Monday, April 6, 2026
HomeUncategorizedRundunar sojin Nijeriya ta ce sojoji sunyi ajalin ‘yan ta’adda 358 tare...

Rundunar sojin Nijeriya ta ce sojoji sunyi ajalin ‘yan ta’adda 358 tare da kama 431 a cikin watan Janairun 2025

CDS Christopher Musa

Daraktan yada labarai na rundunar Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, inda ya ce rundunar na ci gaba kai hare hare ga ‘yan ta’adda da masu tada kayar baya a fadin kasar.

A cewar sanarwar sojojin sun kama mutane 59 da suka aikata laifin satar mai tare da ceto mutane 249 da aka yi garkuwa da su.

Sanarwar ta kuma kara da cewa sojojin sun kwato makamai 370 da alburusai 4,972 da suka hada da bindigogi kirar AK47 guda 105, bindigogi kirar gida guda 25, da karin wasu bindigogin guda 32, da kuma albarusai 3,066.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata