Shugaban Zimbabwe ya nada ‘ya’yansa biyu mukamin minista a gwamnatinsa
Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya nada dan cikinsa David Kudakwashe Mnangagwa mukamin karamin minista bayan sake zabensa da aka yi a matsayin shugaban kasar.
Wannan nadi dai ya tayar da kura a siyasar kasar, inda wasu ke zargin shugaban kasar da nadin ‘yan’uwa da abokan arziki a gwamnatinsa.
An nada David Kudakwashe Mnangagwa mai shekaru 34 a mukamin karamin ministan kudi a yayin da aka nada Tongai Mafidhi, da ga dan’uwan shugaban a matsayin karamin ministan shakatawa na kasar.
Emmerson Mnangagwa dai ya ayyana sunayen mutane 26 da ya nada mukaman ministoci a sabuwar gwamnatin.
A shekarar 2017 dai ne aka fara zaben Mnangagwa mai shekaru 80 a matsayin kasar Zimbabwe.
Tinubu na kwana da tunanin talakawan kasa – Shettima
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya jaddada aniyar shugaba Bola Tinubu na ba da fifikon jin dadin rayuwa ga dukkanin ‘yan Nijeriya kamar yadda suke a cikin shirye-shirye da manufofin gwamnatinsa.
Mataimakin shugaban kasan ya bayyana haka ne a ranar Litinin din nan a wajen bikin kaddamar da rabon kayan abinci na Naira biliyan 5.1 da gwamnatin jihar Sokoto ta yi ga masu karamin karfi domin rage radadin cire tallafin man fetur.
“Shugaba Bola Ahmed Tinubu shugaba ne mai tausayi wanda yake kwana da kuma tashi kowace rana da tunanin yadda zai rage wa ‘yan Nijeriya halin da suke ciki musamman marasa karfi a cikinmu” inji Shettima.
Ba mu saba doka ba don mun murtsuke baburan Okada a Abuja – Hukuma
Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa a babban birnin tarayyar Nijeriya Abuja, ta ce murtsuke baburan yan Okada da ta yi ba saba doka ba.
Deborah Osho, shugabar aiyuka a hukumar ta DRTS ce ta bayyana hakan a wata hira da ta yi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Abuja ranar Lahadi.
Kamfanin na dillancin labarai na NAN ya bada wani rahoto a ranar 31 ga watan Agustan da ya gabata na yadda hukumar ta kama tare da murtsuke babura guda 400 na yan acaba da aka samu da laifin gudanar da aiki ba bisa ka’ida ba a birnin na Abuja.
Zaben shugaba mai nagarta na kara wa kasa kima a idon duniya inji Dr Sirajo Yakubu
Kwararren lauya a Nijeriya Dr Sirajo Yakubu Batagarawa na da ra’ayin cewa kasashe masu tasowa na iya kai wa duk inda ba su tsammani ta fuskar ci gaba, muddin suka rika zabar mutane masu nagarta a wajen shugabanci.
Dr Sirajo Yakubu Batagarawa wanda shi ne shugaban Sashen Koyon Aikin shari’a da Aikin Lauya na Kasa-da-Kasa a Jami’ar Nile, Abuja na magana ne a taron masana kan siyasa, tattalin arziki da yakar miyagun laifuka a Jami’ar Cambridge da ke kasar Ingila a lokacin da ya ke gabatar da makala mai taken: Kima da Mutunci (Integrity).
Malamin jami’ar ya ce akwai bukatar a yaki cin hanci da rashawa da karfin tuwo, muddin ana so a samar da ci gaba mai dorewa a cikin kasa, inda ya kara da cewa babu kasar da za ta ci gaba, matukar cin hanci ya yi mata katutu.
Da ya koma ta fuskar siyasa kuwa, kwararren lauyan ya ce akwai bukatar a tsaftace siyasa musamman a kasashe masu tasowa daga banga da sara-suka da kage da cin mutuncin juna ta yadda za ta zamo abin koyi na kwarai ga matasa masu tasowa.
Ya ce akwai bukatar kasashe masu tasowa da su tashi tsaye wajen yaki da bambancin addini, bangaranci ko al’ada, ta yadda hadin kansu zai ba su damar kawo ci gaba mai ma’ana ga kasarsu don su amfana.
A bangaren kafafen yada labarai kuwa, Dr Sirajo Yakubu Batagarawa ya shawarce su da su ba da gudunmuwa yadda ya kamata wajen yaki da cin hanci da rashawa ganin irin tabon da aikata hakan ke jazawa ga kima da martabar wadanda aka samu da aikata laifin.
APC A jihar Katsina ta taya ‘yan takararta murnar samun nasara a kotu
Shugaban jam’iyyar APC na jihar Katsina, Alhaji Sani Aliyu Daura ya taya yan takarar jam’iyyar murna bisa nasarar da suka samu a kotun sauraren kararrakin zaɓe (Election Tribunal) yana mai bayyana hakan a matsayin nasara ga jam’iyyar APC da magoya bayanta
Yan takarar da suka samu nasarar a hukuncin daban-daban wanda kotun ta zartas sun haɗa da Honarabul Sani Aliyu Ɗanlami na mazabar majalisar tarayya ta karamar hukumar Katsina da Honarabul Abubakar Yahaya Kusada na mazabar Kankia/Kusada/Ingawa wadanda kotu ta maido masu da nasarar su a babban zaben watan Fabrairun 2023 da ya gabata tare da soke zaben yan takarar PDP da aka bayyana a farko a matsayin wadanda suka samu nasara.
Akwai kuma yan majalisun tarayya na Mazabar Ƙanƙara/Faskari/Sabuwa da Batsari/Safana/Danmusa waɗanda kotun zaben ta bayyana zabukan su a matsayin wadanda basu cika ba tare da bada umarni a sake zaben a inda aka bayyana
Da yake tsokaci akan nasarar, shugaban jam’iyyar APC na jihar Katsina, Sani Aliyu ya bayyana cewa magoya bayan APC sun yi bakin kokarin su domin wannan nasara a lokacin zaben, yana mai cewa hukuncin kotun ya tabbatar da muradin dubban al’ummar mazabun wadanda suka fita suka jajirce wajen ‘kada ma yan takarar jam’iyyar APCn kuri’un su
“Magoya bayan mu sun bayyana muradin su ta hanyar kuri’un su kuma gashi yanzu yar gwadal ta nuna cewa lallai yan takarar APC suka ci zabe kuma tun akwatunan zaben,”
“Abinda muke shedawa a yanzu shine kyawun tsarin Demokradiya da kuma mahimmancin bin doka da oda, mun ce anyi mamu ba dai dai ba, mun kai koken mu inda ya dace, kuma gashi an share mamu hawayen mu, muna jinjina ma adalcin bangaren shari’a.
“A madadin jam’iyyar mu ta APC a jihar Katsina Ina taya yan majalisun mu murna bisa wannan nasara da suka samu a kotu wanda ya tabbatar da cewa Katsina ta APC ce,”.inji shugaban jam’iyyar.


