Monday, April 6, 2026
Home Blog Page 494

Rundunar ‘yan sandan Kano ta musanta yaduwar mata masu shan jini

0

 

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta musanta labarin da ke yawo cewa an samu
wasu mata da ke shanyewa mutane jini a sassan jihar, ko kuma su sace musu wani
sashe na jikin su ta hanyar tsafi.

A wani gajeran bidiyo da ya wallafa a shafin sa na Tik-Tok, jami’in yada
labaran rundunar ‘yan sandan jihar SP Abdullahi Kiyawa ya ce a rahotannin da
suka samu a unguwannin Kurna, kwana hudu, Hotoro, Zango, Rijiyar Lemo da kuma Gwagwarwa,
an kama wasu mata da ake zargin masu shan jinin ne kuma har ana yunkurin afka
musu.

SP Kiyawa ya bayar da misalin yadda lamarin ya faru a unguwar kwana hudu,
inda ya ce wasu ‘yan mata ne suka shiga wani gida don kaiwa matar gidan Chajin
waya, shigar su ke da wuya kuma sai daya ta tambayi izinin matar gidan don kama
ruwa, jin haka ke da wuya kuma matar gidan ta fara ihu, kuma ba tare da bata
lokaci ba mutanen suka far musu.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan na jihar Kano ya ce tuni suka kama
mutane 8 cikin wadanda ke yunkurin daukar doka kan wadanda ake zargi da shan jini,
yana mai cewa tun daga lokacin da aka fara yada wannan jita-jita babu wanda aka
samu da rahoton an shanye masa jini ko kuma wani sassa na jikin sa ya bace
kamar yadda ake yadawa ba.

SP Haruna ya kuma bukaci jama’ar Kano da su kwantar da hankalin su yana mai
cewa wannan labari kawai an shirya shi ne don haifar da rudani, sannan ya
gargadi masu irin wannan ta’ada da su kuka da Kansu matukar aka kama su.

Zulum ya kaddamar da dashen itatuwa milyan 1.2

Gwamnan jihar Borno Prof Babagana Umara Zulum ya kaddamar da dashen itatuwa na shekarar 2023, da za a dasa itatuwa milyan 1.2 a fadin jihar.
Kazalika, Gwamna Zulum ya sanar da cewa ana kyautata zaton cewa nan da shekarar badi, 2024, za a dasa itatuwa milyan 10 a jihar.
A cikin wata sanarwa daga mai magana da yawun Gwamna Zulum, Malam Isah Gusau da DCL Hausa ta samu kwafi, ta ce Gwamna Zulum ya shawarci ma’aikatar kula da muhalli da ta watsar da tsarin dashen itatuwa na dauri ta rungumi na zamani domin tafiya da zamani.
Sanarwar Malam Isah Gusau ta ce Gwamna Zulum ya kudurci aniyar dasa itatuwan ne domin yaki da kwararowar hamada da matsalolin da suka jibinci muhalli a jihar.
Kazalika, Prof Zulum ya bukaci mutane da su rage amfani da itace wajen girki don gudun gurbatar yanayi da alkinta muhalli.
Gwamnan Babagana Umara Zulum ya ce daga cikin dashen itatuwa milyan 10 da jihar ke hankoron dasawa nan da 2024, ana kyautata zaton a dasa itace 200,000 a kowace karamar hukuma 27 da ke jihar, jimilla dashe milyan 5.4 a yayin da gwamnatin jiha za ta samar da dashe milyan 5.

Gwamnan Zamfara ya rufe wasu manyan kasuwannin shanu a jihar

Gwamnatin Zamfara ta sanar da rufe kasuwannin shanu 8 nan take a kananan hukumomi biyar na jihar.
 Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da al’adu Mannir Haidara ya fitar ranar Lahadi a Gusau.
Kasuwannin shanun da abin ya shafa su ne: Danjibga da Kunchin-Kalgo da ke Tsafe; Kasuwan shanu na Bagega da Wuya a garin Anka.
 “Sauran su ne Dangulbi da Dansadau a Maru, Dauran a Zurmi da Nasarawar Burkullu a karamar hukumar Bukkuyim.
Gwamnatin jihar ta ce ta dauki matakin ne biyo bayan sake bullar cinikayyar siyar da shanun sata da wasu da ake zargin ‘yan fashin dajin ne suke yi a yankunan da lamarin ya shafa.

‘Yan ta’adda sun farmaki wani masallaci sun kashe masallata a Kaduna

Rahotanni daga jihar Kaduna da ke Arewacin Nijeriya na cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hari a wani masallaci da ke kauyen Saya-Saya a karamar hukumar Ikara kamar yaddajaridarDailytrust taruwaito. 
Majiyar ta DCLHausa ta ce a yayin harin ‘yan bindigar sun kashe masallata 5.
Lamarin dai ya faru ne da misalin karfe 8 na dare na ranar Juma’a a daidai lokacin da mutanen ke gudanar da Sallar Isha’i a wannan masallaci.
Mansir Alhassan shi ne 
mukaddashin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ya tabbatar da faruwar lamarin a Asabar din nan a Kaduna.

Gwamnatin Dikko ta raba N20m ga iyalan ‘yan sintirin da ‘yan ta’adda suka hallaka a Katsina

Gwamnatin jihar Katsina ta sanar da rarraba kudi Naira milyan 20 ga wasu daga cikin iyalai da ‘yan’uwan ‘yan sintirin Vigilante da ‘yan ta’adda suka hallaka a lokacin da suke bakin daga a jihar.
Sakataren Gwamnatin jihar Abdullahi Garba Faskari a lokacin rarraba kudin a Katsina, ya ce kudin wani tallafi ne ga iyalan mamatan ba wai diyyar rayukansu ba.
A nasa bangaren, babban mataimaki na musamman ga Gwamnan jihar Katsina kan ‘yan gudun hijra da wadanda iftila’i ya fada mawa Sa’id Ibrahim Danja ya ce gwamnatin ta kuma dauki nauyin kula da lafiyar duk jami’an da aka raunata a lokacin da suke kokarin kare rayuka da dukiyoyin al’ummar yankunansu.
Ya ce akwai jami’an tsaro 4 da mutanen gari 32 da ke kwance a asibitin kashi na ‘Orthorpaedic Katsina’ da asibitin koyarwa na Federal Teaching Hospital, Katsina inda suke karbar magani da kulawar likitoci duk kyauta bayan da gwamnatin Dikko ta dauke musu dawainiyar.
Ya ce wannan tallafi an yi shi ne da zummar tallafar wadanda suka samu raunuka da iyalan wadanda suka rasu a lokacin arangama da ‘yan ta’adda musamman a kananan hukumomin da ke fama da karancin tsaro a jihar.
Hon Sa’id Ibrahim Danja ya ce iyalan ‘yan sintiri 33 ne suka amfana da wannan tallafin kudin, inda aka rarraba musu Naira dubu dari biyar-biyar, a yayin da wadanda suka samu raunuka su 10 suka samu Naira dubu 250 kowane.
Kazalika, akwai wani jami’in dan sanda mai mukamin ‘Insfekta’ da ya samu rauni aka bashi gudunmuwa kudi Naira dubu 250 sai jinjirin matar wani soja da ya rasa ransa a filin daga aka bata gudunmuwr kudi Naira milyan 1. Bayanai dai sun ce ‘yan ta’addar sun hallaka wannan soja ne a ranar da ake sunan jaririn.

Yaron da na taimaka na neman zame min ‘karfen-kafa’ – Aisha Humaira

Fitacciyar jaruma a masana’antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood Aisha Humaira ta fito fili ta nuna rashin jin dadinta dangane da wani taimako da ta yi wa wani yaro masoyinta da ya zo Kano saboda ita.
Humaira ta ce bayan an kawo mata yaron ta yi masa goma ta arziki ta kuma yi alkawarin cewa za ta dauki nauyin karatunsa. 
Ta ce yanzu haka yaron sau biyu tana sa a mayar da shi garinsu yana dawowa wai sai an kawo shi wajenta.
A karshe dai jarumar ta nuna cewa ta iya masa iya abin da za ta iya don haka ta mika shi ga hukumar Hisbah a jihar Kano.

Tinubu zai raba gilashin rashin gani guda milyan 5 ga masu matsalar idanu a Nijeriya

Tinubu zai raba gilashin rashin gani guda milyan 5 ga masu matsalar idanu

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya amince da shirin samar da gilashin ido miliyan 5 ga ‘yan kasar masu matsalar ido bayan ganawa da shugabannin gidauniyar Peek Vision.

Barayi sun zane masu gadi sun yi awon gaba da kadarorin N20m a Jigawa

Wasu da ake kyautata zaton barayi ne sun afka ma’aikatar samar da ruwan sha a garin Birnin Kudu da ke karamar hukumar Birnin Kudu a jihar Jigawa, inda suka lakada wa ma’aikata duka tare da sace wasu kayayyaki na sama da Naira miliyan 20.
Kwamishinan Albarkatun Ruwa, Ibrahim Garba ne ya bayyana haka a lokacin da ya ziyarci cibiyar a ranar Juma’a.
Garba, wanda ya nuna damuwarsa kan lamarin, ya ce gwamnati za ta dauki tsauraran matakai kan masu yin zagon kasa ga kokarinta na samar da ruwan sha ga mazauna jihar.

Matashi ya kashe mahaifinsa don yin tsafin da zai kudance

Wani matashi mai suna Ridwan dan kimanin shekaru 20 a duniya ya hallaka mahaifinsa domin ya yi tsafin da zai sa ya samu kudi a jihar Ogun.
Kungiyar ‘yan sintirin jihar Ogun dai ne suka yi nasarar kama matashin a yankin Ijebu ta arewa a jihar. Kwamandan sintirin Soji Ganzallo a cikin wata sanarwa ya ce jami’ansa ne suka yi nasara kama matashin a lokacin da suke aikin sintiri, sai suka ji hayaniyar mutane a cikin wani kango.
Ganzallo ya ce da jami’ansa suka kutsa kai cikin gini, sai suka tarar da mutum sharbe cikin jini, wanda ake zargin ya yi aika-aikar ya tsere.
Kwamandan ya ce nan take ya ba jami’ansa umurnin su kamo wanda ake zargin cikin sa’o’i 24, kuma haka aka yi, suka nemo shi a inda ya ke labe a cikin daji.

Tura ta kai bango: Dole mu yi yajin aiki – NLC

Kungiyar Kwadago a tarayyar Nijeriya NLC ta ce za ta fara wani yajin aikin gargadi na kwanaki biyu daga ranar Talata 5 ga wannan wata na Satumba.
NLC ta ce yajin aikin ya zame mata tilas domin ta nuna adawa da matakin gwamnatin kasar kan nuna gazawarta karara na kasa magance kalubalen da yan kasar ke fuskanta na matsanancin hali sakamakon janye tallafin man fetur ya haifar.
A ranar 2 ga watan Agustan da ya gabata ne dai kungiyoyin kwadago na NLC da TUC suka shirya zanga-zangar lumana a wasu daga cikin manyan biranen kasar domin nuna rashin amincewarsu kan matakin da gwamnatin shugaba Tinubu ta dauka na janye tallafin man fetur.