Sunday, April 5, 2026
Home Blog Page 6

Kotu ta bai wa ICPC izinin binciken na’urorin El-Rufa’i

0

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bai wa Hukumar da ke Yaki da cin Hanci da rashawa mai zaman kanta, ICPC, izinin bincike da nazarin na’urorin da aka kwato daga gidan tsohon gwamnan Kaduna, Nasir Ahmad El‑Rufai.

Alkalin kotun, Joyce Abdulmalik, ta bayar da umarnin ne bayan karar da lauyan ICPC Osuobeni Akponimisingha ya gabatar, inda ya roki kotu ta ba hukumar damar bude na’urorin domin binciken fasaha da fitar da bayanai.

Na’urorin da aka ambata sun hada da wayoyin salula, kwamfuta da kuma na’urorin ajiya na bayanai, inda kotu ta ce ICPC na da hurumin duba sakonnin WhatsApp, kira, hotuna da sauran bayanai domin binciken da take yi.

Sai dai El-Rufai ya shigar da wata kara daban yana kalubalantar binciken gidansa, inda ya bukaci kotu ta bayyana cewa an take masa hakkinsa tare da neman diyya ta Naira Biliyan daya.

Gwarzon aikin jarida ya cika 67: Tarihin hikima da jagorancin Dan Malikin Lafiya, Yusuf Sarki Muhammad

Daga Muhammad Aliyu Mustapha

A yau muna murnar zagayowar ranar haihuwar babban jigo a masana’antar watsa labarai—Alhaji Yusuf Sarki Muhammad, wanda aka fi sani da sarautarsa ta gargajiya, wato Dan Malikin Lafiya.

Yusuf Sarki Muhammad dai shahararren masanin aikin jarida ne, kwararre a fannin sadarwa, kuma ga shi fitaccen jagora abin koyi a harkar jarida ta zamani.

Duk wanda ya san Yusuf Sarki, zai shaida cewa shi tamkar wata “makaranta ce sukutum-da-guda” idan aka yi la’akari hikimarsa da kuma kwarewarsa a aiki.

Ta yin amfani da kamfaninsa, wato: ‘Actuality and Clips’ da ke Kaduna, Dan Malikin Lafiya ya kwashe shekaru yana rainon matasan ‘yan jarida da ma’aikatan kafafen yada labarai, inda yake koya musu dabarun aikin rediyo da talabijin kai har ma da kafafen sada zumunta na zamani.

Irin zurfin da Yusuf Sarki ya yi a harkar watsa labarai da kuma fahimtarsa ga wannan rayuwar ta duniyar sun sa ya zama tamkar wani babban rumbun ilimi ga duk mai kishirwar kwarewa da hidimtawa kasa. Dan Malikin Lafiya ya shahara da kwarewa bakin aiki da jajircewa wajen kiyaye dokokin tsarin aiki, don tsira da mutunci.

Yawancinmu muna cin moriyar sana’o’inmu ne sakamakon tarbiyya da jagorancinsa; ya nuna mana sirin wannan sana’a kuma ya dasa mana kishin aikin. Mu ne wadanda suka fi amfana da yalwar iliminsa, kuma muna alfaharin dorewar wannan gado nasa.

Muna addu’ar Allah Ya ci gaba da ba shi lafiya da arziki da tsawon kwana; Ya kuma ci gaba da kwararo masa albarkarSa ba tare da yankewa ba har abada. Amin!

Hukumar lafiya ta duniya ta koka kan irin kudaden da ake kashewa a yake-yake duk da yunwar da ake fama da ita a fadin duniya

0

Babban Daraktan Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya soki yadda kasashen duniya ke kashe makudan kudade wajen yaki, yana mai cewa hakan na nuna cewa an karkatar da muhimmancin abubuwan da ya kamata a ba fifiko a kai.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, ya ce kudaden da ake kashewa kan harkokin soja a duniya sun kai dala tiriliyan 2.7 a cikin shekara guda, alhali kiyasin MDD ya nuna cewa dala biliyan 93 kacal ake bukata a duk shekara domin kawo karshen yunwa a duniya nan da shekarar 2030.

Ya ce hakan na nufin kasashen duniya na kashe kusan sau 30 fiye da haka wajen yaki da juna maimakon tabbatar da cewa kowa ya samu abinci, yana mai cewa wannan bambanci na nuna gazawar duniya wajen tinkarar matsalar yunwa.

Hukumar tsaro ta Civil Defence ta kama tsohon dalibin wata makaranta kan zargin satar kayan dakin gwaje-gwaje a jihar Jigawa

0

Rundunar tsaron Civil Defence ta Nijeriya a Jihar Jigawa ta kama wani tsohon dalibin makaranta bisa zargin yunkurin satar kayan dakin gwaje-gwaje a wata makaranta da ke Dutse.

Mai magana da yawun rundunar a jihar, Badruddeen Tijjani, ya ce an kama wanda ake zargi mai suna Aliyu Musa mai shekara 22 ne yayin da yake kokarin kwashe na’urorin microscopes guda biyar daga babban dakin gwaje-gwajen makarantar.

Ya ce binciken farko ya nuna cewa wasu kayan gwaje-gwaje sun taba bacewa a baya, kuma an gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bisa tuhume-tuhumen shiga makaranta ba bisa ka’ida ba da kuma sata.

Sanatoci 9 sun sauya sheka zuwa jam’iyyar hamayya ta ADC a majalisar dattawan Nijeriya

0

Akalla sanatoci tara daga jam’iyyu daban-daban sun sanar da komawarsu jam’iyyar ADC a zauren majalisar dattawan Nijeriya, lamarin da ya sake sauya fasalin siyasa a majalisar.

Daga cikin sanatocin da suka sauya sheka akwai Aminu Waziri Tambuwal (Sokoto ta Kudu), Enyinnaya Abaribe (Abia ta Kudu), Binos Yaroe (Adamawa ta Kudu), Victor Umeh (Anambra ta Tsakiya), Tony Nwoye (Anambra ta Arewa), Lawal Usman (Kaduna ta Tsakiya), Ogoshi Onawo (Nasarawa ta Kudu), Austin Akobundu (Abia ta Tsakiya) da Ireti Kingibe (FCT).

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya karanta wasikun sauya shekar a zaman majalisar, inda wasu daga cikin sanatocin suka danganta matakin da rikice-rikicen cikin jam’iyyunsu na baya.

Akpabio ya ce sauya shekar na nuna matsalolin cikin gida a jam’iyyun adawa, yana mai cewa har yanzu jam’iyyar APC na da rinjaye a majalisar da sanatoci 87, yayin da ADC ta karu zuwa sanatoci bakwai.

Gwamnan Kano Abba kabir Yusuf ya gargadi kwamishinoninsa da su gujewa cin amanar gwamnati da kuma fitar da sirrinta

0

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya gargadi mambobin majalisar zartarwar jihar da su guji rashin aminci, takaddama a tsakaninsu da kuma fitar da sirrin gwamnati.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin taron majalisar zartarwar karo na 38, inda ya bukaci su hada kai domin ci gaban jihar da walwalar al’umma, yana mai cewa lokacin sabani da zargin juna ya wuce.

Ya kuma jaddada cewa wasu sauye-sauyen siyasa a jihar suka sa shi da wasu manyan shugabanni suka mara wa jam’iyyar APC baya domin samun karin hadin kai da gwamnatin tarayya.

Gwamnan ya kuma tabbatar da murabus din kwamishinoni biyar bayan sauyin siyasar, tare da taya sabbin ‘yan majalisar da suka lashe zaben cike gurbi murna, yana mai bukatar su yi aiki tukuru domin al’ummarsu.

Birtaniya za ta rufe wasu hanyoyin jiragen sama da kuma tituna, baya ga girke jami’an tsaro don tarbar shugaban Nijeriya Bola Tinubu a mako mai zuwa

Mahukunta a Burtaniya sun sanar da tsauraran matakan tsaro a garin Windsor yayin da Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, zai kai ziyara ta musamman a mako mai zuwa bisa gayyatar Sarkin Birtaniya, King Charles III.

‘Yan sandan Thames Valley sun ce za a kara takaita zirga-zirgar jiragen sama a sararin samaniyar Windsor daga karfe 7 na safe zuwa karfe 11:59 na dare a ranar 18 ga Maris, yayin da za a tura jami’an tsaro da suka hada da masu makamai, rundunar doki da jami’an kula da hanyoyi.

Hukumomin sun ce za a kuma yi amfani da na’urorin CCTV, katangar tsaro da sauran matakai domin tabbatar da tsaron ziyarar da za a yi a Windsor Castle, tare da gargadin cewa duk wanda ya karya dokar hana zirga-zirgar jiragen sama zai fuskanci hukunci.

Dan takarar Gwamnan jihar Sokoto na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Sa’idu Umar ya fice daga jam’iyyar

0

Tsohon dan takarar gwamnan Jihar Sokoto a 2023 karkashin jam’iyyar PDP, Saidu Umar, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar, yana mai danganta matakin da rikicin shugabanci da ke ci gaba a matakin kasa.

Umar ya bayyana hakan ne cikin wasikar murabus da ya aika wa shugaban jam’iyyar a mazabarsa ta Sarkin Adar Kofar Atiku da ke karamar hukumar Sokoto ta Kudu. Ya ce sabanin shugabanci da kararraki a kotuna sun janyo rashin hadin kai da tabarbarewar harkokin jam’iyyar.

Ficewar tasa na zuwa ne kwanaki kadan bayan tsohon gwamnan jihar, Aminu Waziri Tambuwal, shi ma ya bar PDP, lamarin da ke nuna karin sauyin siyasa da ke faruwa a jihar. Duk da haka, Umar ya ce zai ci gaba da goyon bayan dimokuradiyya da ci gaban jihar.

Amurka ta batar da sama da Dala Biliyan 11 cikin kwanaki 6 a yakinta da Iran – Rahotanni

0

Rahotanni sun ce yakin da Amurka ke yi da Iran ya lakume sama da Dala Biliyan 11 a makon farko kacal.

Jaridar The New York Times ta ruwaito cewa an bayyana hakan ne a wani bayani da jami’an tsaro suka gabatar wa ‘yan majalisar dokoki a Pentagon.

Rahoton ya nuna cewa kudin sun hada da makamai da sauran kayan yaki da aka yi amfani da su a farkon hare-haren, inda aka ce kusan Dala Biliyan 5.6 na makamai aka kashe cikin kwanaki biyu na farko.

Wani bincike na cibiyar Center for Strategic and International Studies ya kiyasta cewa sa’o’i 100 na farko na farmakin da ake kira Operation Epic Fury sun kashe kusan Dala Biliyan 3.7, yayin da wasu kididdiga ke nuna cewa Amurka na kashe kusan dala biliyan daya a kowace rana a yakin.

Ni cikakken dan dimokradiyya ne – Shugaba Bola Tinubu

Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya sake jaddada kudurinsa na kare dimokuradiyya da bin doka a Nijeriya, yana mai cewa shi “dan dimokuradiyya ne na gaske”.

Ya bayyana hakan ne yayin buda baki da shugabannin jam’iyyar APC da kuma majalisar shawarwari tsakanin jam’iyyu a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Tinubu ya ce dimokuradiyya a Nijeriya ta samu ne bayan doguwar gwagwarmaya, inda wasu suka shiga zanga-zanga, aka tsare su, wasu ma suka yi gudun hijira.

A cewarsa, shi da sauran masu gwagwarmaya sun tsaya tsayin daka wajen tabbatar da hadin kan Nijeriya da dorewar dimokuradiyya.

Shugaban ya kuma ce ci-gaban dimokuradiyya na bukatar gaskiya da adalci a cikin jam’iyyun siyasa, yana mai jaddada cewa dole ne a mutunta rinjaye tare da bai wa marasa rinjaye damar fadin ra’ayinsu.

Hakazalika, ya kuma tabbatar wa jam’iyyarsa ta APC cewa zai ci gaba da kasancewa tare da ita.