Monday, April 6, 2026
Home Blog Page 500

Gwamnatin Najeriya ta kwaso yan kasar Kusan 200 da aka kulle a gidan yarin Libya

0

Gwamnatin Najeriya
ta kwaso yan asalin kasar 161 da aka daure su a gidajen yarin kasar Libya daban-daban
sakamakon aikata laifukan da suka sabawa ka’idar yin kaura.

Jakadan Najeriya a Libya Ambasada Kabiru Musa ne ya bayyana hakan a wata
sanarwa da ya fitar ga manema labarai a birnin tarayyar kasar Abuja.

A cewar Ambasada Musa gwamnatin Najeriya
ta rika kai gwauro da kai mari wajen ganin an saki mutanen da aka garkame a
gidan yarin don basu damar komawa gida, da nufin sake gina rayuwar su.

Sanarwar ta kuma kara da cewa tuni
mutanen suka isa Najeriyar, yayin da aka gargade su da su kaucewa yunkurin tsallakawa
zuwa turai ta barauniyar hanya don gudun fadawa hannun hukumomi ko kuma bata
gari.

Wannan dai ba shine karon farko da ake samun ‘yan Najeriya da dama na
tsallakawa zuwa turai da saharar Libya ba, inda kuma a mafi yawan lokuta suke
gamuwa da masu garkuwa da mutane ko yan fashi ko kuma  a wasu lokutan su ci karo da jami’an tsaro.

 

‘Yan sanda sun cafke ‘dilan’ wiwi cikin tashar mota a Kano

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wani matashi mai suna Rayyanu Ibrahim, wanda aka fi sani da Yellow, a lokacin da yake siyar da tabar wiwi a cikin babbar tashar mota ta Mallam Kato da ke cikin kwaryar birnin jihar.
Rundunar ‘yan sanda ta Anti-Daba, karkashin jagorancin OC Musa Gwadabe, ta kama wanda ake zargin, bayan samun rahotannin sirri game da yadda yake gudanar da ayyukansa na cinikayyar tabar wiwi a cikin tashar motar ta Mallam Kato.
Da yake amsa laifin, Rayyanu Yellow, ya ce ya shafe sama da shekaru biyar yana sana’ar ta sayar da tabar wiwi.
Ya ce wannan shi ne karo na biyu da ‘yan sanda suka kama shi kuma a baya ya tuba amma daga bisani ya koma ruwa.

An gurfanar da matar da ta caka wa wani mutum almakashi a Kano

Wata kotun shari’ar Musulunci da ke zamanta a unguwar Gama ta jihar Kano ta tasa keyar wata mata mai suna Hafsa Musa a gidan gyaran hali bisa zarginta da daba wa wani mutum mai suna Buhari Mikail da almakashi.
‘yan sandan sun shaida wa kotun cewa wadda ake kara ta aikata laifin ne a lokacin da fada ya barke tsakanin kawarta da mutumin inda ta daba wa masa almakashin ya kuma yi masa mummunan rauni.
Alkalin kotun ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare ta a gidan yari tare da dage sauraron karar zuwa ranar 19 ga watan Satumba domin yanke mata hukunci.

Abuja ba wajen kiwon shanu ba ne – Wike

Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT) Nyesom Wike ya sha alwashin kawo karshen kiwon shanu a cikin birnin Abuja.
Wike, tsohon gwamnan jihar Ribas ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ya kira sa’o’i kadan bayan an rantsar da shi a matsayin ministan na Abuja ranar Litinin.
“Za mu tuntubi makiyaya cikin laluma domin mu ga yadda za su daina (kiwo a fili) saboda ba za mu iya barin shanu a cikin gari ba,” in ji shi.

Ya zama dole mu yi karin albashi – Sabon ministan Kwadago

0

 

Gwamnatin tarayya ta bayyana aniyar ta na magance matsalolin rayuwa ga ma’aikatan kasar ta hanyar bullo sabon mafi karancin albashin ma’aikata da sauran abubuwan jin dadi da zai kawo magance wahalar rayuwa da suke ciki sakamakon cire tallafin man fetur.
Simon Lalong, sabon ministan kwadago da samar da ayyukan yi ya yi wannan alkawarin a lokacin da yake karbar mukaminsa a ranar Litinin a Abuja.
Lalong ya ce hakan ya zama wajibi domin bunkasa kyakkawar alaka tsakanin gwamnatin tarayya da kuma kungiyoyin kwadago na NLC da kuma TUC.

Matar da yunwa ta kusa yi wa lahani a Katsina ta samu kabakin arziki

Matar nan mai suna Hadiza Abubakar da ke zama a birnin Katsina da ta kwashe kwanaki kusan 9 ba ta ci abinci ba, ita da ‘ya’yanta, ta samu tallafin kudi tsaba har Naira milyan 7 daga al’umma a sassan kasar nan daban-daban.
Malama Hadiza ‘yar asalin jihar Kwara, ta zo Katsina da zama bayan da mijinta dan asalin Giwa, jihar Kaduna ya zo da ita. Bayanan da DCL Hausa ta tattara sun ce mijin ya gudu ya barta, babu abinci. Tana fita nemar wa ‘ya’yanta abin da za su ci ne, wani mai babur ya banke ta, har ta ji raunin da ba za ta iya fita neman abinci ba.
Wannan dalilin ne ya sa ta kwashe kwana kusan 9 ba su ci abinci ba, ita da ‘ya’yanta, dalilin da ya sa masana kiwon lafiya suke ganin kamar yunwa ta kama matar da ‘ya’yanta.
Bayan banke ta da babur ne, wasu makwabtanta, suka je domin yi mata “kamu” a inda ta ji raunin, a nan ne suka fahimci halin da take ciki har wani matashi mai suna Ahmad Abdullahi BilHaqqi ya yi mata bidiyo ya tura a kafar sadarwar zamani domin nemar mata taimako. Dalilin da ya sa bidiyon ya karade ko’ina har aka samu wannan tallafi. 
Bayan nadar bidiyonta ne suka garzaya da ita asibitin Turai Yar’adua, Katsina domin ceto ranta. Sai dai daga bisani aka mayar da ita asibitin kwararri na Medical Center, Katsina.
Da yake yi wa manema labarai karin haske a Katsina matashin da ya wallafa bidiyon matar, Ahmad Abdullahi BilHaqqi, ya ce mutane sun bayar da gudunmuwa sosai daga sassa daban-daban na kasar nan.
Ya ce mutane sun ba da gudunmuwar kudi da ta kayan abinci da yanzu haka ake da buhunan shinkafa 7 manya da kanana 6.
Kazalika akwai wake buhu da masara da Taliya da Indomie da man girki da ‘kwamaso’ da sauran kayan abinci iri daban-daban.
Ahmad Abdullahi BilHaqqi ya ce an samu wannan tallafi ne kasa da kwanaki uku da aka fitar da sanarwar neman taimakon.
Matashin ya ce za su saya mata gida da kudin kuma su ba ta jarin da za ta rika sana’ar da za ta rike kanta da yaranta hudu, biyu maza, biyu mata.
Ahmad Abdullahi BilHaqqi ya ce sun kira taron manema labarai ne domin a sanar da al’umma yawan tallafin da aka samu kuma gwamnati ta daukin nauyin hidimomin matar. Ya kara da cewa su na sanar da mutane da su daina turo da wata gudunmuwa, don bata-gari na amfani da lambar bankin su na zamba-cikin aminici.
Daga cikin kungiyoyin da suka shige gaba don ba da tallafin da kuma ganin al’umma sun tallafa, akwai kungiyar Katsinawa ta HOHDI da ta Shagari Low Cost Community Development da kungiyar da ‘yar gwagwarmaya Fauziyya D Sulaiman da ke Kano ke jagoranta da sauransu.

Gwamna Uba Sani ya zabtare kudin rajistar manyan makarantun jihar Kaduna

0

 

Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya sanar da rage kudin rajistar shiga manyan makarantun jihar, a wani mataki na rage tsadar rayuwar da ke addabar jama’a ciki har da Kaduna. Sanarwar da DCL Hausa ta samu a kan wannan batu ta nuna cewa yanzu kudaden rajistar makaratun jihar sun koma kamar haka:

Jami’ar Jihar Kaduna 

– Kudin makarantar sun koma 105,000 a maimakon N150,000
Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Nuhu Bamalli 
– Kudin makarantar sun koma N50,000 a maimakon N100,000
Kwalejin Kiwon Lafiya ta Shehu Idris Makarfi
-HND: N70,000 a maimakon N100,000
-ND: 52,000 a maimakon N75,000
Wannan na zuwa ne a kwanaki kalilan bayan da wasu mata a jihar ta Kaduna suka yi zanga-zangar tsadar rayuwa.

Ana zanga-zanga a Kano

Zanga-zanga ta barke a Kano duk da haramcin hakan da ‘yan sanda suka yi.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Kano Muhammad Usain Gumel ya haramta wata zanga-zanga da magoya bayan jam’iyyar NNPP da na APC suka bukaci mambobin su da su fito su yi a jihar.
Zanga-zangar dai ta biyo bayan zargin bayar da cin hanci ga sashen shari’a na jihar ya yi ba daidai ba game da batun shari’ar  zaben gwamna na 2023.
Kwamishinan ya ce duk wani yunkurin aiwatar da wannan zanga-zanga, zai zamo wata kafa ta kawo tsaiko ga tsaron kasa.
Sai dai kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito, jim kadan bayan fitar da wannan sanarwa, masu zanga-zangar suka yi fitar farin dango, suka cike titunan jihar suka nufi gidan gwamnatin jihar.

‘Yan majalisa na son gwamnati ta yaki cutar ‘malaria’ da karfin tuwo

Kwamitin majalisar wakilan Nijeriya kan cutar sida, tarin fuka da cutar zazzabin cizon sauro ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta kafa dokar ta baci kan cutar malari duba da irin hatsarin da ke tattare da cutar.
Shugaban kwamitin Amobi Godwin Ogah ya sanar da hakan a ranar yaki da cutar malari ta duniya.
Ya ce duba da irin hatsarin da cutar ke da shi ya ga ya dace gwamnati ta dauki dukkanin matakan da suka kamata don magance matsalar da yakar sauron da ke haddasa ta.
Amobi Godwin ya bukaci gwamnatoci daga dukkanin matakai da su bullo da tsare-tsaren da za su fatattaki sauro a cikin al’umma.
Dan majalisar ya ce kwamitin zai yi aikinsa ta hanyar bibiyar cibiyoyin kiwon lafiya na yankunan karkara don gani da ido yadda hukumomin kula da lafiya daga tushe ke aiwatar da aikin yaki da cutar zazzabin cizon sauro da alkinta shirin Roll back Malaria.

Nijeriya na bin bashin Naira bilyan 132 na kudin lantarki ga kasashen Nijar, Togo da Benin

Nijeriya na bin bashin kudi Naira bilyan 132.2 ga kwastomomin kasashen ƙetare a Nijar da Togo da Benin na kudin lantarkin da suka sha na tsawon shekaru hudu.
Kididdigar kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito, ta nuna cewa ana bin wadannan kasashen wannan bashin ne tun daga shekarar 2018 har zuwa rubu’in farko na wannan shekara ta 2023.
Hukumar da ke lura da harkokin lantarki ta Nijeriya NERC ta fitar da jadawalin yadda aka raba wutar ga kasashen, inda ta ce an biyo kasashen bashi ne bayan da aka caje su kudin lantarki Naira bilyan 180.8, a yayin da su kuma suka biya Naira bilyan 48.57, kaso 26.8% kenan suka iya biya.
Kididdigar ta nuna cewa an fi bin kasar Benin kaso mai tsoka na kudin, inda ake binta, Naira bilyan 72.1 sai kasar Nijar da ake bi Naira bilyan 31.3 da kasar Togo da ake bi Naira bilyan 10.03.