Sunday, April 5, 2026
Home Blog Page 503

Gwamnan jihar Katsina ya umarci a fitar da hatsi buhu dubu 36 domin raba wa al’ummar jihar kyauta

Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda PhD ya umurci da a fitar buhunan hatsi 36,100 domin raba wa masu karamin karfi su samu saukin rayuwa.
Malam Dikko Umaru Radda ya ce ya umurci kananan hukumomi 34 na jihar da su je su sayi masara domin raba wa mabukata su samu sa’ida a rayuwar yau da kullum.
Ya ce an yanke shawarar yin hakan ne domin mutane su samu saukin rayuwa da cire tallafin man fetur ya jawo musu. Ya ma kara da cewa kowa shaida ne ana cikin mawuyacin hali.
Malam Dikko Umaru Radda ya ce gwamnatin tarayya za ta sayar wa gwamnatoci n jihohi da masara, shinkafa da taki, amma a jihar Katsina, za a raba wa talakawa kyauta.

Kishi: Magidanci ya saki matarsa bayan likita namiji ya karbi haihuwar da za ta yi a Katsina

Magidanci a jihar Katsina ya saki matarsa da suka shafe shekaru 14 da aure saboda an bar wani likita namiji ya karbi haihuwar da matar za ta yi a wani asibiti.
Babbar Darakta ta kungiyar kula da mata da yammata Nana Women and Girls Initiative, Dr Fatima Adamu, ta bayyana hakan a ranar Alhamis.
A cewarta matar wadda mijinta ya sake ta, an ce ta samu matsala mai sarkakiya yayin nakuda wanda hakan ya sa aka garzaya da ita asibiti inda babu wata likita mace a bakin aiki da za ta duba ta.

Yajin aikin da za ku tsunduma haramtacce ne, sakon FG ga kungiyar NLC

Gwamnatin Nijeriya ta sanar da kungiyar kwadago ta kasa NLC cewa yajin aikin da take shirin fadawa ya kan halin matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa haramtacce ne kamar yadda doka ta sanar.
Jaridar Punch ta rawaito cewa kungiyar kwadago ta NLC ta ba gwamnatin tarayya wa’adin kwanaki 7 da ta soke aniyarta kan duk tsare-tsaren da suka jefa talakawa cikin mawuyacin hali ko kuma a fuskanci mummunan yajin aiki a kasar.
Sai dai, babbar Sakatariya a ma’aikatar shari’a ta kasar Mrs B.E Jeddy Agba ta sanar cewa kotun kula da ma’aikata ta kasa ta haramta tafiya wannan yajin aiki mai dangane da cire tallafin man fetur.
Ta ce a ranar 5 ga watan jiya na Yuni, kotu ta dakatar da kungiyar kwadago na tafiya yajin aiki.
Sanarwar ta shawarci kungiyar kwadagon da ta bullo da wasu sabbin dabaru ba wai na yajin aiki ba.

Likitoci za su tsunduma yajin aiki a Ingila kan albashi

Kungiyar kananan likitoci a kasar Ingila ta sanar da tafiya yajin aiki na tsawon kwanaki hudu daga karfe 7na safe a ranar 11 ga watan Agusta zuwa 7 na safe a ranar 15 ga watan na Agusta, 2023.
Wannan yajin aiki dai shi ne na baya-bayan nan da likitoci kanana da kwararri da ya yi sanadiyyar dakatar da ganin marasa lafiya.
 
Kungiyar dai na son gwamnatin kasar ta kara wa mambobinta albashi, bayan da ta yi boren cewa abin da ake biyansu ya yi kadan.
Shugaban kungiyar likitocin Dr Robert Laurenson a cikin wata sanarwa, ya ce abin bai yi musu dadi ba, da suka sanar da yajin aikin karo na biyar cikin lokaci kankani.
Yajin aikin da ya gudana a kasar Ingila dai ya haddasa aka jingine ganin marasa lafiya 819,000. 
A farkon wannan watan dai gwamnatin Ingila ta sanar da karin albashi ga ma’aikatan gwamnati, ciki hada likitoci. Inda ta ce kananan likitoci za su samu kaso 6%.

Wata amarya ta yanke mazakutar angonta a Katsina

Wata mata mai suna Nana da ke da kimanin shekaru 17 ta sa reza ta yanke mazakutar mijinta a daren farko da ya tare bayan ya aure ta a kauyen ‘Yar Kyasuwa na karamar hukumar Kafur ta jihar Katsina.
Majiyar DCL Hausa a kauyen ta ce mijin mai suna Malam Abubakar ya hadu da matar a lokuttan baya, da yake zuwa zawarci, har ya yi nasarar aurenta. Bayan an daura aure ne, ya tare a daren Lahadi wayewar Litinin, ake zargin ta sa reza ta yanke masa mazakuta.
Har ya zuwa lokacin hada wannan labari, ba a kai ga sanin dalilin wannan mata na yanke wa mijinta wannan hukunci ba. Amma dai, mijin na asibitin Kwandala na garin Malumfashi yana karbar magani.
Sai dai bayanan da DCL Hausa ta tattara sun ce yanzu haka matar ta shiga hannun jami’an tsaron ‘yan sanda. Duk da rahotanni sun ce mutumin na jin jiki, bayan wannan aika-aika da ake zargin wannan sabuwar mata ta aikata masa.
Rundunar ‘yan sandan jihar ta hannun kakakinta ASP Aliyu Abubakar, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce yanzu haka ana cigaba da gudana da bincike, da zarar an kammala, za a maka matar kotu.

Nijeriya ta ji kunya a idon duniya – Obasanjo

Tsohon shugaban kasar Nijeriya Olusegun Obasanjo ya ce shekaru 63 da samun ‘yancin kan kasar, har yanzu ba ta yi wani abin a zo a gani ba.
Obasanjo na magana ne a Abuja wajen kaddamar da littafin da tsohon ministan ciniki da masana’antu Olusegun Aganga ya rubuta.
Ya ce a lokacin da kasar ta samu ‘yancin kai, ta zamo wata tauraruwa mai haske. Ya ce idan ana son gyara kasar, dole ne sai shugabanni sun amsa laifin cewa akwai matsala.
“Mun ji kunya, mun sa nahiyar Afrika ta ji kunya, mun sa bakaken fata sun ji kunya sannan mun ji kunya a idon duniya”. In ji Obasanjo.
Tsohon shugaban kasar ya ce kasar ba ta ajiye kowace kwarya a gurbinta. Ya ce son zuciya ya dabaibaye kowa.

‘Yan daba sun kai hari Gidan Rediyon Rock Fm Jalingo, sun saci kayan aiki

Wasu gungun ‘yan daba, sun afka Gidan Rediyon Rock Fm da ke birnin Jalingo na jihar Taraba, in da suka saci kayan aiki masu tarin yawa.
Matasan su sama da dubu biyu, da suka da maza da mata, sun afka shagon wani dan kasuwa, kafin su isa a gidan rediyon. Sai dai bayanan da DCL Hausa ta tattara, sun nuna cewa jami’an tsaro sun yi nasarar hallaka biyu daga cikin wadannan ‘yan daba, sannan sun kama da yawa daga cikinsu.
A cikin wata sanarwa daga Ahmad Umar Gassol, daraktan gudanarwa na gidan rediyon, ya ce bata -garin sun afka ofishin nasu ne a a daren Juma’a 21st Yuli, 2023, in da suka suka saci talabijin 2, kwamfitoci, na’urorin nadar sauti, amsa-kuwwa, janareto da kujeru da sauran kayan amfani a gidan rediyo.
Sanarwar ta ce, ‘yan dabar sun yi kokarin illata babban jami’in gudanarwar gidan rediyon Mr Oloye Ayodele Samuel, amma ya samu kubuta bayan da jami’an tsaron ciki na DSS da sojoji suka kawo dauki, bayan kiran gaggawa da aka yi musu.
Gidan Rediyon Rock Fm, Jalingo wanda shi ne na farko mai zaman kansa a jihar Taraba, dai na a Unguwar Malam Jada da ke cikin birnin Jalingo a jihar Taraba. Jihar dai na da tarihin ayyukan daba da matasa ke aikatawa. Wasu lokuttan, matasan kan farmaki shagunan al’umma, da ake gudanar da kasuwacin yau da kullum.

Daliban wata makarantar Sakandare sun zane malaminsu

Wasu daliban makarantar sakandire su goma a jihar Ogun sun lakada wa wani malaminsu, Kolawole Shonuga dukan tsiya saboda ya hana daya daga cikinsu satar amsa a lokacin da suke rubuta jarabawa.
Majiyar DCLHausa ta jaridar PUNCH ta ce lamarin ya faru ne a ranar Talatar da ta gabata a makarantar Isanbi Comprehensive High School da ke Ilisan-Remo a karamar hukumar Ikenne a jihar.
A cewar jaridar malamin mai suna Shonuga, a yayin da yake tsaron jarabawar a ajin daliban SS 1, ya kama wani matashi mai suna Ashimi Adebanjo mai shekaru 18 da haihuwa, yana satar amsa inda nan take ya kwace takardarsa.

An samu karin jam’iyyar siyasa a Nijeriya

Hukumar zaben Nijeriya INEC ta sanar da rajistar sabuwar jam’iyyar siyasa mai suna  wato Youth Party (YP).
A cikin sanarwar da kwamishinan hukumar Festus Okoye ya fitar a Abuja, ta ce hukumar ta yi hakan ne karkashin sashen doka na 225 (a) na kundin tsarin mulkin 1999 da aka yi wa kwaskwarima.
Ya zuwa yanzu dai, akwai jam’iyyun siyasa 19 a Nijeriya  bayan soke rajistar jam’iyyu 74 da hukumar ta yi a shekarar 2020 da aka samu da gaza wani katabus a zaben 2019.
A zaben 2019 dai, jam’iyyu 91 ne suka shiga aka dama da su a zaben.
Festus Okoye ya tunaso cewa a watan Agustan 2018 aka yi wa YP rajista domin bin umurnin kotu da ta yi hukunci a 2017.

Ganduje ya fara samun turjiya wajen shugabancin jam’iyyar APC

Tsohon Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya fara haduwa da turjiya wajen shugabancin jam’iyyar APC ta kasa kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.
Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kasa mai kula da shiyyar arewa maso yamma Salihu Lukman ya ce maye gurbin Abdullahi Adamu da tsohon Ganduje a shugabancin jam’iyyar kamar kirari ne a daba wa ciki wuka.
Akwai wasu bayanai dai da ke cewa shugaban kasa Bola Tinubu na son Ganduje ya jagoranci jam’iyyar a matakin kasa bayan Abdullahi Adamu ya yi murabus.
A cikin wata sanarwa da Salihu Lukman ya fitar a ranar Alhamis, ta ce ba da sunan Abdullahi Ganduje a matsayin wanda zai rike jam’iyyar har zuwa babban taronta na kasa ba zai haifar wa jam’iyyar da mai ido ba.
Salihu Lukman dai na daga cikin masu fada a ji na jam’iyyar APC a kasa bakidaya.