Sunday, April 5, 2026
HomeBabban LabarinmuSule Lamido zai tsaya takarar kujerar shugabancin PDP na kasa

Sule Lamido zai tsaya takarar kujerar shugabancin PDP na kasa

Jigo a jam’iyyar PDP a Nijerita Alhaji Sule Lamido ya bayyana kudirinsa na sayen tikitin neman zama sabon Shugaban jam’iyyar PDP na kasa

A wani takaitaccen rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook ya ce kudurinsa na ganin an dawo da martabar dimokuraɗiyya da kuma farfaɗo da jam’iyyar zuwa darajar da take da ita a da, ba zai taɓa yankewa ba.

Tsohon gwamnan na Jigawa na cikin sahun farko na wadanda aka kafa jam’iyyar ta PDP da su a Nijeriya.

Kuma na gaba-gaba a takarar neman zama sabon shugaban jam’iyyar ta PDP daga Arewa maso Yamma.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata