DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 11, 2026
HomeUncategorizedShugaban hukumar aikin Hajji ta Nijeriya NAHCON ya yi alhinin ajalin matafiya...

Shugaban hukumar aikin Hajji ta Nijeriya NAHCON ya yi alhinin ajalin matafiya 16 a jihar EDO

Farfesa Abdullahi Sale Usman

Shugaban hukumar aikin Hajji ta Nijeriya NAHCON, Farfesa Abdullah Sale , ya bayyana bakin cikin sa kan ajalin matafiya mafarauta su 16 da aka kashe a garin Uromi na jihar Edo.

Shugaban ya mika ta’aziyyar sa ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da iyalan wadan da suka rasu da al’ummar Nijeriya baki daya.

A cewar shugaban al’ummar Nijeriya ya zama wajibi su mutunta  juna a matsayin ‘yan uwa daya ba tare da banbanci ba don ci gaban kasa , kana kare rayukan kowa ya zama tilas a fadin kasar.

Farfesa Saleh ya ce ya yi matukar kaduwa tare da bakin cikin abinda ya faru na matafiyan a yankin Undune Efandion dake Uromi a jihar ta Edo da ya faru ranar 27 ga Maris 2025.

Haka zalika ya yabawa shugaban kasa Tinubu , bisa umarnin da ya bayar na kama batagarin da sukayi aika – aikar.

Ya kuma yaba da kokarin jami’an tsaro na kama Mutum 14 da suka aikata ta’addancin bisa umarnin na shugaban kasa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata