Ministan Kudi kuma Mai Kula da Tattalin Arzikin Nijeriya, Wale Edun, ya bayyana cewa tattalin arzikin kasar na cikin wani mawuyacin hali, yayin da kasashen duniya ke fuskantar tasirin rikicin da ke gudana a Gabas ta Tsakiya.
Wata sanarwa daga hadimin ministan kan yada labarai da sadarwa, Dr Ogho Okiti, ta bayyana cewa wannan girgizar na zuwa ne bayan sabbin gyare-gyaren tattalin arziki da aka yi domin shimfida tubalin da zai taimaka wajen fitar da miliyoyin mutane daga talauci.
Asusun Lamuni na Duniya IMF, a wata sanarwa da ya fitar gabanin taron shekarar 2026 da ya fara a ranar Litinin 13 ga Afrilu, ya ce yana sa ran kasashen da suka fuskanci matsalar rashin daidaiton kudaden waje za su bukaci tallafin gaggawa har dala biliyan 50.
Fiye da wakilai 1,000 daga kasashe 190 ne ake sa ran za su hallara a birnin Washington domin halartar taron na World Bank da IMF.
An sanya wa taken taron na bana “Karfafa Daidaito da Inganta Daidaitaccen Ci Gaba”, wanda ke zuwa a daidai lokacin da ake fuskantar sabon kalubale na tattalin arziki sakamakon yakin Gabas ta Tsakiya.
Shugaban Amurka Donald Trump ya umarci rundunar ruwan Amurka a ranar Lahadi da ta toshe muhimmiyar hanyar ruwa ta Tekun Gulf wato mashigar Strait of Hormuz, sakamakon rashin amincewar Iran na janye shirin nukiliyarta bayan tattaunawar sulhu ta lalace ba tare da cimma matsaya ba.
A martaninta, rundunar juyin juya halin Iran ta gargadi cewa tana da cikakken iko kan zirga-zirgar jiragen ruwa a wannan muhimmiyar hanya, kuma za ta kama duk wani abokin gaba da ya yi yunkurin kalubalantar ta.
Babbar daraktar IMF, Kristalina Georgieva, ta gargadi cewa asusun zai rage hasashen ci gaban tattalin arzikin duniya da zarar an fara taron daga ranar 13 ga Afrilu.
Ta danganta hakan da “illolin tashin farashin makamashi, tangardar samar da kayayyaki, da lalacewar ababen more rayuwa” sakamakon yakin.
Taron na IMF da Bankin Duniya na shekarar 2026 na gudana ne a lokacin da duniya ke cikin babban rashin tabbas.
A cewar Minista Edun, wanda kuma shi ne shugaban tawagar Nijeriya a taron, ya ce a wannan muhimmin lokaci na sauyin tattalin arziki, wannan girgiza na kara dagula hauhawar farashin mai, tsadar abinci da sauran matsin tattalin arziki, wanda ke kara nauyi ga gidaje da ‘yan kasuwa.
Rikicin Amurka da Isra’ila da Iran ya haifar da babbar girgiza daga waje, inda ya kawo tangarda a kasuwannin makamashi, ya tsaurara sharuddan hada-hadar kudi a duniya, tare da kara matsin hauhawar farashi a kasashe masu karfi da masu tasowa in ji gidan talabijin na Channels.
A Nijeriya, Edun ya ce gwamnati na kokarin hanzarta bunkasar tattalin arziki duk da kalubalen da ke tattare da tasirin waje da kuma matsin farashi a cikin gida.
Sai dai ya ce gwamnati na da kudurin tabbatar da daidaiton tattalin arziki da kuma jawo zuba jari domin fitar da miliyoyin mutane daga talauci.
Farashin danyen man fetur na Nijeriya ya samu gagarumin sauyi tun bayan fara rikicin, inda ya karu tsakanin kashi 35 zuwa sama da kashi 50, musamman sakamakon tangardar da aka samu a mashigar Strait of Hormuz.
Farashin man Bonny Light ya tashi daga kusan dala 70 zuwa 73 a kowace ganga zuwa sama da dala 110 zuwa 120.
Ya ce, a matsayin Nijeriya na kasa mai samar da mai, tsawon lokacin rikicin na iya kara kudaden shiga daga waje da kuma kudaden shiga na gwamnati, amma wannan girgiza na zuwa ne a lokacin da ake kokarin karfafa tattalin arziki.
Ministan ya bayyana hanyoyi uku muhimmai da rikicin ke iya kawo barazana ga tattalin arzikin Nijeriya.
Farashin fetur, dizal da gas ya fara sauyawa sakamakon canjin kasuwannin makamashi na duniya, lamarin da ke da tasiri kai tsaye kan rayuwar ‘yan Nijeriya.
Farashin man fetur ya karu da sama da kashi 50, daga kusan N890 zuwa N900 zuwa tsakanin N1260 zuwa N1330, yayin da farashin dizal ya karu da sama da kashi 70, daga N1,100 zuwa kusan N1,550.
