Monday, April 6, 2026
HomeUncategorizedRundunar 'yan sandan jihar Plateau ta musanta fashewar wani abu mai hatsari...

Rundunar ‘yan sandan jihar Plateau ta musanta fashewar wani abu mai hatsari a Kasuwar Terminus dake yankin Jos ta arewa.

Mai magana da yawun rundunar, Alfred Alabo wanda ya sanar da hakan a cikin wani bayani da ya fitar, ya ce sun sa mu rahoton cewa, an dasa wani abin fashewa a cikin rame a yankin, abin da ya razana al’umma. 
Alabo ya ce ba su yi hanzari ba Kwamishinan yan sanda na jihar ya tura jami’an da ke kwance bam domin bincike, kuma babu wani abin fashewa da suka gano a wurin. 
Jaridar Punch ta ruwaito cewa wata fashewa mai karfi ta faru a birnin Jos na jihar Plateau da safiyar yau Talata, lamarin da ya jefa al’umma cikin fargaba.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata