Monday, April 6, 2026
HomeBabban LabarinmuSERAP ta bai wa gwamnan jihar Neja awanni 48 ya janye matakin...

SERAP ta bai wa gwamnan jihar Neja awanni 48 ya janye matakin rufe Badeggi FM

Kungiyar SERAP ta bukaci Gwamnan Jihar Neja, Umar Bago, da ya janye matakin rufe gidan rediyon Badeggi FM, ya dawo da lasisinsa, kuma ya daina barazanar rusa ofishin rediyon.

SERAP ta zargi gwamnatin Bago da keta ’yancin fadin albarkacin baki da ‘yancin kafafen yada labarai, tana kuma neman a daina gallaza wa mai gidan rediyon, Shuaibu Badeggi, da ma’aikatansa.

A cewar SERAP, rufe rediyon da zargin karya bisa rashin hujja ya saba wa kundin tsarin mulkin kasa da alkawarin kare ’yancin bil’adama.

Ta ce idan gwamnatin Neja bata dauki mataki cikin awanni 48 ba, za ta dauki matakin shari’a.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata