Tuesday, April 7, 2026
HomeBabban LabarinmuShugaba Tinubu ya ba da umurnin buɗe cibiyar agajin gaggawa a Neja...

Shugaba Tinubu ya ba da umurnin buɗe cibiyar agajin gaggawa a Neja saboda ambaliyar Mokwa

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya bayar da umarnin a gaggauta bude cibiyar bayar da agajin gaggawa ta kasa a jihar Neja, biyo bayan mummunar ambaliyar ruwa da ta afku a karamar hukumar Mokwa ta jihar.

Shugaban ya bayar da wannan umarni ne da sanyin safiyar Asabar bayan da rahotanni suka nuna cewa ambaliyar ta yi sanadin asarar rayuka sama da 100 tare da raba iyalai da dama.

A wata sanarwa da ya fitar a shafin sa na X, Shugaba Tinubu ya yi jimamin faruwar ibtila’in, ya kuma yi alkawarin daukar matakin gaggawa da tura agajin jin kai na gwamnatin tarayya don tallafa wa al’ummomin da abin ya shafa.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata