Shugaban majalisar dokokin jihar Borno, Abdulkarim Lawan, ya nuna rashin jin daɗinsa kan rashin sanya hoton mataimakin shugaban Nijeriya, Sanata Kashim Shettima a hotunan da aka yi amfani da su wajen wani taron jam’iyyar APC da ake gudanarwa a Maiduguri, babban birnin jihar.
Abdulkarim Lawan ya bayyana hakan ne a yayin taron, inda ya ce abin bai dace ba a ki saka hoton mataimakin shugaban kasa ba, musamman ganin cewa taron na gudana ne a mahaifarsa, kuma shi ne wakilin Arewa maso Gabas a matsayin mataimakin shugaban ƙasa.
Ya ƙara da cewa irin wannan rashin sanya hoton Shettima ne ya jawo rikici a taron APC na Gombe a bara, yana mai gargadin cewa ya kamata a kauce wa maimaita kuskuren.
