Tuesday, April 7, 2026
HomeBabban LabarinmuRikicin PDP ya kara rincabewa bayan da Wike ya janye daga kokarin...

Rikicin PDP ya kara rincabewa bayan da Wike ya janye daga kokarin sulhu da ake yi

Rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar PDP ya kara kamari, yayin da ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya fice daga yarjejeniyar sulhu ta cikin gida da aka cimma a jam’iyyar adawa.

Wike ya zargi gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, kan matsalolin da suka dabaibaye jam’iyyar PDP, yana mai jaddada cewa shi ne ya jawo wannan matsalar.

A cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu, tsohon gwamnan na Rivers ya zargi shugabannin jam’iyyar da suka hada da gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah da cin amana, da rashin gaskiya, da kuma take yarjejeniyar da aka yi da shi.

Ministan ya sha alwashin ci gaba da jan zare har sai ya samu adalci a jam’iyyar.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata