Sunday, April 5, 2026
HomeBabban LabarinmuSojojin Nijeriya sun yi ajalin wadanda suka jagoranci harin gidan gyaran hali...

Sojojin Nijeriya sun yi ajalin wadanda suka jagoranci harin gidan gyaran hali na Kuje

Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya bayyana a ranar Asabar cewa, dakarun sojojin Nijeriya sun halaka wasu manyan kwamandojin ƙungiyar ta’addanci ta Ansaru a wani gagarumin samame da aka gudanar tsakanin watan Mayu da Yuli, 2025.

A cewar Ribadu, cikin waɗanda aka kashe har da Mahmud Usman, wanda aka fi sani da Abu Bara’a, tare da mataimakinsa Mahmud al-Nigeri da ake kira Mallam Mamuda.

Rahoton jaridar Premium Times ya nuna cewa duka biyun sun shafe shekaru ana neman su ruwa a jallo a matsayin manyan masu laifi.

Abu Bara’a, wanda ya ayyana kansa shugaban Ansaru, shi ne ya kafa ƙungiyoyi a sassa daban-daban na ƙasar tare da jagorantar ayyukan ta’addanci ta hanyar garkuwa da mutane da fashi da makami domin samun kuɗaɗe.

Mallam Mamuda kuwa ya jagoranci wani rukuni a dajin Kainji, inda rahotanni suka ce ya samu horo daga ‘yan jihadi na ƙasashen waje a Libya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata