Sunday, April 5, 2026
HomeBabban LabarinmuPDP za ta tattauna da gwamnoninta kan sauya shekar da 'ya'yanta ke...

PDP za ta tattauna da gwamnoninta kan sauya shekar da ‘ya’yanta ke yi

Kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) na jam’iyyar PDP tare da kungiyar gwamnonin jam’iyyar sun shirya wani muhimmin taro a ranar 11 ga watan Mayu, domin tunkarar kalubalen da ke barazana ga makomar jam’iyyar, musamman abun da ya shafi yawaitar sauya shekar da ke ci gaba da addabar jam’iyyar.

Wani amintaccen mamba daga cikin kwamitin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ne ya tabbatar wa jaridar PUNCH cewa shugabannin jam’iyyar da gwamnonin PDP za su gana a ranar 11 ga watan Mayu domin tattauna matsalolin da ke damun jam’iyyar.

Majiyar ta bayyana cewa taron zai fi mayar da hankali ne kan tsara dabarun dakile ci gaba da ficewar wasu jiga-jigan ‘ya’yan jam’iyyar, da warware matsalar da ta shafi kujerar Sakataren Jam’iyyar na Kasa, da kuma wasu muhimman batutuwa da ke ci gaba da addabar jam’iyyar a fadin kasar.

Ana kallon wannan taro a matsayin wani mataki na sake farfado da jam’iyyar tare da dunkulewa domin tinkarar zaben 2027 da ke tafe.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata