Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya umurci Ministan Tsaron kasar, Badaru Abubakar, da ya tashi kai tsaye zuwa jihar Neja domin jagorantar aikin ceto daliban makarantar St. Mary’s Catholic School da ‘yan bindiga suka sace a yankin Papiri, ƙaramar hukumar Agwara.
Umarnin na zuwa ne sa’o’i bayan da kungiyar kiristoci ta Njeriya CAN reshen jihar Neja ta tabbatar da sace ɗalibai 303 da malamai 12 a makarantar, lamarin da ya kara tayar da hankalin al’umma a fadin ƙasar saboda ƙara yawan hare-haren da ake kaiwa makarantun Arewa.
Yawan hare-hare kan makarantun ya sa gwamnatin tarayyar kasar ta umurci da a rufe makarantun sakandare mallakinta sama da 40 a fadin kasar. Yayin da gwamnatocin jihohin Katsina da Plateau suka sanar da rufe nasu makarantun firamare da sakandare.
A baya-bayan nan, Shugaba Tinubu ya tura Ministan Ƙasa a ma’aikatar tsaro, Bello Matawalle, zuwa jihar Kebbi domin ganin an ceto dalibai 24 mata na Government Girls’ Comprehensive Secondary School, Maga, da aka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Danko Wasagu.
Masu sharhi na ganin cewa tura ministoci biyu manya zuwa yankuna biyu daban-daban a lokaci guda na nuna yadda matsalar tsaro ta kara kamari, tare da bukatar sabbin dabaru da matakan gaggawa. Yanzu idanun jama’a na kan yadda gwamnati za ta gudanar da aikin ceto da tabbatar da tsaro a makarantun Arewa maso yamma da tsakiya.
Shugaba Tinubu ya tura Minista Badaru zuwa Neja don ganin an ceto daliban da aka sace
Majalisar dinkin duniya ta yi Allah-wadai da sace dalibai a jihar Neja
Majalisar dinkin duniya ta yi kakkausar suka kan sace ɗalibai da malamai daga makarantar St. Mary’s a Papiri, jihar Neja, inda ta ce harin abin takaici ne kuma makarantu wajibi ne su kasance wuraren kariya ga ɗalibai.
A cewar kungiyar Kiristocin Nijeriya, CAN, ’yan bindigar sun sace ɗalibai 215 da malamai 12, lamarin da ya zo kwanaki bayan sace ɗalibai 25 da kashe malami a Maga, da ke jihar Kebbi kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
MDD ta ce dole a mai da hankali kan ganin an dawo da yaran cikin gaggawa, ta kuma jaddada bukatar aiwatar da yarjejeniyar kariyar makarantu, yayin da gwamnatin Nijeriya ta rufe makarantun Unity 41 domin guje wa sake faruwar irin wadannan hare-haren.
Gwamnatin jihar Taraba ta umurci rufe makarantun kwana a fadin jihar
Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, ya umarci duk makarantun sakandare na gwamnati da masu zaman kansu da dalibai su daina kwana a makarantu da dalibai saboda fargabar tsaro a faɗin ƙasar.
Sanarwar hakan ta fito ne daga kwamishinar ilimi ta jihar, Dr Augustina Godwin, wadda ta ce garkuwa da ɗalibai a Kebbi da Neja ta sanya daliban makarantun kwana zama cikin hadari, don haka gwamnati ta umarci komawa tsarin jeka-ka-dawo har sai tsaro ya inganta kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Umarnin ya zo ne a rana guda bayan ’yan ta’adda sun sace dalibai daga makarantar St. Mary a Papiri, Neja, yayin da kusan mako guda da aka yi garkuwa da dalibai 25 a Maga, jihar Kebbi. Lamarin da ya ƙara nuna tabarbarewar tsaro a makarantun Arewacin Nijeriya.
Gwamnatin Katsina ta rufe duk makarantun sakandare da firamare saboda barazanar tsaro
Gwamnatin Jihar Katsina ta bada umarnin rufe dukkan makarantu sakamakon tsananin barazanar tsaro da ake fuskanta a arewacin kasar, musamman bayan sace dalibai a Jahohin Neja da Kebbi. Kwamishinan Ilmi na Jihar ya tabbatar da hakan, inda ya ce matakin ya zama dole domin kare rayuwar dalibai da malamai.
Wannan batu ya yi karfi musamman idan aka yi la’akari da wani sabon rahoto da ya nuna cewa sama da yara 300,000 a Katsina ba sa zuwa makaranta saboda tsaro mai rauni.
DCL Hausa ta ruwaito cewa gwamnati na duba yiwuwar sake fasalin tsaron makarantun jihar, yayin da ake cigaba da kai hare-hare a makarantu daban-daban a arewacin kasar. Masu sharhi dai na ganin cewa rufe makarantu ka iya kare rayuka, amma hadarin da yake haifarwa ga makomar ilimi ya fi tsanani idan ba a dauki matakan gaggawa ba.
Gwamnatin Bauchi ta dakatar da wasu manyan ma’aikatan gwamnati a jihar
Hukumar Kula da Ma’aikatan Gwamnati ta Jihar Bauchi ta dauki matakin ladabtar da wasu manyan ma’aikata huɗu saboda gagarumin cin amanar aiki a yayin gudanar da ayyukansu.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Mista Saleh Umar, ya fitar wa manema labarai a Bauchi ranar Juma’a.
Umar ya ce wannan mataki da aka dauka yayin zaman majalisar hukumar, na daga cikin ƙoƙarin da ake yi domin tsaftace harkokin aikin gwamnati a jihar.
Ya bayyana sunayen ma’aikatan da abin ya shafa kamar haka: Garba Hussaini, Darakta (Ilimi) kuma tsohon Provost; Haruna Umar, Mataimakin Darakta (Gudanarwa da Harkokin Ma’aikata); Umar Yusuf, Babban Jami’in Gudanarwa – Bursar; da Mohammed Usman, – Cashier; dukkaninsu na aiki ne a Kwalejin Fasahar Kimiyyar Lafiya ta Bill and Melinda Gates da ke Karamar Hukumar Ningi.
Kotu ta yi hukunci ga mutumin da aka samu da laifin satar tiyar wake a jihar Adamawa
Wata kotu a karamar hukumar Shelleng ta jihar Adamawa ta yanke wa wani matashi mai shekaru 31, Iliya Abdullahi hukuncin daurin shekara ɗaya a gidan yari saboda satar mudu ɗaya na wake.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an taɓa kama Abdullahi a baya, aka gurfanar da shi a gaban Kotun Shelleng 2, inda aka yanke masa hukuncin shekaru biyu a bisa laifin da ya aikata, bisa tanadin Sashe na 277 na Dokar Penal Code.
Wani kauye karkashin Abuja da har yanzu bai da makarantar boko da lantarki
Bwaje, ƙauye ne na manoma da ke cikin mazabar Gurdi a Karamar Hukumar Abaji ta Babban Birnin Tarayyar Nijeriya, Abuja.
A cewar basaraken gargajiya na yankin, Malam Aliyu Isah, al’ummar sun shafe fiye da shekaru 100 da kafuwa a Cesar rahoton jaridar Daily Trust.
Tun waɗancan shekaru zuwa yau, shugaban ya ce ba su taɓa jin kamshin wani aiki daga gwamnati ba, ko ta Abuja, ko kuma ta Karamar Hukumar Abaji.
A cewarsa, al’ummar ba su da makaranta, cibiyar lafiya, hanya ko rijiyar burtsatse da za su kira ta su, sai dai idan sun yi tafiya zuwa wasu ƙauyuka.
Har ma idan lokacin zabe ya yi, shugaban ya ce dole sai sun yi tafiya zuwa makwabtan ƙauyuka domin kada kuri’a, domin ma har rumfar zabe ba a tanadar musu ba.
Matsayin da nake da shi a kungiyar dattawan Yammacin Afrika ya sa na janye daga harkokin siyasa – Jonathan
Tsohon Shugaban Nijeriya, Goodluck Jonathan, ya bayyana cewa zama memba a Dandalin Dattawan Afrika ta Yamma (WAEF) shi ne babban dalilin da ya hana shi komawa siyasa kai tsaye ko mara baya ga kowace jam’iyya.
A cewar Jonathan, yayin taron cika shekaru 10 da kafa Goodluck Jonathan Foundation (GJF) da aka gudanar a Abuja, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito, dokokin dandalin na WAEF sun wajabta wa membobinsu su kasance masu ajiye ra’ayin siyasa ko bangaranci a gefe.
Jonathan ya bayyana WAEF a matsayin mai tsarin da ke kai ziyara ƙasashe a lokacin zaɓe domin shawo kan duk wani alamar tashin hankali tun kafin ya rikide ya zama rikici baki ɗaya.
Ya kuma yi tir da abin da ya kira “tashanci a siyasar Nijeriya”, yana kira ga ’yan siyasa su gudanar da harkokinsu cikin ladabi, hikima da ɗa’a domin kare mutuncin ƙasa da dimokuraɗiyya.
‘Yan bindiga sun kuma sace dalibai a jihar Neja
Rahotannin da jaridar Daily Trust ta samu sun ce barayin daji sun yi garkuwa da dalibai da ma’aikatan da har ya zuwa ynzu ba a tantance adadinsu a jihar Neja.
Lamarin ya faru ne a makarantar darikar Katilika ta St. Mary’s School, da ke unguwar Papiri a ƙaramar hukumar Agwara ta jihar Neja.
Gwamnatin Neja ta yi Allah-wadai da sace daliban Agwara, ta ce an bude makarantar ne ba tare da izini ba
Gwamnatin Jihar Neja ta bayyana takaicin ta kan sace wasu daliban makarantar St. Mary’s da ke yankin Papiri a ƙaramar hukumar Agwara, lamarin da ya faru duk da gargadin tsaro da aka riga aka bayar a yankin. Har yanzu hukumomin tsaro ba su tabbatar da adadin waɗanda aka sace ba, yayin da bincike da kokarin ceto su ke ci gaba.
A cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Neja Abubakar Usman ya sanya wa hannu, gwamnatin jihar ta ce tun kafin faruwar lamarin ta samu rahotannin ƙarin barazanar tsaro a wasu sassan Neja ta Arewa, wanda ya sa ta dakatar da ayyukan gine-gine tare da rufe dukkan makarantun kwana na yankin. Sai dai duk da wannan umarni, makarantar St. Mary’s ta buɗe ba tare da sanarwa ko neman izinin gwamnati ba, abin da ya jefa dalibai da malamai cikin haɗari.
