Monday, April 6, 2026
Home Blog Page 491

Babban layin lantarkin Nijeriya ya kara faduwa

Babban layin lantarkin Nijeriya wato ‘National Grid’ ya sake faduwa, dalilin da ya sa mafiyawan sassan kasar babu hasken lantarki.
Bayanan da Daily Trust ta tattara sun ce layin Delta power plant ne kadai ke da megawatt 41 sai layin Afam da ke da megawatt 1.7.
Hakan ya zo kwanaki biyar da durkushewar babban layin lantarkin da hakan ke jefa sassan kasar cikin duhu.
Har yanzu dai babu takamaiman dalilin da ya sa layin lantarkin ya fadi a wannan karon, amma a wancan karon, ministan lantarki Adebayo Adelabu, ya ce wata gobara ce da ta tashi ta haddasa faduwar layin.

Kotu ta soke zaben shugaban majalisar dokokin jihar Gombe

Kotun sauraren kararrakin zabe ta Tribunal ta soke nasarar da shugaban majalisar dokokin jihar Gombe Abubakar Luggerewo ya samu a zaben da aka yi masa a watan Maris.
Abubakar Luggewo dai na wakiltar karamar hukumar Akko, a majalisar dokokin jihar, a jam’iyyar APC.
Mai shari’a Michael Ugar ya yanke hukuncin cewa a gudanar da zaben cike gurbi nan da kwanaki 30 masu zuwa.

An zakuda shugabancin kamfanin mai na NNPC

Bayanan da ke fitowa daga kamfanin kula da man fetur na kasa NNPC na cewa an yi wa mafiyawan manyan daraktocin kamfanin ritaya daga aiki, duk da sauran watanni kusan 15 da suke da shi kafin wa’adin ritayarsu ya cika.
Wannan matakin kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito, na zuwa ne kwanaki kadan bayan da kamfanin ya sanar da sallamar manyan mataimakan shugaban kamfanin su uku.
Daga cikin wadanda aka sallama, akwai Abdulkabir Ahmad da ke kula da bangaren iskar gas da Adokiye Tombomieye da ke kula da sashen albarkatun fetur.
A cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar da sanyin safiyar Talata, ya ce an dauki wannan matakin ne domin kara inganta aikinsa yadda zai zo daidai da zamani.

Majalisar dokokin jihar Kano ta gayyaci matashin da ya tsinci Naira Miliyan 15 kuma ya mayarwa mai shi

0

Majalisar dokokin jihar Kano ta
gayyaci matashi Auwalu Salisu da ke sana’ar tuka babur din adai-daita Sahu,
bayan da ya mayar da wasu makudan kudade har naira miliyan 15 ga wani fasinjan
sa dan asalin kasar Chadi.

Wannan na zuwa ne bayan bukatar hakan da dan
majalisa mai wakiltar karamar hukumar Doguwa Alhaji Salisu Muhammad ya gabatarwa
majalisar, yayin zamanta na yau, karkashin jagorancin shugabanta Alhaji Isma’il
Jibril Falgore.

Majiyar DCL Hausa ta Daily Trust ta ruwato cewa matashin  mai shekaru 22 ya mayar da kuddaden ne bayan
da fasinjansa ya manta da su a cikin adai-daita sahun sa.

Yayin zaman majalisar, dan majalisa Muhammad ya ce matashin
ya nuna tsantsar tawakkali da kuma hali na gari wajen mayar da kudaden idan aka
yi la’akari da halin matsin da ake ciki, a don haka ya kamata majalisar ta
karrama shi.

Wannan ce ta sa shugaban majalisar ya amince da bukatar, yayin
da ya amince a gayyaci matashin sannan yayi alkawarin cewa majalisar zata
tallafa masa.

Dukannin mambobin majalisar 44 sun amince da wannan
bukata, a cewar su wannan zai karfafawa sauran matasa gwiwa kan su rika sanya
gaskiya cikin harkokin su na yau da kullum.

 

 

Kotu ta daure mutumin da ya saci lemon kwalba a Adamawa

Wata kotu a jihar Adamawa ta yanke hukuncin daurin watanni 6 ga wani matashi Nafi’u Sabe da aka samu da laifin satar katan 6 na maltina.
An dai yanke masa wannan hukunci bayan da ya amsa laifinsa na satar wannan maltina.
Alkaliyar kotun Hafsat Abdurrahman ce ta yanke wannan hukunci.
Nafi’u Sabe ya amsa laifinsa inda ya ce ya saci wannan maltina ne a kasuwar Jimeta jihar Adamawa a Agustan, 2023, inda ya yi nadamar aikata hakan.

Nijeriya ta biya bashin Naira tiriliyan 2.34 cikin watanni 6 – DMO

Hukumar kula da basukan Nijeriya ta DMO ta sanar cewa kasar ta kashe kudi Naira tiriliyan 2.34 wajen biyan basuka a cikin watanni 6.
A rubu’i na biyu na shekarar 2023 dai, kasar ta biya bashin Naira bilyan 849.58. Bayanai daga hukumar ta DMO sun ce a rubu’in farko na shekarar ta 2023 an biya bashin Naira bilyan 874.13 na cikin gida tare da bilyan bashin kasashen waje na Naira bilyan 617.35. 
DMO ta ce jimilla kudin sun kama Naira tiriliyan 1.24.

An fara caccakar Tinubu bisa yadda yake rabon mukamai

Kungiyar marubutan da ke kare hakkin bil’adama ta HURIWA ta zargi shugaban Nijeriya Bola Ahmad Tinubu da nada mukamai a tsakanin ‘yan’uwa da aminnan arzikinsa kadai, inda kungiyar ta yi zargin cewa yana nada muhimman mukaman ne daga ‘yan kabilar Yarabawa.
Kungiyar ta yi wannan zargin ne a cikin wata sanarwa daga babban jami’inta Emmanuel Onwubiko, inda sanarwar ta yi magana kan nadin Gwamnan babban bankin kasa CBN da shugaban hukumar tattara kudin haraji ta FIRS da Shugaba Tinubu ya yi a kwana-kwanan nan, da ya nada duk Yarabawa.
Kungiyar ta bukaci shugaba Tinubu da kada irin layin da tsohon shugaban kasa Buhari ya bi wajen irin wadannan mukamai.

Gwamnan Edo ya umurci a kulle ofishin mataimakinsa, bayan rikicin siyasa da ke tsakaninsu

Rikicin siyasa na ta kara ruruwa tsakanin Gwamnan Edo da mataimakinsa

Da sanyin safiyar Litinin din nan, mataimakin Gwamnan jihar Edo Philip Shaibu ya tarar da an kulle kofar shiga ofishinsa a gidan gwamnatin jihar.
Dama dai an dade ana takun-saka tsakaninsa da Gwamna Godwin Obaseki ta dalilin wanda zai gaje shi a zaben 2024 na Gwamnan jihar.
Shaibu Philip dai ne mataimakin Obaseki tun 2016, da bayanai ke cewa yana son a bashi takarar Gwamna a 2024 idan wa’adin Obaseki ya kare, yayin da shi kuma Gwamna Obaseki ke da wanda yake son ya gaje shi.
Mataimakin Gwamnan dai ya zargi gwamnan da yunkurin tsige shi daga mukaminsa, dalilin da ya sa har sai da jiga-jigan jam’iyyar PDP a jihar suka sa baki batun ya kwaranye.
Wannan sa’in-sa dai ce ta ci gaba, har ta kai ga an fitar da ofishin mataimakin Gwamnan ya zuwa wani kango da ba a kammala ginawa daga wajen gidan gwamnati.
Da sanyin safiyar Litinin din nan kuma mataimakin Gwamnan ya kama hanyar zuwa ofishinsa, ya tarar an kulle kofar shiga.

Tinubu ya nada sabbin ministoci biyu

0
https://drive.google.com/uc?export=view&id=1Oklk4-i2wqrZ-3332VbCttNLkNX4GCRu
Ministocin sune Dr. Jamila Bio Ibrahim daga jihar Kwara wadda aka bai wa mukamin babbar ministar kula da harkokin matasa da wasanni. Sai dai Ayodele Olawande da Shugaba Tinubu ya nada karamin minista a ma’aikatar kula da matasan ta Nijeriya.

https://drive.google.com/uc?export=view&id=1eO3vxzhLxHYiiHZTI_uXG4SNXdYRhfiO
Dr. Jamila Ibrahim 
Jaridar DailyTrust ta ruwaito fadar shugaban Nijeriya a cikin wata sanarwa na cewa Shugaba Tinubu ya tura da sunayensu ga Majalisar Dattawa domin tabbatar da su.

Babu wanda ya yi barazanar tsige Akpabio daga mukaminsa – Majalisa

Majalisar dokokin Nijeriya ta sa kafa ta shure wasu rahotannin da ake yadawa a kafafen watsa labarai cewa wasu fusatattun ‘yan Sanatoci na shirin tsige shugabansu Sanata Godswill Akpabio.
Akwai wasu rahotannin da kafafen yada labarai suka watsa a ranar Asabar cewa ana shirin tsige shugaban majalisar dattawan Nijeriya Sanata Godswill Akpabio.
Rahotonannin sun ce akwai wasu Sanatoci da suka yi wata ganawa ta musamman a kasar Saudi Arabia don su kitsa yadda za a tsige Akpabio.
Sai dai, mai magana da yawun majalisar Yemi Adaramodu a cikin wata sanarwa a ranar Asabar, ya bayyana wadannan rahotannin da cewa ba su da tushe bare makama.