Monday, April 6, 2026
Home Blog Page 489

Ana iya haihuwar jariri da hakoransa – Likitoci

Wata kwararriyar likitar hakoran yara Dr Osarugue Ota, ta ce haihuwar jarirai da hakoransu ko su yi hakora cikin kwanaki 30 da haihuwarsu ba wata matsala bace, kuma hakan bai da nasaba da tsafi.
Dr Ota da ke aiki a asibitin koyarwa na jami’ar Benin ta sanar da hakan a lokacin ba da wani horo ta yanar gizo, inda ya ce madamar aka samu hakan, to ba wata matsala da yaro yake da ita.
Likitar ta ce akwai hakoran da ke fitowa yaro bayan an haife shi, akwai kuma nau’in hakoran da ke fitowa jariri da zarar an haife shi.

An ba da belin Diezani kan kudi Dala 70,000 a Burtaniya

A ranar Litinin din makon nan ne tsohuwar ministar man fetur ta Nijeriya Mrs Diezani Alieson Madueke ta bayyana a gaban kotun Majistare ta Westminster da ke Ingila.
Diezani Madueke dai ta bayyana a gaban kotun ne bisa zargin cin hanci na kudi Dala 100,000.
Sai dai Alkalin kotun Michael Snow ya bayar da belin Mrs Diezani kan kudi Dala 70,000.
Kazalika, Alkalin ya yanke cewa an takaita zirga-zirgar tsohuwar ministar daga karfe 11 na dare zuwa 6 na safe. Sannan ya zama wajibi ta rika rataya wata alama ta na’urar zamani da za ta rika nuna inda take.

Lauyoyin Bazoum na nemar masa hakki a Majalisar Dinkin duniya

Lauyoyin Hambararren shugaban kasar Nijar Bazoum Mohammed da iyalansa karkashin jagorancin Me Seydou Diagne dan asali kasar SĂ©nĂ©gal sun gabatar da korafin su a gaban kwamitin kare hakkin dan Adam na majalisar dinkin duniya kan yadda suka ce ana cigaba da rike Bazoum din ne ba akan ka’ida ba kuma hakan ya taka dokar ‘yanci dan adam.
Kazalika, lauyoyin sun ce sun shigar da karar sojojin na Nijar a gaban babbar kotun birnin Yamai inda suka bukaci a saki hambararren shugaban da matar sa Hadiza da dan sa Salem wadanda sojojin da suka yi masa juyin mulki suke cigaba da rike wa a fadar shugaban kasar tun ranar 26 ga watan Yuli da ya gabata.
Dama, a tsakiyar watan Satumba nan da ya gabata lauyoyin tsohon shugaban sun shigar da karar hukumomin mulkin sojan Nijar din a gaban kotun ECOWAS inda suke neman kotun da ta mayarwa hambararren shugaban kujerar mulkin sa.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ga kamar ana dada kara nisa da matakin amfani da karfin soja da kungiyar ECOWAS ta yi ikirarin dauka a baya kan Sojojin na Nijar domin maido da hambararren shugaban kan kujerar sa.

Hukumomin Nijar sun amincewa Aljeriya ta shiga tsakani kan rikicin siyasar kasar

Gwamnatin kasar Aljeriyar ce ta sanar da wannan mataki na hukumomin mulkin sojan na Nijar na amincewa kasar domin shiga tsakani a cikin rikicin siyasar kasar ta Nijar da ke cikin yanayin juyin mulki
A karshen watan Ogustan da ya gabata ne dai kasar ta Aljeriya ta gabatar da bukatarta ta shiga tsakani a rikicin kasar ta hanyar sulhu tare da nuna adawar ta da dukkan wani matakin soja akan Nijar din da ECOWAS ta yi barazanar dauka domin maido hambararren shugaban
Aljeriyar ta bada shawarar wa’adin watanni shidda (6) a baya na rikon kwaryar kafin shirya zaben da zai maido farar hula
A yanzu dai tuni shugaban kasar ta Aljeriya Abdelmadjid Tebboune ya bawa ministan harakokin wajen sa Ahmed Attaf umarnin kai ziyara birnin Yamai nan ba da jimawa domin fara ganawar sharar fage da bangarori da ke da ruwa da tsaki a sha’anin rikicin kasar
Ko daga ranar 23 zuwa 26 ga watan Ogustan shugaban difilomasiyyar na Aljeriya ya kai ziyara kasashen Nigeria, Bénin da kuma Ghana membobin kungiyar ECOWAS domin tattaunawa kan rikicin na Nijar

Tsohon Gwamnan Kaduna Ramalan Yero ya bar PDP

Tsohon Gwamnan jihar Kaduna Mukhtar Ramalan Yero ya sanar da ficewa daga jam’iyyar PDP.
Ramalan Yero dai ne Gwamnan jihar Kaduna daga shekarar 2012 zuwa 2015 bayan da maigidansa a wancan lokacin Gwamna Patrick Yakowa ya mutu, ya gaji kujerarsa.
A cikin sanarwar da shi tsohon Gwamnan ya sanya wa hannu, bai ayyana jam’iyyar da ya koma ba.

Tsadar rayuwa: Sarkin Musulmi ya roki kungiyar kwadago ta NLC da kada ta tafi yajin aiki

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya roki kungiyar kwadago ta NLC da TUC da kada su tafi yajin aikin da suka kudurci aniya a makon gobe.
Kungiyar kwadagon dai ta ware ranar Talata 3 ga watan Oktoba a matsayin ranar da za ta tsunduma yajin aiki na sai baba-ta-gani biyo bayan cire tallafin man fetur da gwamnatin Tinubu ta yi.
Alhaji Sa’ad Abubakar ya ce akwai bukatar a kara ba gwamnatin tarayya dama, kada a yi gaggawar tsunduma yajin aiki.
Ya ce ya shiga cikin sulhu da tattaunawa daban-daban da kungiyar kwadago a lokutta daban-daban, inda ya gano cewa yajin aikin zai kara jefa kasa cikin mawuyacin hali

Yawan hadiman Gwamna Abba a Kano sun haura 400

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya sake fitar da sabbin nade-nade na masu taimaka masa na musamman su 116 a fannoni daban-daban.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar.
Dama dai, a ranar Talatar da ta gabata, Gwamnan ya nada mutane 94 mukamai daban-daban a matsayin masu taimaka masa na musamman.
Jaridar Daily Trust ta gano cewa, da wannan nadin baya-bayan nan, yanzu haka Gwamna Abba na da mataimaka na musamman da hadimai kusan 406.
Da yake kare wadannan nade-nade, Gwamna Abba ya ce yin hakan na da nufin saka matasa sosai a cikin tafiyar da gwamnati da za su taimaka masa ya sauke nauyin da ya dauka na al’ummar Kano.
Daga cikin mukaman na baya-bayan nan, akwai manyan masu taimaka wa Gwamna na musamman SSAs guda 63, sai mataimaka na musamman SAs guda 41.
Bugu da kari, akwai hadimai wato PAs guda 12.

Ganduje bai iya kai Tinubu ga nasara a 2027 – NNPP ta Kwankwaso

Jagoran jam’iyyar adawa ta NNPP a Nijeriya Rabi’u Musa Kwankwaso ya caccaki shugaban jam’iyyar APC Abdullahi Umar Ganduje, inda ya ce Gandujen ba zai iya kai Tinubu ga nasara ba a zaben 2027 mai kamawa.
Kwankwaso da ya yi wa jam’iyyar NNPP takarar ahugaban kasa a zaben watan Fabrairu, 2023 ya ce Ganduje matsala ne a jam’iyyar APC.
A cikin wata sanarwa daga Sakataren yada labaran jam’iyyar NNPP na kasa Hon Yakubu Shendam na mayar da martani ne kan wasu kalamai da aka alakanta su da shugaban jam’iyyar APC Ganduje da aka ce ya ce, Rabi’u Kwankwaso ya saba faduwa zabe.
Jam’iyyar NNPP ta ce duk da zarge-zargen da suka dabaibaye Ganduje, bai kamata ya rika tsoma baki ga harkar mutanen kwarai irinsu Kwankwaso ba. Sanarwar ta kara da cewa wadannan bahallatsar da ake zargin Ganduje da aikatawa a lokacin yana Gwamna ne za su hana shi yin wani katabus a zaben 2027 mai zuwa. Ta kara da cewa muddin Ganduje zai ci gaba da shugabantar APC, tabbaci hakika, jam’iyyar ta mutu.

An yi yunkurin juyi mulki a kasar Burkina Faso

Sojojin da ke mulki a kasar Burkina Faso sun sanar cewa an yi yunkurin hambarar da gwamnatisu.
A cikin wata sanarwa daga sojojin, dakarun kasar sun ce  akwai wasu tsirarun sojojin da suka yi yunkurin juyin mulki, amma dai hakarsu ba ta cimma ruwa ba.
Sojojin da ke jagorantar kasar ta Burkina Faso sun ce masu son sake wani juyin mulkin na son jefa kasar ne cikin hayaniya da rikici na babu gaira babu dalili.
A cikin sanarwar, sojojin sun ce sun yi nasarar kama wadanda suka yi yunkurin juyin mulkin kamar yadda mai magana da yawun tawagar sojin da ke jagorantar kasar ta Burkina Faso Rimtalba Jean Emmanuel ya karanta sanarwar.
Gwamnatin sojin ta ce za ta fadada bincike don gano musabbabin wannan yunkuri na tsirarun sojojin, inda ta kara da cewa abin takaici ne a ce sojin da ya yi rantsuwar zai kare kasarsa, amma ya buge da wannan abu da suka kira aika-aika.
Ta ce ana tsare da sojoji hudu cikin wadanda suka yi yunkurin juyin mulkin, sannan ana neman karin biyu.
Sojoji dai karkashin jagorancin Capt Ibrahim Traore sun karbe mulkin kasar Burkina Faso a shekarar bara Satumba, 2022, bayan da suka ce matsalar tsaro ta yi kamari.

Jami’ar UMYUK ta kori ‘lakcarori’ da wani ma’aikacinta daga aiki

Hukumar gudanarwar jami’ar Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina ta sanar da korar wasu malaman jami’ar su biyar bisa samunsu da aikata wasu laifuka da suka ci karo da dokar da ta kafa jami’ar.
A cikin wata sanarwa daga Magatakardan Jami’ar Muhammad Yusuf Abubakar da DCL Hausa ta samu kwafi, ta ce wannan matakin ya biyo bayan karbar rahoton kwamitin ladabtarwa da aka kafa bayan samun wadannan malamai da laifukan da aka zarge su da shi.
Daga cikin wadanda aka kora din, akwai Mr Ayaka Simon Silas na sashen kimiyyar siyasa (PSN 001003) da Abubakar Rabi’u na sashen tsare-tsare (PSN000565).
Sauran su ne Umar Shehu na sashen koyar da tattalin arziki na ‘Economic’ (PSN 001768) da Nura Hamisu Muhammad shi ma daga sashen koyar da tattalin arziki na ‘Economic’ (PSN 001664) da kuma Umar Abubakar Aliyu duk dai daga sashen koyar da tattalin arziki na ‘Economic’ na jami’ar (PSN 000769).