Maulud: Gwamnan Katsina Dikko na son mutane su yi koyi da kyawawan halayen fiyayyen halitta SAW
Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda ya bukaci ‘yan Nijeriya daga kowane addini da su kaunaci juna a harkokinsu na yau da kullum.
A cikin wata sanarwa daga mai magana da yawun Gwamna, Ibrahim Kaula Mohammed da ya aike wa DCL Hausa ta ce yin hakan, zai sa a samu zaman lafiya hadin kai da kaunar juna a tsakanin ‘yan Nijeriya don samun al’umma daya mai neman makoma daya.
Malam Dikko Umaru Radda a sakon da ya aike da shi don bikin zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta manzon tsira sallallahu ta’ala alaihi wa sallim, na bana, ya bukaci mutane da su rubanya kwazonsu wajen aikata daidai da koyi da halaye na gari na fiyayyen halitta “SAW”.
“Manzonmu, manzon tsira sallallahu ta’ala alaihi wa sallim ya yi daban da sauran manzanni, wanda ya gudanar da rayuwarsa cikin kana’a da tausayin al’ummar duniya da tsantsar gaskiya da rikon amana da sauran halayen na ƙwarai”. Inji Dikko.
Mahaifiya ta kai danta kotu don yana barazanar kashe ta a Kano
Wata kotun shari’ar musulunci da ke zamanta a Kofar Kudu jihar Kano ta tsare wani mutum da aka sakaya sunansa bisa zargin barazanar kisan mahaifiyarsa.
Mahaifiyar yaron dai ce ta maka dan nata kotu bayan da wata zazzafar muhawara ta barke a tsakaninsu.
Mahaifiyar dai ta roki kotu da ta umurci dan nata da ya tashi ya bar mata gida don tsaron rayuwarta.
Sai dai bayan da alkali ya karanta masa laifukan da ake tuhumarsa, dan matar duk ya musanta su.
Ya shaida wa kotu cewa, kawai dai saboda ya rabu da matarsa, kuma yanzu baya da kudi ne ya sa mahaifiyarsa take masa wannan zillar.
Alkalin kotun Khadi Isah Rabi’u Gademi Gaya ya umurci da a ci gaba da tsare yaron har sai ranar 25 ga watan Oktoba inda za a ci gaba da sauraren karar.
Farashin buhun siminti zai iya kaiwa N9,000 a Nijeriya
Kungiyar masu harhada siminti ta Nijeriya ta ja kunnen cewa muddin gwamnatin tarayya ba ta tsahirta shirinta na amfani da tsarin zuba kankare a kan titunan da ake ginawa ba, to farashin siminti zai iya kai wa Naira 9,000 a kasar.
A halin da ake ciki dai, ana sayar da jikkar simintin mai nauyin kilogram 59 kan kudi N5,000 ko fiye a wasu wuraren.
Kazalika, kungiyar ta ja hankalin cewa akwai bukatar gwamnati ta sa baki wajen yawan tashin farashin da simintin ke yi a ‘yan kwanakin nan ta hanyar kai dauki a masana’antar sarrafa simintin.
Kungiyar a cikin wata sanarwa daga Shugabanta Prince David Iweta da Sakatare Reagan Ifomba, ta yaba wa ma’aikatar aikace-aikace ta tarayya da take kokarin yin amfani da simintin a wajen gine-ginen hanyoyi, sai dai ta ja kunnen cewa yawan amfani da simintin zai sa a rika nemansa a kai a kai da kuma hakan zai sa ya yi tsada a kasuwa.
Burin Dikko Radda shi ne kowa ya tsaya da kafafunsa – Abdullahi Garba Faskari
Sakataren Gwamnatin jihar Katsina Barr Abdullahi Garba Faskari ya ce burin Gwamnan jihar Malam Dikko Umaru Radda shi ne kowa ya dogara da kansa.
Ya ce yin hakan zai taimaka mutane su samu ingantattar rayuwar da ta dace.
Barr Abdullahi Garba Faskari na magana ne a Funtua a wajen kaddamar da shirin wayar da kan al’umma game da alfanun da ke tattare da tashar kula da shige da ficen kaya ta kan tudu wato Funtua Inland Dry Port a garin Funtua jihar Katsina.
Sakataren Gwamnatin jihar ya ce gwamnatin jihar ta samar da fili murabba’in kadada 77 domin gina wannan tasha a matsuguni na dindindin domin samun ingancin shige da ficen kaya yadda ya kamata.
Ya misalta cewa fadin fili murabba’in kadada 77, shi ne kwatankwacin filin kwallo 77 ta yadda wurin zai wadatar da duk abin aka shigo ko za a fita da shi daga Nijeriya.
Barr Abdullahi Faskari ya ce hakan zai samar wa da dumbin mutane ayyukan yi da hakan zai sa tattalin arzikin jihar Katsina da na Arewa da ma na Nijeriya bakidaya ya bunkasa.
Ya ce dama tuni burin Malam Dikko Umaru Radda shi ne ya ga mutane sun samu hanyoyin da za su dogara da kansu ta yadda gwamnati za ta yi duk abin da ya kamata domin ta tallafa musu.
Fallen atamfa ya yi sanadiyyar rasuwar wani mutum a Kano
Wani mutum mai shekaru 37 mai suna Usman Ayuba ya riga mu gidan gaskiya a lokacin da ya shiga wata rijiya don dauko atamfar wata mata da ta fada a ciki.
Lamarin ya faru ne a yankin Kawon Maigari na karamar hukumar Nassarawa a jihar Kano.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Saminu Abdullahi ya tabbatar wa da kamfanin dillancin labaran Nijeriya NAN, inda ya ce lamarin ya faru ne da yammacin Talata.
Jami’in ya ce sun samu labarin cewa wata mata ce ta bukaci Usman da ya shiga rijiyar domin dauko mata fallen atamfarta da ya fada a ciki.
Bayanai sun ce mutin ya rasu ne ta dalilin karancin iskar shaka a cikin rijiyar.
Jigon APC ya lakada wa kwamishina dukan tsiya
Shugaban jam’iyyar APC na wata mazaba a jihar Ondo Mr Olumide Awolumate ya yi bayani tiryan-tiryan dalilin da ya sa ya lakada wa kwamishinar mata da walwalar jama’a ta jihar dukan tsiya.
Ya ce sa’in-sa ce ta kaure tsakaninsu, da ta kai su ga dambacewa da Mrs Juliana Osadahun.
Bayanan da jaridar Punch ta tattara sun ce cacar bakin da ta kai ga kai dukan ta faru ne a wajen rabon kayan tallafin rage radadin tsadar rayuwa a karamar hukumar Arigidi Akoko ta jihar ta Ondo.
Bayanai sun ce jigon na APC Awolumate har ya raunata kwamishina Osadahun a kai. Sai dai rahotanni sun ce tuni uwar jam’iyya ta jiha ta dakatar da wannan shugaban jam’iyya na mazaba.
Nijeriya na bukatar karin azuzuwa 907,769 a makarantun bokon kasar – UBEC
Shugaban hukumar kula da ilmin firamare ta Nijeriya UBEC Dr Bobboyi Oyeyemi ya ce kasar na bukatar karin makarantun boko 20,000 da azuzuwa 907,769.
Dr Bobboyi ya ce sai an yi hakan sannan a yi nasarar magance matsalar yaran da ba su zuwa makarantun boko.
Shugaban hukumar na magana ne a lokacin da hukumomin da ke karkashin ma’aikatar ilmi ta kasa suke ganawa da ministan ilmi Prof Tahir Mamman a Abuja.
Dr Bobboyi ya sanar da ministan cewa akwai karancin gine-gine da ma’aikata da ake bukatar a cike gibin muddin ana so a yi nasarar samar da ilmi mai inganci ga yara.
