Tuesday, April 7, 2026
HomeUncategorizedRundunar sojin saman Nijeriya ta halaka 'yan bindiga 20, tare da lalata...

Rundunar sojin saman Nijeriya ta halaka ‘yan bindiga 20, tare da lalata maboyar su a jihar Katsina

 

Rundunar sojin saman Nijeriya ta bayyana cewa, wasu hare-hare ta sama da jami’an tsaro suka kai a jihar Katsina sun lalata maboyar ‘yan ta’adda a dajin Unguwar Goga da ke unguwar Ruwan Godiya a karamar hukumar Faskari ta jihar.

Rundunar sojin karkashin Operation Fansar Yamma ta kai harinne da sanyin safiyar ranar Alhamis, a sansanonin ‘yan bindiga guda biyu, Gero Alhaji da kuma Alhaji Riga.

A wata sanarwa da mataimakin daraktan yada labarai da hulda da jama’a na rundunar sojin saman Nijeriya, Kaftin Kabiru Ali ya fitar a daren Juma’a, ta ce harin da jiragen suka kai sun yi nasarar halaka ‘yan bindiga sama da 20, tare da samun gagarumar nasara a kansu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata