Monday, April 6, 2026
HomeBabban LabarinmuSojoji sun yi nasarar ceto mutane da kwato Naira miliyan 23 a...

Sojoji sun yi nasarar ceto mutane da kwato Naira miliyan 23 a Sokoto da Zamfara

Rundunar Operation Fansar Yamma sun samu nasarori a jerin hare-hare da suka kai a jihohin Zamfara da Sokoto tsakanin 8 zuwa 10 ga watan Satumba, inda suka kwato makudan kudade, dabbobi tare da ceto mutane daga hannun ’yan bindiga.

A cikin wata sanarwa da jami’in yada labarai na rundunar, Kyaftin David Adewusi ya fitar, ya ce dakarun sun kai farmaki a kananan hukumomin Shinkafi, Gusau, Bukkuyum da Tureta, inda suka lalata maboyar ’yan ta’adda tare da fatattakar su.

Ya bayyana cewa an samu nasarar kwato sama da Naira miliyan 23 da ake zargin kudin fansa ne, an kuma ceto wasu daga cikin mutanen da aka sace tare da kwato sama da dabbobi 160 da aka sace.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata