DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 11, 2026
HomeWasanniReal Madrid ba za ta halarci bikin bayar da kyautar Ballon d’Or...

Real Madrid ba za ta halarci bikin bayar da kyautar Ballon d’Or na bana ba

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta bayyana cewa ba za ta halarci bikin bayar da lambar girmamawa ta Ballon d’Or da za a gudanar a daren yau ba.

Wannan matakin ya jawo cece-kuce a duniya, duba da yadda bikin ke zaman ɗaya daga cikin manyan bukukuwan kwallon kafa da ake yi a duk shekara.

Rahotanni daga The Athletic sun tabbatar da cewa shugaban Real Madrid, Florentino Pérez, ya sanar da jami’an da ke shirya taron cewa kungiyar za ta kauracewa wannan bikin.

Duk da cewa ba a bayyana cikakken dalilin yanke wannan shawarar ba, masana harkokin wasanni na ganin hakan na da alaka da yadda aka kada kuri’u zaben na Ballon d’Or, wanda a lokuta da dama ke janyo martini daga bangarori.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata