Shugaba Bola Tinubu ya bai wa mamallaka wuraren hakar man fetur da ba sa aiki a Nijeriya umarnin dawo da su kan aiki, a wani yunkuri na farfado da tattalin arzikin man da ke fuskantar barazanar durkushewa.
Umarnin na kunshe ne cikin bayanan da karamin ministan man fetur na kasar Heineken Lokpobiri ya yi a taron mako na ma’adanan mai da iskar gas a birnin Abuja na shekarar 2025.
Gidan talabijin na Channels ya ruwaito Ministan ya ce farfado da wuraren zai taimaka matuka wajen samun zuba hannayen jari a fannin na man fetur daga bangarori da dama, da kuma tabbatar da ci gaba mai dorewa.
Gwamnatin tarayya dai ta sanya kudurin samar da gangar danyen man fetur miliyan 2 da dubu dari a kowace rana, sannan ta ware sama da Naira tiriliyan 84 a kasafin kudin kasar na bana.
Yanzu haka dai, Nijeriya tana iya samar da ganga miliyan 1 da dubu dari 4 ne kawai a rana, kamar yadda tashar Channels TV ta ruwaito.
