DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, April 12, 2026
HomeUncategorizedSarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero ya sanar da soke hawan...

Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero ya sanar da soke hawan Sallah

Alhaji Aminu Ado Bayero 

Mai martaba Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya sanar da soke hawan Sallah da aka saba yi duk shekara, kamar yadda aka tsara gudanarwa a baya.

Sarkin ya bayyana hakan ne, a cikin wani takaitaccen faifan bidiyo da ya fitar a daren Laraba, inda ya bayyana dalilan da suka sanya aka dakatar da shirin hawan Sallar.

Ta cikin faifan bidiyon, sarki Aminu, ya bayyana cewa ya bada umarnin soke hawan ne sakamakon kokarin da malaman addinin musulunci da kuma dattawa suka yi wajen ganin an samu zaman lafiya, inda ya bukaci mazauna birnin Kano da su yi amfani da lokacin bikin Sallar wajen ziyartar yan uwa da abokan arziki tare da samun damar halartar bikin Sallah.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata