Thursday, April 9, 2026
HomeUncategorizedRabuwar aurena da mai ɗakina Melinda shi ne babban kuskure mafi girma...

Rabuwar aurena da mai ɗakina Melinda shi ne babban kuskure mafi girma da na tafka a rayuwata – Inji Attajirin Duniya Bill Gates

 

Bill and Melinda

Da yake bayani a wata hira da jaridar Times a London, dan kasuwan dan kasar Amurka mai shekaru 69 ya bayyana cewa akwai kura kurai da ya yi a rayuwarsa amma kuskure mafi girma shine rabuwa da matarsa Melinda da suka yi shekaru kusan 27 suna tare

Attajirin Bill da tsohuwar matarsa Melinda sun yi aure a shekarar 1994 kuma suna da yara uku – Jennifer mai shekaru 28,da Rory mai shekaru 25,sai Phoebe mai 22.

Ma’auratan, sun ba da sanarwar rabuwar su a hukumance a watan Mayu na shekarar 2021, wanda a baya aka yi ta zargin sun rabu dama kafin sanarda rabuwar ta su a hukumance.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata