Shugaban Nijeriya, Bola Tinubu na shirin kammala nadin jakadun da za su wakilci Nijeriya a kasashen waje bayan tsawon lokaci kasar na fama da gibi a diflomasiyya, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Majiyoyi daga fadar shugaban kasa sun ce an shiga matakin karshe na tantance jerin sunayen da za a fitar, bayan da wasu daga cikin wadanda aka tura sun rasu, wasu sun yi murabus, ko kuma sun kai lokacin ritaya.
Rahotanni sun nuna cewa majalisar dattawa ta riga ta tantance wadanda aka turo tun da dadewa, sai dai a sake duba jerin domin tabbatar da cewa sunayen da ke ciki sun cancanta kafin a fitar da sakamakon karshe.
