Shugaban kasa Bola Tinubu ya nada sabon shugaban kotun da’ar ma’aikata
Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin Dakta Mainasara Umar Kogo a matsayin shugaban kotun da’ar ma’aikata (CCT).
Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya rabawa manema labarai tace saboda Dokta Kogo kwararren lauya ne kuma manazarci a fagagen shari’a, tsaro, tattalin arziki, siyasa, da diflomasiyyar kasa da kasa hakan yasa aka zakuloshi domin cancantar sa.
Shugaban kasa yayi fatan cewa sabon shugaban zai nuna kwarewa, gaskiya da rikon amana ga kasa wajen gudanar da ayyukan ofishin sa.

