Sojojin mulkin Nijar sun sauke shugabannin jami’o’in Agadez da Zinder
Hukumomin mulkin sojan Nijar sun cire shuwagabannin jami’o’i biyu daga mukamin su
A cikin wata sanarwa ce da suka fitar hukumomin mulkin sojan Nijar suka bayyana cire wasu malaman jami’a daga mukamman da suke rike da su a cikin jami’o’in daban daban ciki kuwa har da shuwagabannin jami’o’in Agadez da Zinder
Wannan na zuwa ne kwanaki biyu bayan da wani gungunsu na malaman jami’ar da ya kunshi malaman 37 ya fitar da wata sanarwa wacce a ciki suka nisanta kansu da wata sanarwar ta daban da kungiyar ta SNECS ta fitar wacce a ciki ta kawo goyan bayan ta da sunan dukkan malaman ga sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar
Shi dai wannan gungu na malaman jami’ar ya ce ko alama ba ya goyan bayan wannan juyin mulki
Kazalika wata sanarwar ta daban da kakakin gwamnatin rikon kwaryar ta Nijar ya karanta na cewa an kawo karshen aikin sakataren ma’aikatar ilimi mai zurfi tare da shugaban hukumar da ke kula da jarabawar Baccalauréat da ake kira da OBEECS
Wasu rahotannin kuma na cewa tuna aka kira daya daga cikin malaman Pr Malaman Issa an kiraye shi ofishin jami’an tsaron na Gendarmerie
Ministocin Tinubu za su lakume Naira bilyan 8.6 matsayin albashi
Gwamnatin Shugaba Tinubu za ta kashe kudi Naira bilyan 8.6 wajen biyan albashi da alawus-alawus cikin shekaru 4 na ministoci 48 da aka nada.
Daily Trust ta rawaito cewa jimillar kudin ta kai haka ne bayan da hukumar tattarawa da rarraba kudaden shiga ta kammala bitar albashi da alawus-alawus na manyan ma’aikatan gwamnati.
Sai dai wani kwararru a bangaren tattalin arziki ya sanar da manema labarai cewa yawan kudin ya ci karo da kudiri ko jawabin Shugaba Tinubu na farko, da ke cewa zai rage yawan kudaden da ake kashewa jami’an gwamnati.
Kwararrun suka ce nada wadannan ministocin da yawa, shi zai sa su ma su nada masu taimaka musu na musamman da hakan zai kara nauyi ta gwamnati.
Lokacin farko dai kenan da aka samu yawan ministoci a Nijeriya sun kai 48 tun 1999 da aka dawo dimokradiyya. Zamanin tsohon shugaban kasa Buhari na da ministoci 42.
Tsohon shugaban kasa Good luck Jonathan na da ministoci 33 sai Marigayi Umaru Musa Yar’adua ya yi ministoci 39. Shi kuwa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi ministoci 42.
Ba zan iya sayar da “manpower” ko kayan mata a Saudiyya ba – Sadiyya Haruna
Sadiyya Haruna ta ce ba za ta iya sayar da kayan da take sayarwa a Nijeriya a kasar Saudiyya ba.
A cikin gajeran bidiyo da ta wallafa, ta ce, ta gode da arzikin da Allah ya yi mata a Nijeriya; ba ta bukatar daukar maganin maza da kayan mata zuwa kasa mai tsarki.
Fitacciya a shafukan sada zumunta da aka jima ana zargin ta da batsa ta hanyar sayar da wadannan kayayyaki na shan cece-kuce a baya-bayan nan a kan tangardar da aurenta da mawaki G-Fresh ke fuskanta.
A wata hira da Sadiyya Haruna ta yi da DCL Hausa a 2021, ta ce, ba ta jin kunyar wadannan kayayyaki da take sayarwa.
An garzaya da kocin Man City Guardiola Asibiti
Mai horar da ‘yan wasan kungiyar Manchester City Pep Guardiola ba zai samu jagorancin kungiyar ba har na wasanni biyu da za ta buga nan gaba sakamakon wata tiyatar gaggawa da za a yi masa a gadon bayansa.
Guardiola wanda yanzu haka yana Barcelona inda aka yi masa tiyata yana kuma murmurewa ana sa ran ba zai jagoranci City ba a wasannin da za ta yi da Sheffield United a wannan Lahadi da Fulham a ranar 2 ga Satumba ba, inda mataimakinsa Juanma Lillo zai maye gurbinsa na wucin gadi.
City ta ce kocinta wanda ya jagoranci yan wasanta suka lashe kofina uku rigis a kakar da ta gabata na fama da “matsanancin ciwon baya na ” kuma tuni aka fita da shi zuwa birnin Barcelona don domin yi masa tiyata.





