Monday, April 6, 2026
Home Blog Page 493

Yakin bai kare ba- Atiku Abubakar

0

 

Dan takarar shugaban Najeriya karkashin
Inuwar jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya sake jadadda watsin da ya yi da
hukuncin kotun sauraren kararrakin zabe, da ya tabbatar da Bola Tinubu a matsayin
halastaccen shugaban kasar.

 

Yayin wani taron manema labarai
da ya yi da yammacin yau a birnin tarayya Abuja, Atiku Abubakar ya ce “Yakin
bai kare ba” a cewar sa babu wata-wata zai garzaya zuwa kotun koli.


A wajen taron manema labaran, Atiku Abubakar ya fito karara ya
bukaci lauyoyinsa da su yi gaggawar shigar da kara kotun koli sannan su fara
tattara hujjoji.

“ Ni ba bakon shari’a bane, don haka taron
lauyoyi da babaken dogayen riguna ba zai razana ni ba, kuma idan ka bi tarihin
siyasa ta na kasance dan gwagwarmaya da bana barin ta kwana, don haka zan yi
duk mai yiwuwa don kwato abinda dama nawa ne a gaban shari’a” inji Atiku
Abubakar.

Atikun ya kuma ci gaba da cewa wannan yakin ba
don biyan bukatun sa dari bisa dari yake yi ba, a’a don tilastawa hukumar zaben
kasa mai zaman kanta INEC ta daidaita sahun ta, ta kuma gane cewa kotu tana da
karfin tayar da hukuncin zalunci da ta yanke.


Zulum zai daure ‘yan bangar siyasa shekaru 7 a gidan kaso

Gwamnan jihar Borno Prof Babagana Umara Zulum ya sa hannu kan dokar da za ta ba da a daure duk wanda aka samu laifin bangar siyasa a jihar.
Gwamnan ya sa hannu kan dokar ne tare da karin wasu dokoki 8 da majalisar dokokin jihar ta amince da su.
Gwamnan ya ce an dauki wannan matakin ne domin dakile yawan matsalolin bangar siyasa da yi wa yara kanana fyade a jihar.
Prof Babagana Umara Zulum ya ce bayan wannan hukunci na daurin shekaru 7. Sannan masu daukar nauyin su ma ba za a bar su haka nan ba, sai an hukunta su.

Harin ‘yan ta’adda ba zai sare mana guiwar yakar ta’addanci a jihar Katsina ba – Dikko Radda

Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda ya ce hare-haren ta’addanci da ‘yan bindiga ke kai wa a yankunan karkarar jihar ba zai sare wa gwamnatinsa guiwa ba ta daina yakarsu.
Malam Dikko Umaru Radda ya sake nanata cewa ba zai yi sulhu da ‘yan bindigar ba har sai idan su ne suka ji wuta suka nemi su ajiye makamansu.
Da ya ke magana don murnar cika kwanaki 100 a bisa karagar mulki, Gwamna Radda ya ce gwamnatinsa na nan na daukar matakai daban-daban da za su magance matsalar tsaron jihar.
Ya ce sama da kudi Naira bilyan 7 gwamnatinsa ta kashe don sayo kayan aikin da za a yaki wadannan ‘yan ta’adda a jihar. Daga cikin kayan aikin kamar yadda ya ce akwai motoci masu sulke 10 da motoci kirar Toyota Hilux guda 65 sai babura 700 da za a rarraba wa jami’an tsaro su gudanar da ayyukansu.
Gwamnan ya ce gwamnatin jihar ta kuma dauki matasa 1,500 a karkashin sabuwar cibiyar inganta tsaro ta ‘Katsina Community Watch Corp’ domin su kare yankunansu. Ya kara da cewa yanzu haka ana horar da su yadda ya kamata.

Kudin Aikin Hajjin 2024 sun tunkari N5m

0

Hukumar jin dadin Alhazai ta Nijeriya  NAHCON ta bukaci maniyyata da ke son gudanar da ibadar aikin Hajj a shekarar 2024 da su saka mafi karanci kudin da suka kai Naira miliyan 4.5,  inda ta bayyana cewa aikin hajji mai zuwa zai yi tsada.

Shugaban Hukumar NAHCON, kuma Babban Jami’in Hukumar, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan, wanda ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai jiya Talata a Abuja

Hukumar ta kuma yi nuni da cewa ana duba rahotannin kwamitocin na aikin Hajjin bana na 2023 da ya gudana.

Ya ce tuni hukumar ta fara kaddamar da shirye-shiryen domin tunkarar yadda za a yi aikace-aikacen maniyyata da ke son yin Aikin Hajjin shekarar 2024

Kotu ta hana NNPP dakatar da Kwankwaso

0

 

Alkalin Babban Kotun Jihar Kano Mallam Usman Na’abba ya jingine dakatarwar da jam’iyyar NNPP tsagin Dr. Boniface Aniebonam ta yi wa tsohon gwamnan Kano Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso. Kazalika alkalin kotun ya dakatar da Dr. Boniface da ‘yan tawagarsa daga bayyana kansu a matsayin shugabannin jam’iyyar har sai an kammala shari’a. Alkali Usman Na’abba ya kuma bukaci hukumar zabe ta INEC da ka da ta yi mu’amula da wadannan mutane a matsayin shugabannin jam’iyyar NNPP.

Wannan hukuncin dai ya biyo bayan karar da aka shigar a gaban kotun ne bayan dakatarwar da su Dr. Boniface din suka yi wa Kwankwaso a ranar 29.08.2023. Sai dai kuma jaridar Punch wacce ta ruwaito wannan labari na jingine dakatarwar Kwankwaso ba ta bayyana ko matakin ya shafi korar da shugabannin na NNPP suka yi wa jagoran Kwankwasiyya daga jam’iyyar a wannan Talata ba. A ranar 05.10.2023 kotun za ta ci gaba da sauraran wannan kara da ke a gabanta.

Mai dokar barci: ‘Yan sanda sun sace babur din ‘yan fashi a Ghana

0

 Jami’an tsaro a birnin
Tamale na arewacin Ghana sun kama wasu ‘yan sanda guda biyu da laifin sace
babur din wasu ‘yuan fashi da aka kama.

Tun farko ‘yan sandan sun
sacewa wasu ‘yan fashi babur din ne bayan da bude wuta a dai-dai lokacin da
wata kotu take gab da yanke hukuncin fashi da makami da ake zargin abokin su da
aikatawa.

Tuni dai aka tsare yan sandan biyu da suka
hadar da Lance Copral Muhammad Aboagye da Sergent Elvis Emmanule, inda kuma aka
bude kundin bincike akan su.

A bincike farko-farko da jami’an tsaro suka
gudanar sun gano cewa dai-dai lokacin da ‘yan sandan ke musayar wuta da mutanen
bayan sun bude wa kotun wuta, a lokacin ne su kuma ‘yan sandan suka zagaya
bayan kotun inda masu laifin suka ajiye ababen hawan su ba tare da wata-wata ba
kuma suka yi awon gaba da mashin din.

Bayan bincike da kama mutanen 13 ne kuma suka
gane mashin din su a lokacin da ake hole su a shalkawatar rundunar ‘yan sandan kasar,
kuma ba tare da bata lokaci ba, suka shaidawa jami’an tsaro cewa wannan shine
mashin din su da aka sace.

Jaridar Ghanian Times ta ruwaito cewa tuni aka
adana mashin din a shalkawatar rundunar ‘yan sandan kasar, yayin da aka fara bincike
don gano sauran Babura 3 da ‘yan fashin suka ce an sace musu.

DSS ta kama wasu mutane da ake zargi da karkatar da tallafin da gwamnatin tarayya ta bayar don rabawa jama’a

0

Hukumar tsaron sirri ta DSS a Najeriya ta sanar da kama wasu mutane
da hannu a karkatar da kayayyakin abincin da gwamnatin tarayya ta samar don
rabawa jama’a.

Hukumar ta ce duka mutanen da ta kama jami’an hukumar bayar da
agajin gaggawa na kasa NEMA ne, kuma mafi yawan su an kama su ne a kasuwar
Lafia da ke jihar Nasarawa lokacin da suke tsaka da sayar da kayan ga ‘yan
kasuwa.

Mai Magana da yawun hukumar Peter Afunanya
ya ce tuni aka kamo wasu kayayyakin da mutanen suke yunkurin sayarwa.

Afunanya ya kuma bukaci jama’ar Najeriya da su
sanya idanu sossai kan masu sayar da kayan abinci don basu rahoton masu sayar
da kayan da gwamnati ta tanadar don rabawa jama’a a kyauta.

Haka kuma hukumar ta ce ta kama wasu mutanen na
daban wadanda sune suke shirya yadda za’a sace kayan kafin ma a kai su kasuwa.

NNPP ta kori jagora Kwankwaso

0

 

Jam’iyyar NNPP ta sanar da korar jagoranta Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso bayan da ta dakatar da shi makonni uku da suka gabata, sakamakon zargin sa da yiwa jam’iyyar zagon kasa tun bayan kammala babban zaben kasar.

Gidan rediyon Faransa, RFI Hausa, ya ce korar  ta Kwankwason na cikin wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar dauke da sa hannun sakataren yada labaranta na kasa Abdulsalam Abdulrasaq.

Wannan dai na zuwa ne kasa da kwanaki uku bayan da wani tsagi na jam’iyyar ya sha alwashin gurfanar da tsohon gwamnan Kanon da wasu mabiyan sa a gaban shari’a, sakamakon zargin wadaka da fiye da naira biliyan 1 da aka tara a asusun jam’iyyar na kudaden sayar da fam din ‘yan Takara.

Sanarwar ta Abdulrasaq ta kuma kara da cewa korar kwanwason zata fara aiki ne nan take, yayin da yayi karin hasken cewa an dauki matakin ne bayan da Kwankwason ya ki bayyana a gaban kwamitin ladabtarwa na jam’iyyar, sakamakon gayyatar sa da aka yi don amsa wasu tambayoyi. 

Sakataren yada labaran jam’iyyar ya kuma tabbatar da cewa korar Rabi’u Kwankwaso na da goyon baya a cikin kundin jam’iyyar na shekarar 2022.

To sai dai da yake jam’iyyar ta rabu gida biyu kan matakin korar ta Kwankwaso, guda daga cikin masu goyon bayan sa kuma mai bincken kudi na jam’iyyar Ladipo Johnson yace bangaren da suka kori Kwankwason basu da alkibla kwata-kwata.

Akwai fargabar yajin aikin NLC ba zai yi tasirin da ake bukata ba

0

Bankuna da hukumomin gwamnati da ke biyayya ga kungiyar
kwadago ta NLC a Najeriya sun kauracewa guraren ayyukan su, yayin da yajin aikin
ya doshi sa’o’I 24.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya NLC ya ruwaito
cewa baki daya bankuna basu yi aiki a fadin kasar ba, yayin da wasu daga cikin
ma’aikatun gwamnati suka fita aiki wasu kuma suka zauna a gida.

Tun farko dai kungiyar NLC ce ta kuduri aniyar tafiya yajin
aikin na kwanaki biyu don nunawa gwamnatin kasar bacin ranta a game da rashin
mayar da tallafin man fetur da ya haddasa tsadar rayuwa.

A cikin sanarwar da kungiyar ta fitar ta ce zata kuma tsunduma
wani yajin aikin na sai baba ta gani nan da makonni biyu masu zuwa matukar
gwamnati bata dauki matakin gyara bayan wannan yajin aikin da suka aiwatar ba.

DCL Hausa ta gano yadda mambobin na kungiyar NLC suka kulle
kofofin shiga gidan talabijin din NTA na kasa da na Radio don hana ma’aikata shiga.

To amma dai masana a kasar na ganin zai yi wuya
wannan yajin aikin yayi tasiri la’akari da barakar da ke tsakanin kungiyoyin
kwadago guda biyu na NLC da TUC, kasancewar TUC ta barranta kanta da mambobin
ta daga wannan yajin aiki.

‘Yan ta’adda sun kashe mutane 7, sun raunata 5 sun sace 11 a wani sabon hari a Katsina

Wasu mutane dauke muggan makamai da ake kyautata zaton ‘yan ta’adda ne, sun afka kauyen Doka na karamar hukumar Sabuwa a jihar Katsina cikin daren Litinin wayewar Talata, inda suka rika harbin kan mai uwa da wabi.
Bayanan da DCL Hausa ta tattara sun ce ‘yan ta’addar a yayin wannan harbe-harbe, sun kashe mutanen gari 7 suka raunata 5.
Wata majiya daga yankin da ta nemi a sakaya sunanta, ta ce mutanen sun kuma sace wasu daga al’ummar yankin su 11 tare da kwashe dabbobin da har ya zuwa lokacin hada wannan labarin ba a kai ga sanin hakikanin yawansu ba.
Kauyen Doka dai na cikin mazabar Mai Bakko a cikin karamar hukumar Sabuwa a jihar Katsina.
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta hannun mai magana da yawunta ASP Abubakar Sadiq Aliyu ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce mutane 6 ne aka kashe tare da raunata 5.
Duk da rundunar ‘yan sandan ba ta tabbatar da yawan mutane da dabbobin da ‘yan ta’addr suka sata ba, sai dai ta ce jami’anta yanzu na can na bincike a cikin dajin da ake kyautata zaton an tafi da mutane da dabbobin domin kwato su.
ASP Aliyu Abubakar Sadiq ya ce an ma kara tsaurara matakan tsaro domin ceto mutanen da kuma kare afkuwar hakan a gaba.