Monday, April 6, 2026
HomeBabban LabarinmuShugaba Tinubu zai gana da kamfanonin samar da lantarki kan bashin Tiriliyan...

Shugaba Tinubu zai gana da kamfanonin samar da lantarki kan bashin Tiriliyan 4 da suke bin gwamnati

Shugaba Bola Tinubu zai gana da shugabannin kamfanonin dake samar da wutar lantarki a Nijeriya, a kokarin ganin an biya bashin Naira Tiriliyan 4 da ke barazanar gurgunta hanyoyin samar da wutar lantarki a kasar.

A cewar wata sanarwa da ma’aikatar lantarki ta Nijeriya ta fitar, matakin ya biyo bayan wani taro da aka yi a ranar Talatar da ta gabata tsakanin ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, da shugabannin kamfanonin a Abuja, a dai dai lokacin da ake ci gaba da fargabar yiwuwar rugujewar tsarin samar da wutar lantarkin a Nijeriya.

Gwamnatin tarayya ta yi alkawarin daukar matakin gaggawa don rage yawan bashin Tiriliyan 4 da ake bi.

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa kamfanonin sun yi gargadin ga gwamnatin tarayya kan ci gaba da tara bashin da ya haura Tiriliyan 4.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata