Sunday, April 5, 2026
HomeBabban LabarinmuShugaba Tinubu ne dan takara daya tilo na jam’iyyarmu a zaben 2027...

Shugaba Tinubu ne dan takara daya tilo na jam’iyyarmu a zaben 2027 – Gwamnonin APC

Gwamnonin jam’iyyar APC sun amince da Shugaba Bola Tinubu a matsayin dan takara daya tilo na jam’iyyar a zaben 2027.

Gwamnan Jihar Imo kuma shugaban dandalin gwamnonin APC, Hope Uzodima ne ya bayyana haka a babban taron jam’iyyar da ya gudana a fadar Shugaban Kasa.

Uzodinma ne ya fara ayyana wannan kudiri yayin da gwamnan Kaduna, Uba sani ya mara masa baya inda daga bisani kuma sauran gwamnonin suka amince da Tinubu a matsayin dan takara tilo a jam’iyyar.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata