Monday, April 6, 2026
Home Blog Page 502

Jaridar Katsina City News ta sauya suna zuwa Katsina Times Newspaper

Mawallafi kuma mallakin jaridar nan ta yanar gizo mai suna Katsina City News Malam Danjuma Katsina na sanar da jama’a cewa ya sauya sunan jaridar zuwa Katsina Times Newspaper.
A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Malam Danjuma Katsina, mamallakin jaridar ya ce hakan ya zamo wajibi domin cimma duk wasu tsare-tsare da za su sa jaridar ta zamo tsara a idon duniya ba kamar sunan Katsina City News ba da aka takaita a Katsina kadai ba.
Sanarwar ta ce za a iya samun dukkanin wallafe-wallafen da suka gabata ta shafin www.katsinatimes.com.
Malam Danjuma Katsina ya ce sun yi karatu a tsanake sun gano cewa akwai kasashe kusan 29 da ke da jaridu da ke amfani suna kusan makamancin wannan irinsu Khaleej Times da ke kasar Qatar, Tehran Times da ke kasar Iran, Istanbul Times da ke kasar Turkiyya da New York Times da ke kasar Amurka.
Sauran su ne Japanese Times ta kasar Japan, Hindustan Time ta kasar Indiya, Daily Times, Premium Times da ke a Nijeriya sai kuma yanzu da aka samu Katsina Times, ita ma a Nijeriya.
Mawallafin ya sanar cewa ya dakatar da wallafa a jaridarsa ta ‘The Links News’ domin kara yawan ma’aikata a jaridar Katsina Times. Ya kara da cewa tuni sun cimma yarjejeniya da wasu Editoci na manyan jaridun duniya domin dillanci da musayar labarai tsakaninsu da jaridar Katsina Times, inda Katsina Times za ta rika ba su labaran jihar Katsina, Nijeriya da ma nahiyar Afrika, su kuma za su rika ba ta labaran sauran sassan duniya.
Za a dai rika wallafa jaridar da Turanci da Hausa domim ta ilmatar, fadakar da nishadantar da masu karatu.

Tinubu zai binciki ayyukan bankin CBN

Shugaban Nijeriya Bola Ahmad Tinubu ya shaida cewa ba da jimawa zai fara bincike mai zurfi kan ayyukan bankin kasa na CBN.
Kazalika, shugaban kasar ya ce gwamnatinsa za ta yi garambawul ga aikin gwamnati da kuma gudanar da bincike mai zurfi kan tsarin biyan albashin ma’aikatan.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga mai magana da yawun shugaban kasar Ajuri Ngelale, inda ya rawaito shugaban kasar ya fadi haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugaban bankin duniya Mr Ajay Banga.

Shugaba Tinubu ya umurci a rufe duk wata kan iyaka da Nijeriya ta yi da Jamhuriyar Nijar

Shugaban Nijeriya Bola Ahmad Tinubu ya umurci da a rufe dukkanin iyakokin da Nijeriya ta yi da Jamhuriyar Nijar.
Sabon shugaban hukumar kwastam na kasa Adewale Bashir Adeniyi ya sanar da hakan a lokacin da ya ziyarci kan iyakar Magamar Jibia, jihar Katsina.
Ya ce shugaban kasa ya umurci da a rufe dukkanin iyakokin har sai baba-ta-gani ta dalilin hambarar da gwamnatin Bazoum da sojoji suka yi.

Jiga-jigan NNPP na neman Kwankwaso ya sauka daga jagorancin jam’iyyar saboda zargin zagon-kasa

Kungiyar shugabannin jam’iyyar NNPP na jihohi a Nijeriya sun yi kira ga jagoranta na kasa Engr Rabi’u Musa Kwankwaso da ya gaggauta yin murabus daga jam’iyyar ko su fatattake shi da karfin tsiya.
Jiga-jigan jam’iyyar sun ce su na zargin Kwankwaso wanda shi ne ya yi wa jam’iyyar takarar shugabancin Nijeriya a zaben 2023, na yi wa jam’iyyar zagon-kasa.
Sannan sun ce su na bukatar Rabi’u Kwankwaso da ya yi musu bayani dalla-dalla kan irin alakar da suka ga na wanzuwa tsakaninsa da jam’iyyar APC.
A cikin wata sanarwa daga Shugaban jiga-jigan jam’iyyar ta NNPP Sunday Oginni, ta zargi Kwankwaso ta hura wutar rikici a jam’iyyar domin ya yi uwa makarbiya da jam’iyyar daga wadanda suka kafa ta.

Cutar mashako ta diphtheria ta hallaka mutane 122 a Nijeriya – UNICEF

Ofishin Najeriya na Asusun Tallafa wa Ilimi da Ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) na yayata irin ƙoƙarin da ya ke yi na ganin an shawo kan yaɗuwar annobar cutar mashaƙon da ke shafar ƙananan yara a jihohi guda 27 a kasar. Izuwa watan Yuli na shekakar 2023, an sanar da waɗanda ake zargin sun kamu mutum 3,850, waɗanda aka tabbatar da kamuwar mutane 1,387 da cutar ta mashaƙo. Abin tashin hankali shi ne, an rasa rayuka mutane 122, wanda yawan mace-macen ya kai kaso takwas da ɗigo bakwai cikin ɗari 8.7%.
Ɓarkewar cutar ta fi shafar Jihohin Kano da Yobe da Katsina da Ikko da Abuja da Sakkwato da kuma Zamfara, waɗanda suka bayar da kaso casa’in da takwas cikin ɗari na waɗanda suka kamu da cutar.
Yawancin waɗanda aka tabbatar sun kamu da cutar, waɗanda a taƙaice sun kai kaso saba’in da ɗaya da rabi cikin ɗari sun shafi ƙananan yara ne waɗanda suke daga shekaru 2 – 14. 
Kamar yadda wakilin Ofishin Nijeriya na Asusun Tallafa wa Ilimi da Ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF), Ms.Cristian Munduate ta faɗa, “Abu ne mai matuƙar sosa rai jin cewa kaso ishirin da biyu cikin ɗari 22 %  ne kawai aka yi wa allurorin rigakafi da ake yi wa ƙananan yara.
“Yawancin waɗannan ƙananan yara da suka kamu da cutar mashaƙon, musamman waɗanda suka rasu, suna cikin waɗanda ba a yi wa allurorin rigakafin ko sau ɗaya ba. Buƙatar da ake da ita ta sanar da waɗanda ba a iya kaiwa gare su ba wani abu ne mai wuya ba.”
Domin ganin an ɗauki mataki kan ɓarkewar cutar,  Asusun Tallafawa Ilimi da Ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) na haɗin gwiwa da Cibiyar Shawo kan Yaɗuwar Cututtuka (NCDC) da Jihohin da abin ya shafa da Hukumar Kulawa da Bunƙasa Lafiya a Matakin Farko ta Ƙasa (NPHCDA) don ganin an bayar da taimako da tallafawa don ganin an yi tsari da kuma tabbatuwar ɗaukin da za a kai. Jajircewa da taimakon Asusun Tallafawa Ilimi da Ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ya faɗaɗa har zuwa nau’o’in tallafi daban-daban da suka haɗar da:
•Tsarawa da aiwatarwa da kuma tallafawa wajen sanar da bayanai game da afkuwar haɗura, sai kuma ayyukan da suka shafi sanya jama’a cikin ayyukan da suka shafi al’umma.
•Ɗaukar nauyin safarar kayayyakin rigakafi da sauran kayayyaki masu alaƙa da su izuwa jihohin da abin ya shafa, sai kuma ƙarfafa yin rigakafi akai-akai. 
•Bayar da horo ga jami’an Kula da lafiya da masu aikin sa-kai wajen ayyukan al’umma, sanar da afkuwar wasu haɗura da shigar da jama’a cikin ayyukan al’umma.
•Sanya ido kan ayyukan kai ɗauki game da ɓarkewar cututtuka.
•Nemowa da samar da takunkumin rufe fuska da sinadaran tsaftace hannu da magungunan samun kariya daga cutar mashaƙo. 
•Samar da kayayyakin amfani a ɗakin gwaje-gwaje da kayayyakin yi wa waɗanda ake zargin sun kamu gwaje-gwajen a Cibiyar Shawo kan Yaɗuwar Cututtuka (NCDC).
Ms Munduate ta ƙarfafa buƙatuwar da ake da ita na ganin an sami yaran da ba a iya yi wa rigakafin ba sakamakon hana shige da fice a yayin ɓarkewar cutar (COVID-19). Ya cigaba da cewa, “Yawancin yara ba a sami damar yi musu rigakafi ba a lokacin da aka hana shige da fice sakamakon ɓarkewar annobar KWABID (COVID-19). “Dole ne yanzu mu tashi tsaye don ganin mun cike wannan giɓin. Yaran da ba a yi musu rigakafin ko ɗaya ba, wato waɗanda ba a taɓa yi musu ba, su ne babbar damuwarmu.”
Dangane da wannan ƙididdiga mai ban takaici,  Ofishin Nijeriya na Asusun Tallafawa Ilimi da Ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) na kira da iyaye da wakilan ‘ya’ya da su tabbatar sun kai yaransu an yi musu rigakafi don kare su daga cututtukan da ake iya yin rigakafinsu, kamar cutar mashaƙo. Asusun na UNICEF zai ƙara ƙaimi wajen ganin an shawo kan wannan cuta da ta ɓarke da kuma yin aiki tare da hukumomi don ganin tabbatuwar lafiyar al’umma da kuma ganin kyautatuwar rayuwar yara ‘yan Nijeriya ta nan gaba.

Akwai bukatar a kara yawan hutun haihuwa ga mata ma’aikata daga watanni 3 zuwa 6 – UNICEF

Asusun kula da kanan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF ya ce akwai bukatar mahukunta su duba yiwuwar tsawaita wa’adin hutun haihuwa ga mata maaikatan gwamnati daga watanni 3 zuwa watanni 6.
Hakan kamar yadda babban jami’in UNICEF na Nijeriya Mr Rahama Rihood Mohammed Farah, ya sanar a bikin zagayowar makon shayar da nonon uwa na 2023 a Katsina, ya ce na da nufin ba iyaye mata damar shayar da jariransu sosai ba tare da an samu wata tangarda ba.
A sakon da Mohammed Farah ya aike da shi, da kwararre akan abinci mai gina jiki Mr Oluniyi Oyedokun ya karanta, ya kara kira ga mahukunta da su samar da wurare na musamman a ma’aikatun gwamnati da iyaye mata masu shayarwa za su rika shiga su na shayar da ‘ya’yansu yadda ya dace da ware wasu sa’o’i a matsayin lokuttan fita a shayar da jarirai.
A taken bikin na bana, 2023 “Ba da dama ga masu shayarwa – samar da yanayi mai kyau ga iyaye mata masu shayarwa da ke aiki”, UNICEF ta yi kira ga iyaye mata da ke shayarwa da su rika neman hakkinsu a ko’ina idan batun shayar da jariransu ya taso domin gudun kada ‘ya’yansu su kamu da cutar tamowa.
Sannan UNICEF ta bukaci matan da ke da ilmin zamani, su rika bincike don shiga kwasa-kwasan da za su tallafe su wajen inganta lafiyar ‘ya’yansu.
Taron na bana, da Asusun UNICEF ya shirya hadin guiwa da hukumar lafiya a mataki farko ta jihar Katsina suka shirya, an kuma yi kira ga masu rike da sarautun gargajiya, malaman addini, manema labarai da kungiyoyin fararen hula da su hada hannu wajen yekuwa kan shayar da jarirai nonon uwa zalla don tabbatar da lafiyar yaran da farincikin iyayensu.

Mutanen Nijar na aza tambaya kan matsayar Seini Oumarou

Kakakin majalisar dokokin Nijar Alhaji Seini Oumarou ya nuna damuwa kan takunkuman da ECOWAS da UEMOA suka saka wa Nijar.
Alhaji Seini Oumarou ya nuna wannan damuwa ce a cikin wani sako da ya isar ga al’umma ta hanyar wata takarda da ke yawo a shafukan sada zumanta na zamani inda a ciki ya ce talakawan da ba su ji ba, ba su gani ba ne za su fi dandana kudar su a cikin wannan mataki na kungiyoyin biyu da suka dauka, don haka ya ce wannan mataki ba komai zai yi ba face kara dagula al’amuran kasar ciki har da na tsaro da ‘yan kasar ke ciki daman.
Kazalika ya ce a ganinsa wannan mataki sam sam bai da ce da wanda zai kawo karshen matsalar da ake ciki ba yanzu, don haka ya ce yana kira da a hau teburin sulhu.
Sai dai wani abin mamaki a cikin wannan sako na shugaban jam’iyyar ta MNSD Nassara babbar jam’iyyar kawancen ta PNDS shi ne, rashin yin Allah wadai da wannan juyin mulki tare da kin yin kiran sakin shugaba Bazoum sai kuma kiran kansa a da tsohon shugaban majalisar dokokin a inda ya saka hannu a kasan takardar.

Na zo ne don na taimaki ‘yan Nijeriya, ba zan cutar da kowa ba – Tinubu

 

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya tabbatar wa ‘yan kasar cewa ya zo mulki ne domin ya taimake su ba domin ya cutar da kowa ba. Shugaban ya bayyana hakan a yayin da yake jawabi ga yan kasar a yammacin Litinin din nan.

Tinubu ya kuma bayyana cewa ya san irin halin da ‘yan Nijeriya ke ciki tun bayan cire tallafin man fetur da gwamnatinsa ta yi. Sai dai ya ce babu wata mafita idan ba dauki wannan mataki ba, yana mai cewa idan da akwai wata hanya ta dabam domin ci-gaba da ya dauke ta, ya kauce wa janye tallafin.

Kawo yanzu dai shugaban ya ce gwamnatinsa ta yi nasarar adana sama da naira tiriliyan daya daga dakatar da biyan tallafin da ta yi.

Jam’iyyar NNPP ta rushe a jihar Katsina, mambobinta sun koma APC

Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda ya karbi bakuncin jagororin jam’iyyar NNPP na kananan hukumomi da jiga-jigan ta na jiha da suka jingine tafiyar jam’iyyar suka koma jam’iyyar APC.
Shugaban jam’iyyar APC na jihar Katsina Alh Sani Aliyu da sauran kusoshin jam’iyyar APC na jiha ne suka karbi wadanda suka bar NNPP suka koma APC karkashin jagorancin Sanata Abdu Yandoma.
Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda, a jawabinsa, ya ce jam’iyyar APC na sane da duk irin gudummuwar da suka ba da har aka samu nasara duk kuwa da irin kalubalen da suka fuskanta daga wasu tsirarun cikinsu.
Gwamnan ya kara da cewa ‘ya’yan jam’iyyar sun yanke shawarar barin NNPP su koma APC ne bisa radin kansu ba tare da sun gindaya wasu sharudda ba. Ya cigaba yana cewa kawai sun duba cancantar ‘yan takarar jam’iyyar APC ne da kuma yadda jam’iyyar ke tsaye kai da fata don ganin jihar Katsina ta cigaba.
A nasa bangaren shugaban jam’iyyar APC na jihar Katsina, Alha Sani Aliyu ya ba da tabbacin cewa daga yanzu sun zama ‘yan gida kuma ana bukatar gudunmuwarsu domin kara inganta jam’iyyar APC da ma jihar Katsina bakidaya.
Shugaban jam’iyyar ya ce Mai Girma Gwamna ya nada mashawarta na musamman kan harkokin jam’iyya da siyasa domin samun daidaito da adalci a tsakanin ‘ya’yan jam’iyya a jihar.
Tun da farko, tsohon shugaban jam’iyyar NNPP na jihar Katsina Hon Sani Liti Yankwani da tsohon jigon jam’iyyar ta NNPP Sanata Abdu Yandoma sun yi godiya bisa ga yadda Gwamnan ya karbe su hannu bibbiyu. Sun sha alwashin ba da dukkanin goyon bayan da ake bukata domin tafiyar siyasa ya kara inganta a jihar musamman a zamanin mulkin jam’iyyar APC.