DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 11, 2026
Home Blog Page 97

Firaministar Italiya ta bukaci gwamnatin Nijeriya ta kare rayukan Kiristoci a kasar

0

Fira-ministar kasar Italiya, Giorgia Meloni, ta bukaci gwamnatin Nijeriya ta kara tsaurara matakan tsaro domin kare Kiristoci a sassa daban-daban na Nijeriya.

A wata sanarwa da ta wallafa a X a ranar Juma’a, Meloni ta bayyana harin da aka kai wa al’ummomin Kirista a Nijeriya a matsayin mummuna kuma abin ƙyama. Ta bukaci hukumomi su dauki matakin gaggawa domin hukunta masu aikata irin wadannan laifuka.

Jaridar Punch ta ruwaito Meloni ta ce ’yancin yin addini hakki ne da ba ya karyewa, tana mai jaddada cewa dole ne gwamnati ta kare dukkan rukunan addinai ba tare da wariya ba.

Haka kuma ta nuna alhini ga iyalan da lamarin ya shafa da al’ummomin da ke fargaba sakamakon hare-haren da ake kai musu.

Wannan furuci ya fito ne a lokacin da ake cikin damuwa kan yadda hare-haren ’yan bindiga, ’yan ta’adda ke kamari kan al’umma a Nijeriya, tare da sace-sace da kai farmaki ga kauyuka.

Sauya shekata zuwa APC daga PDP don amfanin mutanen jihar Taraba ne – Gwamnan Taraba

0

Gwamnan Taraba, Agbu Kefas, ya ce shawarar da ya ɗauka na komawa jam’iyyar APC ta samo asali ne daga bukatar kare muradun mutanensa, ya bayyana haka ne a wani biki na raya al’adun kabilar Margi da aka yi a Jimeta, Jihar Adamawa a ranar Asabar.

Kefas, wanda ya dage bikin shigarsa APC saboda sace ’yan mata a Kebbi, ya ce taron ba na siyasa ba ne, sai dai na ɗaukaka al’adun Margi inda ya bayyana cewa duk wani sabani tsakaninsa da Gwamna Ahmadu Fintiri na Adamawa ya samo asali ne daga matakin da ya ɗauka na sauya sheƙa domin muradun jama’ar Taraba.

A cewarsa, kabilar Margi sun taru ne domin duba tarihinsu da makomarsu, yana mai cewa duk da sabanin siyasa, Fintiri ɗa Margi ne na gari kuma mai son haɗin kai, kuma yana da tabbacin daga ƙarshe zai yarda cewa matakin da ya dauka zai yi amfani ga jama’a.

Gwamnan Oyo, Seyi Makinde, wanda ya halarci taron, ya soki yadda siyasar ƙasar ke sauya salo zuwa tsarin jam’iyya daya, yana mai gargadin cewa hakan ba zai haifar da da mai ido ba kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Gwamnatin jihar Adamawa ta rufe makarantun kwana na gwamnati da masu zaman kansu a fadin jihar

0

Gwamnatin jihar Adamawa ta umarci dukkan makarantun sakandare masu kwana na gwamnati da masu zaman kansu da su daina kwana nan take, saboda barazanar tsaro da ta kai ga sace dalibai a jihohin Neja da Kebbi.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, kwamishinan ilimi na jihar, Dr Umar Pella ya ce Gwamna Ahmadu Fintiri ya dauki matakin ne domin kare rayuwar dalibai.

Sanarwar ta bayyana cewa makarantun kwana sun zama babban wurin da ’yan ta’adda ke kai hari, don haka dukkan makarantu za su koma tsarin jeka-ka-dawo ba tare da bata lokaci ba. An umarci dukkan shugabannin makarantu da masu makarantu su aiwatar da wannan sauyi cikin gaggawa.

Hakan na faruwa ne a lokacin da jihohi da dama irin su Kwara, Filato, Katsina da Neja suka rufe makarantu saboda tashin hankali, yayin da Taraba ma ta umurci daina kwana. A lokaci guda.

Babu abin da ke tada mun hankali irin matsalolin tsaron da ya addabi Nijeriya – Shugaba Tinubu

0

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya ce matsalar tsaro ita ce babbar damuwar Nijeriya, musamman Arewacin ƙasar, yana mai cewa dole a hanzarta dawo da zaman lafiya da haɗin kai.

Da yake magana a Kaduna ta bakin Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, a bikin cika shekara 25 na kungiyar tuntuba ta Arewacin Nijeriya, ACF, ya ce gwamnati na aiki da hanzari don murkushe ’yan ta’adda da ’yan bindiga da ke lalata tattalin arziƙi da ilimi.

A cewarsa, babu abin da ke tayar masa da hankali irin matsalolin tsaro musamman a Arewacin kasar inda ya ce ba za a ci-gaba ba matukar wani bangare na kasar na cikin matsala kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Tinubu ya ce gwamnatinsa ta gaji matsaloli masu tsanani amma tana tunkararsu, yana fatan Arewacin Nijeriya za ta farfaɗo tare da manyan ayyuka kamar titin Abuja–Kaduna–Kano da kuma rijiyar mai ta Kolmani da ake sa ran za su farfado da tattalin arziƙi.

Hakazalika, Tinubu ya yaba wa ACF bisa zama murya ɗaya ta Arewa, yana gargadin cewa yankin ba zai ci-gaba ba idan shugabanni suka kasa kare marasa ƙarfi, musamman yayin da jama’a ke fama da tsoro da yunwa.

Trump na Amurka ya sake aibata Nijeriya inda ya zargi gwamnati da gazawa a harkar tsaro

0

Shugaban Amurka Donald Trump ya sake sukar Nijeriya, inda ya kira ta da “abin kunya” tare da zargin gwamnati da kasa dakile kashe-kashen da ake yi wa ’yan ƙasa. Ya ce ana kashe mutane dubbai ba tare da wani mataki ba, inda ya zargi gwamnati da gazawa.

Kalaman Trump sun zo ne bayan ya sake saka Nijeriya a jerin ƙasashen da ake kula da su na musamman, yayin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta tura mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, zuwa Amurka don gabatar da bayanai kan matakan tsaro.

Tun bayan kalaman Trump, hare-haren sun ƙaru a yankuna daban-daban inda ‘yan bindiga suka halaka babban hafsan soja a Borno, yayin da barayin daji suka sace dalibai mata 25 a Kebbi tare da halaka mataimakin shugaban makarantar.

A ciki ƙarin hare-haren, ’yan bindiga sun kutsa coci a Eruku, Kwara, sannan suka sace fiye da ɗalibai 300 da malamai 12 daga makarantar St Mary’s a Papiri, Jihar Neja, abin da ya kara nuna tsananin tabarbarewar tsaro a ƙasar kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnatin Nijeriya ta musanta jita-jitar rufe makarantu a fadin kasa

0

Ma’aikatar Ilimi ta Nijeriya ta musanta wani saƙon da yake yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa an ba da umarnin rufe makarantu a fadin ƙasar daga 24 ga watan Nuwamba, 2025.

A cewar sanarwar da mai magana da yawun ma’aikatar, Folasade Boriowo, ta fitar a ranar Asabar, ta ce labarin ba gaskiya ba ne, kuma ba daga gwamnatin tarayya ko ta jiha, ko wata hukuma ta tsaro da aka amince da ita yake ba.

Sanarwar ta bukaci jama’a su dogara kacokan ga bayanai daga ingantattun hanyoyin gwamnati kawai, tare da gargaɗin cewa duk wani saƙo daga majiyoyi marasa tushe ya kamata a yi watsi da su domin hana yaɗa bayanan ƙarya.

Ma’aikatar ta ce bayanai daga gwamnatin tarayya, ma’aikatar ilimi ta tarayya, gwamnatocin jihohi da hukumomin tsaro ne za su iya zama a hukumance kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Sanarwar ta zo ne kwana daya bayan gwamnatin tarayya ta rufe manyan makarantu 41 da ke cikin yankunan da ke fuskantar tashin hankali, sannan wasu jihohi kamar Kwara, Filato, Katsina da Neja suma sun dakatar da karatu saboda matsalar tsaro.

A baya-bayan nan ma, gwamnan Taraba, Agbu Kefas, ya umarci duk makarantu su daina kwana da ɗalibai a makarantu har sai yadda hali ya ba da.

Gwamnatin jihar Neja ta sanar da rufe daukacin makarantun firamare da sakandare na jihar

0

Gwamnatin Jihar Neja ta ce ta rufe dukkan makarantun gwamnati da masu zaman kansu na firamare da sakandare bayan sace daliban makarantar St. Mary’s Catholic da ke Papiri a Agwara.

Wannan na cikin sanarwar da aka fitar bayan taron tsaro da Gwamna Umar Bago ya yi da shugabannin hukumomin tsaro, kamar yadda mai magana da yawunsa, Bologi Ibrahim, ya bayyana.

Gwamnan ya ce makarantun boko, Islamiyoyi da kwalejojin tarayya ciki har da FGC Minna, duk sun shiga jerin makarantun da aka rufe, sai dai matakin bai shafi manyan makarantu ba face waɗanda ke yankunan da aka ayyana masu hadari a Neja ta Arewa da Gabas.

Bago ya kuma jaddada cewa gwamnati na aiki tare da hukumomin tsaro wajen ceto daliban, inda ake ci-gaba da lissafi domin tantance adadin waɗanda aka sace.

Gwamnatin jihar Kebbi ta bukaci addu’o’i daga al’umma domin dawo da daliban da aka sace cikin aminci

0

Gwamnatin jihar Kebbi ta bukaci al’umma su tsananta addu’o’i domin ceto ɗaliban GGCSS Maga da ’yan ta’adda suka sace, kamar yadda kwamishinan harkokin addini, Sani Aliyu, ya bayyana a Birnin Kebbi.

jaridar Punch ta ruwaito kwamishinan ya ce halin da ake ciki ya zarce ƙarfin ɗan adam, don haka ana buƙatar cikakken taimakon Allah duk da ƙoƙarin gwamnati da jami’an tsaro.

Aliyu ya roƙi malamai, limamai, da masu ibada su rika yin qunut da addu’o’i a cikin sallolinsu, musamman a cikin dare. Haka kuma ya bukaci fastoci da su ware lokuta a cikin wa’azozinsu da taron ibada domin roƙon zaman lafiya a Kebbi da Nijeriya gaba ɗaya.

Hakazalika, kwamishinan ya kuma yi kira ga jama’a su kasance masu lura, su nisanci hulɗa da miyagu, tare da tura duk wani muhimmin bayani ga jami’an tsaro domin taimakawa wajen gano masu laifi da kuma ceto ɗaliban cikin gaggawa.

Gwamnatin Amurka na aiki da ta Nijeriya domin kawo karshen musguna ma Kiristoci da ‘yan ta’adda ke yi a kasar – Sakataren tsaron Amurka

0

Gwamnatin Amurka ta ce gwamnatin shugaba Donald Trump na aiki tare da gwamnatin Nijeriya domin kawo ƙarshen abin da ta kira zaluntar Kiristoci da ’yan tada kayar baya ke yi a kasar, kamar yadda sakataren tsaron Amurka Pete Hegseth ya bayyana.

Hegseth ya bayyana haka ne a shafinsa na X da Facebook bayan ganawarsa da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, da tawagarsa a Amurka.

A cewar sakataren, sun tattauna kan tashin hankaulan da ke addabar Kiristoci a Nijeriya, inda ya ce gwamnatin Trump na kokari sosai don dakile hare-haren da ake danganta wa ’da ‘yan tada kayar baya.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Ribadu ya jagoranci tawaga mai ƙarfi zuwa Amurka domin tattaunawa kan zargin zaluntar Kiristoci a Nijeriya, inda kuma kafin haka shugaba Trump ya sanya Nijeriya cikin jerin ƙasashen da ake kallon suna da matsalar tauye ’yancin addini.

Binciken kwakkwafi da ake ne ya hana a gurfanar da wadanda ake zargi da daukar nauyin ta’addanci – Gwamnatin Nijeriya

0

Ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris ya ce gwamnati ba ta gurfanar da waɗanda ake zargi da ɗaukar nauyin ta’addanci ba saakamakon binciken yana da sarkakiya, ba kuma abin da za a hanzarta shi ba ne duk da matsin lambar jama’a.

Jaridar Punch ta ruwaito Idris ya ce, ba wai da an samu jerin sunaye ne kawai za a garzaya kotu ba, yana mai cewa dole a tattara bayanai sosai kafin daukar mataki. Wannan na zuwa ne yayin da ake ƙara zargin gwamnati da rashin gaskiya kan yawaitar hare-haren tsaro.

Ministan ya ce gwamnatin Tinubu na aiki tukuru wajen murƙushe ta’addanci, inda ya bayyana cewa tun daga Mayu 2023 sama da ’yan ta’adda 13,500 aka hallaka, fiye da 17,000 kuma aka kama, wasu ma na fuskantar shari’a yanzu.