Monday, April 6, 2026
Home Blog Page 488

Za a haifi jarirai 365,595 a Jigawa cikin shekarar 2023

Gwamnatin jihar Jigawa ta ce ana kyautata zaton samun haihuwar jarirai 365,595 a jihar cikin shekarar nan ta 2023.
Kwamishinan lafiya na jihar Abdullahi Kainuwa ya sanar da hakan a Dutse babban birnin jihar kamar yadda jaridar Premium Times ta rawaito.
A wajen taron, Abdullahi Kainuwa ya ce matan da suka kai shekarun haihuwa a jihar suna samun maganin hana haihuwa na zamani a akalla a cibiyoyin kiwon lafiya 300 daga cikin cibiyoyi 761 da ke jihar.
Kwamishinan ya ce daga cikin jariran 365,595, tuni har an haifi 273,000 ya zuwa watan Juli da ya gabata.
Ya ce jihar na da matan da ke iya daukar ciki su haihu kimanin 1,608,616. Sai dai ma’aikatar kula da lafiya ta jihar na kokarin nan da shekarar 2027, matan na amfani da maganin takaita haihuwa.

Kamfanin BUA ya yi karin farashin kayan abinci a sirrance

Kwanaki kadan bayan sanar da rage farashin buhun siminti, kamfanin BUA ya yi ta karin farashin kudin kayan abinci irinsu buhun sukari da na garin fulawa da kuma katan din taliya spaghetti, kamar yadda wani bincike ya nuna.
Hukumar gudanarwa ta kamfanin na BUA a ranar 1 ga watan Oktoba ta sanar da rage farashin buhun siminti zuwa Naira 3,500 kan kowace buhu.
 Sai dai har ya zuwa wannan lokaci yan Nijeriya na guna-gunin cewa sabon farashin siminti bai fara aiki ba a kasar domin ko kobo ba a rage ba har yanzu.

Tsohon shugaban kasa Buhari na nadamar irin shugabancin da ya yi – Solomon Dalung

Tsohon ministan matasa da wasanni a zamanin gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammad Buhari, Barr Solomon Dalung ya yi ikirarin cewa yanzu haka halin da ake ciki, tsohon shugaban kasa Buhari na nadamar irin shugabancin da ya yi a zamanin da ke shugaban kasa.
Solomon Dalung ya ce dalilin da na sanin da Buhari ke yo, shi ne na yadda wasu makusantansa suka ingiza shi ya aikata abin da ya aikata da yanzu ba ya jin dadin abin.
Barr Dalung da ya yi minista a wa’adin farko na gwamnatin Buhari daga 2015-2019, ya ce shugaba Buhari ya gaza cika alkawurran da ya dauka a lokacin yakin neman zabe na 2015.
A lokacin da ya ke tattaunawa da gidan rediyon Trust Radio, ya ce dole ya fadi gaskiya a matsayinsa na daya daga cikin wadanda suka yanke wa APC cibi.
Sai dai Solomon Dalung ya ce tsohon shugaban kasa Muhammad Buhari mutum ne mai gaskiya da rikon amana, da ya aminta da mutanen da ke kewaye da shi dari bisa dari. Sai dai yanzu haka Buhari na nadamar amincewa wadannan mutane da ya yi.

Wani mai tabin hankali ya kashe mutane 8 a Adamawa

……sai dai shi ma wasu fusatattu sun kashe shi
Wani mutum da ya samu matsalar tabin hankali ya bi mutane da sara da wuka har ya kashe 8 ya jikkata da dama a yankin Kate-Gamji na karamar hukumar Shellengbta jihar Adamawa.
Mutumin mai suna Ali Denham ya zari wukarsa ya bi mutane yana yanka har ya kashe mutane 8 ya jikkata karin uku a daren Larabar makon nan, kafin daga bisani aka samu wasu fusatattu, suka kashe shi.
Da ya ke tabbatar da lamarin, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Sulaiman Nguroje ya ja kunnen mutane da su daina ajiye masu tabin hankali a gida ba tare da sun kai su asibiti ba.
Ya ce mutumin da ke da tabin hankali ya kashe mutane 8 kafin a samu wasu fusatattu shi ma su kashe shi.

NAHCON ta ba jihar Katsina kujerun aikin hajji 4,513 a hajjin badi, 2024

Hukumar kula da aikin hajji ta jihar Katsina ta sanar cewa jihar ta samu yawan kujerun aikin hajjin shekarar 2024 kimamin 4,513 daga hukumar kula da aikin hajji ta kasa NAHCON.
Kazalika hukumar ta sanar cewa an fara biyan kudin ajiya na Naira milyan 4 da dubu 500 ga duk maniyyacin da ke da burin sauke farali a badi, 2024.
Shugaban hukumar ta kula da aikin hajji ta jihar Katsina Alhaji Sulaiman Nuhu Kuki, ya sanar cewa gwamnatin jihar ta amince da a fara rajistar maniyyata aikin hajjin badi, 2024 tare da karbar kudaden ajiya na wadannan maniyyata.
Ya yi karin hasken cewa maimakon saka kudin ajiyar na jimillar Naira 4.5, gwamnatin jihar Katsina ta saukaka, inda ta ce ko da Naira milyan uku ana iya fara ajiyewa, daga bisani a rika sanyawa kadan-kadan har su cika 4.5 din duba da yanayin tattalin arzikin da ake ciki.
Shugaban hukumar ya ce maniyyata aikin hajjin na badi na da daga nan har zuwa watan Disambar shekarar nan na su zuba kudaden ajiyar ta su na aikin hajjin.
Alhaji Sulaiman Nuhu Kuki ya ce Nijeriya gabadaya, an samu jimillar kujerun aikin hajji 95,000 daga kasar Saudi Arabia kamar yadda aka yi a shekarar nan ta 2023.
Shugaban hukumar kula da aikin hajjin ta jihar Katsina ya ce yanzu haka kuma ana nan ana ci gaba da biyan kudaden wadanda suka fara ajiye kudi a hukumar a aikin hajjin da ya gabata, amma ba su samu damar cika kudin ba, har lokacin aikin hajjin ya wuce. 
Sai ya yi kira ga maniyyata aikin hajjin da su rika muamala Kai tsaye da jami’an hukumar kula da aikin hajji don gudun fadawa hannun ‘yan damfara.

Gwamnatin Dikko za ta dauki nauyin dalibai ‘yan asalin jihar Katsina zuwa karatu kasashen waje

SHIRI NA MUSAMMAN DON BAYAR DA GURABEN KARATU ZUWA JAMI’O’IN KASASHEN WAJE GA DALIBAI ‘YAN ASALIN JIHAR KATSINA

Mai girma gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umar Radda, PhD, ya amince da a fara tattara takardun neman guraben Karatu (wato scholarship) daga dalibai ‘yan asalin jihar Katsina zuwa Jami’o’in Kasashen waje wanda Gwamnatin Jiha za ta dauki nauyinsu.
Kwasa-kwasan da za a karanta sune: –
Karatun ilimin likita (wato MBBS)
Karatun ilimin kirkire-kirkiren Na’ura mai kwakwalwa dake da kaifin basira (wato Artificial Intelligence)
Karatun ilimin tattalin arziki dake da alaka da hallittu da tsirrai. (wato Bio-Economy).
Daliban da suke da sha’awar shiga shirin su kasance suna da takardu kamar haka:-
Takardar Sakamakon gama makarantar sakandare WAEC/NECO a zama guda, da yabo (wato credit) akalla takwas (8) a darussa kamar haka:-
Darasin ilimin kwakwaf (Physics)
Darasin ilimin hada magunguna (Chemistry)
Darasin ilimin sanin hallittu da tsirrai (Biology), kona Ilimin Aikin Gona (Agric Science)
Darasin Turanci
Darasin Lissafi
Darasin ilimin Na’ura Mai Kwakwalwa [a inda keda bukatar haka]
Bugu da kari, daliban da ke neman karatun likitanci (wato MBBS), wajibi ne su kasance suna da sakamako mai daraja ta “A” ko “B” akalla a darussa ukku masu alaka.
Sauran Kwasakwasan biyu kuma (wato, Artificial intelligence da Bio Economy) wajibi ne dalibi ya kasance yana da sakamako mai matakin daraja “A” ko “B” akalla guda biyu (2).
Sannan wajibi ne dalibi ya kasance bai gaza shekaru goma sha shidda (16) ba, kuma bai wuce shekaru ashirin da biyu (22) ba na haihuwa a lokacin neman wannan gurbin Karatu.    
Daliban da suka gama makarantun gwamnati kadai ne za su shiga wannan shiri.
Sannan Kowace Karamar Hukuma za ta samu wakilci a cikin daliban da za a tantance a kuma dauka.
Za a aiko da takardun neman gurbin karatun tare da: –  
Takardun shaidar gama makarantar primary da na sakandare WAEC/NECO.
Takardar haihuwa.
Takardar shaidar zama dan Karamar hukuma
Takardar shaidar nuna hali na gari mai dauke da sa hannun shugaban Karamar hukuma.
Za a aiko da takardun neman guraben karatun ga adireshi kamar haka: –
The Chairman 
Coordination committee
Special Foreign Scholarship Programme     
Katsina State.
Ana iya aikawa da takardun a ofishin shiyyar ilimi na tsofaffin kananan hukumomi 7 na : –
Katsina, Daura, Funtua, Malumfashi, Kankia, Dutsinma da Mani. Ko kuma a aiko da takardun neman gurbin karatun a sakateriyar kwamitin da ke a ofishin shugaban Ma’aikata na Jaha wanda ke Babbar Sakateriya Jahar Katsina.
Za a lika sunayen wadan da aka tantance don su zauna jarabawa, tare da wuri, da lokacin yin jarabawar, a kananan hukumomin daliban, ranar Lahadi 15 ga watan October, 2023.
Za a fara amsar takardun neman gurbin karatun daga ranar Laraba 4 ga watan October, 2023, za a kuma rufe amsar a ranar Laraba 11 ga watan October, 2023. In sha Allah.
Sanarwa daga Sakataren Kwamitin Gudanarwa, Mas’ud B. Mustapha, (Permanent Secretary, Establishment, Pension & Training).

‘Yan bindiga sun sace dalibai mata na Jami’ar FUDMA, Katsina

Wasu mutane dauke da makamai sun mamaye gidajen kwanan daliban jami’ar Gwamnatin tarayya da ke Dutsinma, FUDMA jihar Katsina suka sace dalibai mata guda biyar kamar yadda DCL Hausa ta samu labari.
Lamarin da ya faru da misalin karfe biyu na daren Talata wayewar Laraba, ya faru ne a gidajen kwanan daliban da ke bayan makarantar Mariamoh Ajiri, a inda daliban suka kama hayar gidajen da suke kwana.
Ya zuwa yanzu dai babu takamaiman bayanin asalin jihohin da suka fito da kwasa-kwasan da suke karantawa da azuzuwan da daliban suke. Kazalika, babu cikakken bayanin halin da daliban mata suke ciki a halin yanzu, don babu tabbacin ko ‘yan bindigar sun kira waya suna neman kudin fansa ko a’a.
Ko a kwanakin baya, wasu dalibai ‘yan jami’ar ta FUDMA sun taba fadawa irin wannan hali, inda wasu ‘yan bindiga suka yi awon-gaba da dalibai biyu a gidajen kwanan da suka kama haya bayan ginin gidan rediyo na Dutsinma.
Ko a makonni biyu da suka gabata, wasu ‘yan bindiga sun shiga jami’ar gwamnatin tarayya da ke Gusau jihar Zamfara, inda suka sace dalibai mata masu tarin yawa. Sai dai bayanai sun ce an kubuto wasu daga cikinsu.
Sashen hulda da jama’a na jami’ar ta FUDMA bai kai ga fitar da sanarwa kan lamarin ba a hukumance. Amma dai DCL Hausa ta kira sashen, wani daga cikin ma’aikatan ya ce zai kira idan sun kammala tattara bayanai. 
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta hannun mai magana da yawun ta ASP Sadiq Aliyu Abubakar ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce an kama mutum daya da ake zargi yana ba ‘yan ta’addar bayanan sirri, sannan an kama wasu mutane da dama da ake zargi da hannu a satar wadannan dalibai mata na Jami’ar FUDMA, Katsina. 
Rundunar ‘yan sandan ta ce tana ci gaba da gudanar da bincike tare da tsaurara tsaro don ceto daliban da sauran mutane da ‘yan ta’adda ke tsare da su.

Majalisa ta ja kunnen Tinubu kan kisan kudi ba bisa ka’ida ba

Majalisar dokokin Nijeriya ta ja kunnen shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu kan kashe kudi ba bisa ka’ida ba, har ma ta shawarce shi da ya mika mata kasafin kudin cike gibi na ‘supplementary’ musamman kan batun iskar gas.
Majalisar ta hannun shugaban kwamitin majalisa dattawa kan iskar gas Sanata Jarigbe Jarigbe ta bukaci sashen zartarwar da ya mika mata kasafin kudin cike gibi na 2023 don fara aikin inganta bangaren iskar gas.
Wannan bukata dai ta zo ne kasa da sa’o’i 48 bayan da shugaban kasa Bola Tinubu ya sanar da daukar matakan saukaka rayuwa bayan cire tallafin man fetur ga ‘yan Nijeriya.
‘Yan majalisar sun tsaya kai da fata cewa ya kamata a rika kashe kudi a hurumin doka.

Gwamnatin Tinubu za ta mayar da yara milyan 10 makarantun boko

Gwamnatin tarayya ta sanar cewa tana nan tana shirin mayar da yara milyan 10 makarantun boko a fadin kasar nan da wasu ‘yan shekaru masu zuwa.
Karamin ministan ilmi Dr Yusuf Tanko Sununu ya sanar da hakan a lokacin da ya karbi bakuncin ‘yan majalisar dokoki na jam’iyyar APC a Abuja.
Babban jami’in kungiyar ‘yan majalisar dokokin wanda shi ne mataimakin shugaban majalisar wakilai Babangida Nguroje bayan taya murna ga ministan, ya bukaci da su saka idanu sosai kan ilmin yara kanana musamman masu karamin karfi.
Sai dai da ya ke mayar da jawabi, Dr Yusuf Sununu ya ce gwamnati na shirin mayar da yara milyan 10 makarantun boko.
Ya ce gwamnati na da burin dasa harsashi mai dorewa a kan ilmi ta hanyar bullo da matakan da za su sa yaran su ji su na son zuwa makarantar ta hanyar samar musu yanayi mai kyau.

Gawuna zai sake farfado da kasuwancin da aka rusa a Kano idan aka rantsar da shi – Ganduje

Shugaban jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje ya tabbatar wa da ‘yan kasuwar Kano cewa za su dara idan jam’iyyar APC ta dawo mulki a jihar.
Gwamnan jihar Kano na yanzu Engr Abba Kabir Yusuf tun bayan da ya karbi ragamar tafiyar da gwamnatin jihar, ya fara rusa wasu wurare da ya ce an gina su bisa son zuciya.
Duk da Gwamnan ya sha fadin cewa yana wadannan rushe -rushe ne don tsaftace gari da inganta kasuwanci a jihar, amma wasu na ganin cewa yana yin hakan ne don dakushe tarihin ayyukan raya kasa da tsohon Gwamna Ganduje ya yi a jihar.
A ranar 20 ga watan Satumba ne dai kotun sauraren kararrakin zabe ta jihar ta yanke hukuncin cewa jam’iyyar APC ce ta yi nasara a zaben Gwamnan jihar Kano ba NNPP. Sai dai dukkanin jam’iyyun biyu sun garzaya kotun daukaka kara.
Da ya ke karbar matasan ‘yan kasuwa na jihar Kano a sakatariyar jam’iyyar APC ta kasa da ke Abuja, Abdullahi Ganduje ya ba su tabbacin cewa jam’iyyar APC idan ta dawo kan mulki za ta maido musu da martaba da kimar kasuwancinsu.
Tsohon Gwamna Ganduje ya ce yanzu mutane da dama na dari-darin zuwa Kano don gudanar da kasuwanci.