Wednesday, April 8, 2026
HomeKetareSaudia Airlines ta rage kuɗin tikitin jirage da kashi 50% ga masu...

Saudia Airlines ta rage kuɗin tikitin jirage da kashi 50% ga masu zuwa Umrah

Kamfanin jiragen sama na Saudia Airlines ya sanar da rangwamen kuɗin tikitin jiragen sama da kashi 50 cikin 100 ga matafiyan Umrah daga ƙasashe daban-daban na duniya

Rangwamen zai shafi tikitin Economy da kuma Business Class, inda ake buƙatar a kammala yin ajiyar kujeru kafin ranar 31 ga watan Agusta, 2025, yayin da za’a fara jigilar maniyata tsakanin 1 ga watan Satumba zuwa 10 ga Disambar, 2025.

Hakan ya shafi matafiya daga Nahiyar Turai, Asiya, Afirka da Arewacin Amurka, inda jirage za su sauka a manyan filayen jiragen Jeddah da Madina domin sauke farali.

Hukumar ta Saudia ta ce ana iya yin rajista ta hanyar shafin intanet, manhajar waya, ko kuma ofisoshin hada-hada da aka amince da su.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata