Monday, April 6, 2026
Home Blog Page 501

‘Yan sanda sun kama mutanen da suka yi wa Sarkin Kano rashin kunya

0
https://drive.google.com/uc?export=view&id=1odnVNqLO5O-OkoSmTf6StxjAPN2U1IY3
Rundunar ‘yan sanda a jihar Kano ta ce ta yi nasarar kama karin wasu mutane uku da ake zargi da kalaman batanci ga Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Bayero.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Usaini Gumel, ne ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Kano.
Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa tun farko rundunar ta kama wasu mutane shida da ake zargi da hannu a lamarin.
Gumel ya bayyana sunayen wadanda ake zargin kamar haka; Abdulrazak Usman Sarki daga Disu Quarters, karamar hukumar Gwale, sai wani mai suna Fatihu Muktar Faruk Kano da kuma Usman Baba Attah, 25, mazaunin unguwar Kabara Quarters, Kano Municipal.

Sojojin ECOWAS sun sanya ranar afka wa sojojin Nijar

https://drive.google.com/uc?export=view&id=1bS6qjoGkErP1BnpUzoCcdfYuO4213r7d
Sojojin ECOWAS sun sanya ranar afka wa Nijar da makami domin dawo da Bazoum.
Shugabannin rundunonin sojojin kasashen kungiyar ne suka cimma wannan matsaya a taronsu na wannan Juma’a a birnin Accra na Ghana.
 Kafar yada labaran Aljazeera wacce ta ruwaito labarin ta ce sojojin duk da cewa sojojin sun sanya ranar da za su shiga Nijar Idan sulhu ya gagara amma dakarun na ECOWAS sun kauce wa sanar da jama’a sanin takamaimiyar ranar.

Tinubu zai raba wa talakawa buhunan shinkafa 100,000 a kowace jiha

https://drive.google.com/uc?export=view&id=1CFM-vvd-2mJFv6XPrZdp36_YmjWN0bum
Gwamnatin Tinubu ta bai wa kowacce jiha a Nijeriya Naira biliyan 5 domin a sayi kayan abinci don raba wa talakawa.
Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito gwamna Babagana Zulum na jihar Bornon na sanar da haka bayan taron Majalisar Tattalin Arziki ta kasa a Alhamis din nan.
Ya ce an umurci jihohi su sayi buhu 100,000 na shinkafa da buhu 40,000 na masara da takin zamani domin raba wa marasa karfi.

‘Yan sanda sun hallaka dan ta’adda sun kwato tumakin sata a Katsina

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta sanar da kashe wani dan ta’adda daya tare da kwato tumakin sata 60 a wata musayar wuta tsakaninsu da ‘yan ta’adda a kauyen Kogoro na yankin Daddara ta karamar hukumar Jibia a jihar Katsina.
Kazalika rundunar ‘yan sandan ta ce ta kuma yi nasarar kwato bindiga samfurin AK-47 da kuma alburusai 110.
A cikin wata sanarwa daga mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar ASP Aliyu Abubakar Sadiq, ta ce ‘yan sandan sun samu labarin ‘yan ta’addar sun durfafi kauyen Kogoro na yankin Daddara ta karamar hukumar Jibia a jihar Katsina, inda suke harbi na kan mai uwa da wabi suka sace tumaki. Da jin haka, DPO na karamar hukumar Jibia ya tattara jami’an ‘yan sanda suka far musu, aka yi musayar wuta. Da suka ji matsi ne suka watsar da wadannan dabbobi suka yi kokarin ranta a na kare. Bayan nan ne ‘yan sanda suka gano tumakin nan 60 da gawar dan ta’adda da bindiga da alburusai.
ASP Aliyu Abubakar Sadiq ya ce yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

Zafin kishi ya sa wani saurayi ya bugi budurwarsa har ya karyata a Kano

Kotun shari’ar musulunci da ke zamanta a ofishin hukumar Hisbah a Kano ta tsare wani saurayi Abbas Sadiq bisa zarginsa da karya budurwarsa bayan da ya same ta tana waya da wani saurayi daban.
Ana tuhumar Abbas Sadiq mazaunin Unguwar Sheka da laifuka uku da suka hada da hana ‘yancin dan’adam, amfani da karfi da kuma ji ma wani rauni.
‘Yan sandan sun sanar da kotu cewa budurwar ta ce musu haka kawai saurayin ya hau ta da bugu har ya karya mata hannu bayan da ya same ta tana waya da wani saurayin.
Da aka karanta masa laifukan, nan take ya amsa. Alkalin kotun Khadi  Sani Tanimu Sani Hausawa ya umurci da a cigaba da tsare shi a gidan gyaran hali har sai ranar 25 ga watan Agusta da za a sake zama.

Jagoran PDP A Jihar Katsina, Shema Na Shirin Shiga Jam’iyyar APC

Tsohan gwamnan jihar Katsina, Alhaji Ibrahim Shehu Shema, ya shirya tsaf domin barin jam’iyyarsa ta PDP zuwa jam’iyyar APC nan ba da jimmawa.
Barista Ibrahim Shehu Shema ya ziyarci shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje a gidansa da ke Abuja a daren jiya Asabar a cigaba da Shirye-shiryen shigarsa jam’iyyar APC.
Majiyarmu ta shaida mana cewa Shirye-shirye sun kammala na karɓar jagoran jam’iyyar PDP a jihar Katsina kuma jigo a matakin Kasa, Alhaji Ibrahim Shehu Shema zuwa APC.
Alhaji Ibrahim Shehu Shema ya yi gwamnan jihar Katsina daga shekarar 2007 zuwa 2015 kuma shi ne jagoran jam’iyyar PDP a jihar Katsina.

Barr Hannatu Musawa na da kwarewa da gogewar da duk ake bukata wajen gina kasa – Alhaji Abdullahi Yaya

Wani dan kishin kasa daga jihar Katsina Alhaji Abdullahi Umar Yaya ya yaba wa shugaban kasa Bola Tinubu da ya dauko Barr Hannatu Musawa domin nada ta matsayin minista kuma mamba a majalisar zartarwa ta kasa.
Abdullahi Umar Yaya ya ce duba da gida da tsatson da Barr Hannatu ta fito, da yadda mahaifinta marigayi Musan Musawa ya yi ta fadi tashin ganin an yi jagoranci na adalci a cikin al’umma tun zamanin su Malam Aminu Kano da cigaban talakawa ke zukatansu.
Ya ce Barr Hannatu ta cimma nasarori daban-daban a lungu da sako na jihar Katsina kuma ta kafa tarihin zama mace ta farko da aka nada matsayin mukamin minista daga jihar Katsina.
Alhaji Abdullahi Umar Yaya ya ce irin gogewa da kwarewar da Barr Hannatu ke da ita ya sa duniya ke mutuntata har shugaban kasa ya ga ya dace a ba da sunanta daga jihar Katsina don nada ta mukamin minista.
Kwararriya a aikin lauya, Barr Hannatu Musawa na da rajin kare hakkin bil’adama, sannan tana da burin ganin matasa sun samu sana’o’in hannu domin dogaro da kansu, sannan tana sha’awar rubuce-rubuce domin inganta ilmi.
Dan kishin kasar ya ce irin wadannan halaye na Barr Hannatu Musawa ne wasu matan da ma mazan ke kwaikwaya domin su kyautata wa al’ummarsu.
Ya yi godiya ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya zabi Barr Hannatu Musa Musawa a matsayin daya daga cikin ‘yan majalisar zartarwa ta kasa. Hakan ya nuna yadda shugaba Tinubu ke da adalci a tsakanin jinsi.
Alhaji Abdullahi Umar Yaya ya ce shugaban kasa Bola Tinubu ya saci zuciyar Katsinawa musamman matasa da ya yi wannan kyakkyawan zabi na Barr Hannatu Musawa daga jihar Katsina.

Wani Bakano ya raunata yaro don ya hana shi bashin koko da kosai

Kotun shari’ar musulunci a karamar hukumar Kiru ta jihar Kano ta tsare wani mutum mai suna Jaafar Lukman bisa zarginsa da raunata wani yaro dan wata mata Jamila Mai Kosai da ke sayar da koko da kosai, don sun hana mutumin bashin koko da kosai.
Kazalika, kotun ta yi zargin mutumin ya sa kafa ya harbe bokitin koko da kaskon suyar kosan da kuma kwanon da ake ajiye kosan matar a saman titi a lokacin da takaddamar ta barke.
‘Yan sanda sun ce bincikensu ya gano cewa mutumin ya tafi wajen matar ne da nufin ta ba shi bashin koko da kosai, amma dai matar ta hana saboda ta ce tana binsa bashin wasu kidin da bai biya ba.
Bayan ta hana shi ne ya sa kafa ya harbe bokitin kokon da kaskon suyar kosan har man ya yi buja-buja a kasa.
Lokacin da aka karanto masa laifukan da ake zarginsa da aikatawa, mutumin ya amsa, amma ya sanar da kotu cewa a lokacin ransa ne ya baci, Kasantuwar yana jin yunwa a lokacin.
Alkalin kotun, Khadi Usman Haruna Usman ya dage zaman sauraron shari’ar sai 4 ga watan Satumba, sannan ya umurci a ci gaba da tsare mutumin a gidan gyaran hali.

Dikko Radda ya nada sabon sakataren gwamnatin jihar Katsina

Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda ya amince da nadin Barr Abdullahi Garba Faskari a matsayin sabon sakataren gwamnatin jihar.
Abdullahi Garba Faskari dai shi ne tsohon mataimakin Gwamnan jihar Katsina Barr Ibrahim Shema a wa’adi na biyu na mulkin jihar Katsina daga 2011 zuwa 2015 da ya maye gurbin Arch Ahmad Musa Dangiwa da ya samu mukamin minista a Abuja.
Kamar yadda sanarwar da mai magana da yawun Gwamna Radda, Ibrahim Kaula Mohammed ya fitar, ta ce nadin ya fara aiki ne nan take.
Tun a watan Maris na 2019 dai Abdullahi Garba Faskari ya bar jam’iyyar PDP ya koma APC.
Ya dai rike mukamin babban lauyan gwamnati wato Attorney General a jihar Katsina daga 2003 zuwa 2007 zamanin Marigayi Malam Umaru Musa Yar’adua. Sannan bayan Gwamna Shema ya hau wa’adin farko na mulkinsa a jihar Katsina ma Abdullahi Garba Faskari ya ci gaba da rike mukamin kwamishinan shari’a na jihar daga 2007 zuwa 2009, inda ya bar ma’aikatar shari’a ya koma kwamishinan ilmi daga 2009 zuwa 2010.

‘Yan bindiga sun kai wa jami’an ‘yan sanda hari a Zamfara

‘Yan Bindiga Sun kai hari a ofishin ‘yan sanda na karamar hukumar Bundugu a jihar Zamfara, sun kuma hallaka tare da jikkata mutane.
Wata majiya ta shaida wa jaridar LEADERSHIP cewa gungun ‘yan bindigar da sun boye kansu a gonaki da ke kusa da inda suka kai farmaki a  ofishin ‘yan sanda.
Majiyar ta ci gaba da cewa wani jami’in dan sandan ya rasa ransa sakamakon artabu da ‘yan sandan suka yi da ‘yan bindigar.
Sai dai majiyar ta DCL Hausa ta tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Zamfara, ASP Yazid Abubakar, inda ya bayyana cewa basu da masaniya kan  harin, amma ya ce zai tuntubi baturen ‘yan sanda (DPO) da ke karamar hukumar Bungudu domin jin cikakken bayani.