Rikicin da jam’iyyar PDP ke ciki APC ce ta kirkireshi-Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana haka ne a ranar Larabar da ta gabata inda ya ce rikicin da jam’iyyar PDP ke ciki jam’iyyar APC ce ta kirkira.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake karbar mambobin kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP a gidan gwamnati da ke Bauchi.
Yace duk wani kalubalen da jam’iyyar PDP ke ciki suna kokarin shawo kansa domin itace kadai keda gogewa ta iya shugabanci a kasar nan
Ya kara da cewa APC naso ta ga PDP ta shiga rudani kuma itace ke haddasawa,da kuma neman bayanan abinda ke faruwa a cikin jam’iyyar.
A cewar sa ko Wike da ke aiki cikin gwamnatin APC yana PDP, yana taka rawar gani sosai wajen gudanar da abubuwa domin APC basu da gagaggun mutane irin nasu
Gwamna Mohammed ya kuma yarda da kalubalen da Wike ke da shi kuma ya danganta hakan da rikicin da jam’iyyar adawa ke kara hura wutar,amma suna kokarin shawo kan lamarin
Ya kara da cewa babban abin da PDP ta fi mayar da hankali a kai shi ne hada kan jam’iyyar don karbar ragamar mulki a 2027 da tabbatar da ingantaccen shugabanci.

.jpeg)