Sunday, April 5, 2026
HomeBabban LabarinmuSaura kiris PDP ta daidaice, shi ya sa mambobinta ke tururuwar komawa...

Saura kiris PDP ta daidaice, shi ya sa mambobinta ke tururuwar komawa APC – Ganduje

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce jam’iyyar adawa ta PDP ta shiga zullumi da rashin tabbas sakamakon irin nasarorin da APC ke samu.

Da yake jawabi a taron kolin APC da aka gudanar a fadar shugaban kasa, Ganduje ya ce APC za ta lashe zaben da ke tafe a babban birnin tarayya (FCT) saboda kwarewar siyasa da karfinta.

Ya ce rikice-rikice da sauya sheka da ke damun PDP ya sanya mambobinta da dama ke komawa APC.

Ganduje ya kara da cewa APC na da gwamnonin jihohi 22 daga cikin 36, kuma wani gwamna na shirin sauya sheka zuwa jam’iyyar.

Ya ce nasarorin APC a zabukan da suka biyo bayan na 2023 na nuna hasashen nasararta a 2027.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata