Thursday, April 9, 2026
HomeUncategorizedShugaba Tiani na Nijar ya jagorancin bikin daga tutar kungiyar AES ta...

Shugaba Tiani na Nijar ya jagorancin bikin daga tutar kungiyar AES ta kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar

 

Janar Abdulrahman Tiani

Shugaban gwamnatin mulkin sojan Nijar Janar Abdourahamane Tiani ya jagorancin bikin daga sabuwar tutar kungiyar kasashen AES a hukumance wanda ya gudana a Jamhuriyar Nijar.

Shugaba Tiani ya jagoranci wannan biki ne a fadarsa da ke a babban birnin Yamai a gaban membobin gwamnatinsa.

A makonnin da suka gabata ne shugaban kungiyar AES kuma shugaban kasar Mali Janar Assimi Goïta ya gabatar da sabuwar tutar kungiyar ga ministocin kasashen uku da suka halarci wani taro a birnin Bamako.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata