Sunday, April 5, 2026
HomeBabban LabarinmuShugaba Tinubu ya rantsar da Amupitan a matsayin sabon shugaban hukumar zaben...

Shugaba Tinubu ya rantsar da Amupitan a matsayin sabon shugaban hukumar zaben Nijeriya INEC

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya rantsar da Farfesa Joash Amupitan, SAN, a matsayin sabon shugaban Hukumar Zaɓen Nijeriya, INEC.

An gudanar da rantsuwar ne da misalin ƙarfe 1 da minti 50 na rana a dakin taro na fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, inda Farfesa Amupitan ya ɗauki rantsuwar aiki a gaban shugaban ƙasa.

Tinubu ya bukace shi da ya kare mutuncin zaɓen Nijeriya da tsarin gudanar da shi, tare da ƙarfafa ingantaccen tsarin gudanarwa a hukumar INEC domin tabbatar da gaskiya da adalci a zaɓe mai zuwa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata