBC dai ya sanar cewa babu inda shugaba Tinubu ya yi karya a takardunsa.
Sai dai mai magana da yawun Atiku Abubakar, Phrank Shaaibu a hira da ya yi da gidan talabijin na Channels, ya ce binciken BBC cike yake da son zuciya.

An rufe kasuwar Mile 12 International Market Lagos

Gwamnatin jihar Lagos ta umurci da a gaggauta rufe kasuwannin Mile 12 International Market, da Owode Onirin.
A cikin wata sanarwa daga daraktan hulda da jama’a na ma’aikatar muhalli ta jihar Kunle Adesina ta ce an rufe wadannan kasuwanni ne biyo bayan rashin tsafta da sauran karya dokokin da suka shafi muhalli.
Ya ce an rufe wadannan kasuwanni ne biyo bayan wani aikin hadin guiwa da jami’an LAWMA da na KAI suka gudanar biyo bayan umurnin da suka samu daga kwamishinan ruwa da tsaftar muhalli na jihar Tokumbo Wahab.
Sanarwar ta ce gwamnatin jihar Lagos ba za ta sassauta kan duk wani nau’in tara kazanta ba a ko’ina.

Ban tarar da ko sisi a lalitar Sokoto ba – Gwamna Ahmad

Gwamna Ahmad Aliyu na jihar Sokoto ya ce babu ko sisin-kwabo a lokacin da ya karbi ragamar tafiyar da jihar a matsayin Gwamna daga hannun Aminu Waziri Tambuwal.
Kazalika, Gwamnan ya ce babu wata takardar hannanta mulki da tsohuwar gwamnati ta bashi a lokacin da aka rantsar da shi.
Gwamna Ahmad na ba da amsa ne ga mataimakin shugaban majalisar wakilai Benjamin Kanu da ya tambaye shi yadda aka yi ya iya gabatar da ayyuka kusan 100 a cikin kwanakinsa 100 da rike ragamar tafiyar da jihar Sokoto.
Benjamin Kanu dai ya ziyarci Sokoto ne a ranar Alhamis a lokacin da ya je ziyarar ta’aziyya.
Gwamnan da ya yi magana ta hannun mataimakinsa Engr Idris Gobir ya ce kawai suna sadaukar da rayuwarsu ne don al’ummar jihar Sokoto su samu saukin rayuwa, amma dai ba su tarar da sisin-kwabo a cikin lalitar gwamnatin jihar kusan watanni biyar kenan.